Makalu

Yadda ake crispy onion rings

 • Assalamu alaikum barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. A yau zan nuna mana yadda ake hada onion rings a saukake.

  Abubuwan hadawa

  1. Albasa (manya)
  2. Man gyada
  3. Maggi da seasoning
  4. Kwai
  5. Filawa
  6. Corn flour
  7. Yeast
  8. Baking powder

  Yadda ake hadawa

  1. Za ki yanka albasa slices ki aje su gefe.
  2. Sai ki zuba cup na flour da 1/2 cup na corn flour da baking powder ko yeast a bowl (ko wane ki kasa yadda zai tashi daban). Bayan haka, sai ki sa maggi da gishiri ki kwaba shi da kauri yadda zai kama albasa.
  3. Ki fasa kwai ki kada shi sai ki bi albasa nan kina dipping cikin batter na flour sai ki tsoma a ruwan kwai, sannan sai ki sa a cikin man gyada da ke kan wuta. Idan ya yi brown a juya. A ci lafiya.

   Sannan za a iya dubaYadda ake hada shredded chicken sauce da yadda ake hada oven grilled liver da sauransu.

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Nazari kan hukunce-hukuncen ittikafi

  Posted May 25

  Ma'anar ittikafi: Ittikafi shine lizimtar masallaci don bautawa Allah Madaukakin Sarki. Hukuncinsa: Sunnah ne, ba ya wajaba sai ga wanda ya yi bakance akansa. Dalilin haka ya tabbata daga Al-Kur'ani da Hadisai da ijma'in malamai. Dalili daga Al-Kur'ani Allah Ya ...

 • Shar’antattu daga cikin ladubban mai yin azumi

  Posted May 23

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da alayensa da sahabbansa baki daya. Lallai Allah Ya shar'anta wasu ladubba ga ibadar azumi, wanda ya dace mumini ya yi riko da su, saboda ya yi azuminsa cikin cikakkiya...

 • Tasirin fina-finai a kan al’adun Hausawa: Keɓaɓɓen nazari a kan wasu Ɗabi’u na musamman a cikin fina-finan Hausa

  Posted May 22

  Maƙalar da aka Shirya Gabatarwa a Taron Ƙara wa Juna Sani na Ƙasa-da-ƙasa a Kan Gudummuwar Fasaha ga ci Gaba, Wanda Tsangayar Fasaha da Addinin Musulunci, Jami’ar Bayero, Kano ta Shirya, Daga Ranar Laraba 5 ga Watan Oktoba Zuwa Ranar Asabat 8 ga Watan Oktoba, Shek...

 • Abubuwan da suke karya azumi

  Posted May 20

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa, da wadanda suka biyo bayansu har zuwa rananr sakamako. A wata makala da ta gabata mun yi bayani akan falalar azumin watan Ramalana inda muka ka...

 • Yadda ake hada tuna muffins

  Posted May 19

  Asaalamu alaikum, barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya a yau. Zamu yi bayanin yadda ake hada tuna cheese muffins ne a yau. Abubuwan hadawa Tuna fish 2 Kwai 2 Gishiri Yaji Grated karas Corn flour Yankakken tattasai Yankakken koren tattasai ...

View All