Makalu

Yadda ake hada rolled stuffed moi-moi

 • Assalamu alaikum barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. A baya mun koyar da crispy onion rings da ma wasu kalan girke-girke da dama, mai karatu zai iya dubawa. A yau zan nuna mana yadda ake hada rolled stuffed moi-moi (alale).

  Abubuwan hadawa

  1. Wake
  2. Tarugu da tattasai
  3. Albasa
  4. Maggi da seasoning
  5. Garlic
  6. Manja
  7. Sausage
  8. Kwai
  9. Karas

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko za ki wanke wake ki surfa sai ki zuba tarugu da tattasai da albasa ki nika shi ya yi laushi sosai.
  2. Ki zuba wannan hadin a cikin bowl ki sa manja, seasoning, garlic powder, da curry, sannan za ki iya saka cray fish ma ki juya shi sosai komai ya hade.
  3. Ki saka mai kadan a pan ki sa sausage da karas ki yi stir frying na su sai ki sauke. Ki dafa kwai ki bare shi ki yanka slices. Shi ma ki aje a gefe.
  4. Za ki kunna oven 180° sai ki dauko parchment paper ki shinfida ta akan tray na baking ki zuba kullun ki saka a oven.
  5. Bayan mintina 10 in ya fara yi sai ki sauko da shi ki zuba fillings ko ina ki mayar ya gama gasuwa.
  6. Idan ya yi za ki ji kamshin ya hade ko ina ki sa toothpick ki duba, don kin tabbatar ya dahu. Ki sauke ki nade kaman nadin tabarma. Ki dan bari ya huce sai ki yanka. A ci lafiya.

  Sannan za a iya dubaYadda ake hada crispy samosa da yadda ake hada grilled gizzard da sauransu.

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Yadda ake hada ladoos

  Posted Mar 12

  Assalamu alaikum, barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. A yau zan koya mana yadda ake hada Laddoos. Abubuwan hadawa Condensed milk Powered milk ko wane irin Biscuit plain desiccated coconut Nutella Sprinkles Yadda ake hadawa ...

 • Yadda ake hada spicy pancakes and potato fillings

  Posted Mar 11

  Assalamu alaikum, barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. A yau zan koya mana yadda ake hada spicy pancake and potatoe fillings. Abubuwan hadawa Filawa Tarugu Albasa Dankali (Irish) Maggi Seasoning Kwai Man gyada Baking powder Yadda a...

 • Yadda ake hada sweet pancakes

  Posted Mar 11

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. A yau zan koya mana yadda ake hada sweet pancake. Abubuwan hadawa Filawa Sugar Baking powder Kwai Chocolates Nutella Dark chocolates Maltesers Smarties Yadda ake hadawa Far...

 • Yadda ake hada milky nut pap

  Posted Mar 11

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. A yau zan koya mana yadda ake hada milky nut pap. Abubuwan hadawa Farar shinkafa ta tuwo Gyada Madara Dabino Sugar Yadda ake hadawa Farko za ki jika farar shinkafa sai ki gyara ...

 • Yadda ake peppered soup na kaza

  Posted Mar 11

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. A yau zan koya mana yadda ake hada peppered soup na kaza. Abubuwan hadawa Kazan Hausa Tarugu da tattasai Albasa  Lawashi Curry Maggi da seasoning Tafarnuwa Tandoori Chicken sp...

View All