Makalu

Yadda ake dambun nama

 • Assalamu alaikum barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. Har a yau mai karatu zai iya duba makalunmu da muka gabatar na daruruwan girke-girke. A yau na zo mana da yadda ake hada dambun nama  kaza ko dai na jar nama.

  Abubuwan hadawa

  1. Nama/kaza
  2. Tarugu
  3. Albasa
  4. Tafarnuwa
  5. Seasoning
  6. Maggi
  7. Man gyada

  Yadda ake hadawa

  1. Farko za ki wanke nama ko kaza ki zuba cikin tukunya ki zuba albasa da tarugu da tafarnuwa.
  2. Ki dora a wuta, ki barshi ya yi ta dahuwa kaman awa 4/5 yana dahuwa.
  3. Idan kin sauke, sai ki raba shi da kashi da kitsensa ko fata duka ki cire ki mayar da tsokar ki sa muciya ki tuke shi ki sa seasoning da spices.
  4. Sai ki zuba man gyada har ya rufe naman ki soya. Ba za ki daga ba ki na yi kina juya shi har ya yi.
  5. Sai a kwashe a saka a cikin abun tata a matse man. A tabbar ba sauran mai sai a zuba cikin sieve ko colander. A ci lafiya

  Za a iya duba: Yadda ake hada ladoos da yadda ake hada sweet pancakes da sauransu.

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Nazari kan hukunce-hukuncen ittikafi

  Posted 3 hours ago

  Ma'anar ittikafi: Ittikafi shine lizimtar masallaci don bautawa Allah Madaukakin Sarki. Hukuncinsa: Sunnah ne, ba ya wajaba sai ga wanda ya yi bakance akansa. Dalilin haka ya tabbata daga Al-Kur'ani da Hadisai da ijma'in malamai. Dalili daga Al-Kur'ani Allah Ya ...

 • Shar’antattu daga cikin ladubban mai yin azumi

  Posted Thu at 12:18 PM

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da alayensa da sahabbansa baki daya. Lallai Allah Ya shar'anta wasu ladubba ga ibadar azumi, wanda ya dace mumini ya yi riko da su, saboda ya yi azuminsa cikin cikakkiya...

 • Tasirin fina-finai a kan al’adun Hausawa: Keɓaɓɓen nazari a kan wasu Ɗabi’u na musamman a cikin fina-finan Hausa

  Posted Wed at 1:07 PM

  Maƙalar da aka Shirya Gabatarwa a Taron Ƙara wa Juna Sani na Ƙasa-da-ƙasa a Kan Gudummuwar Fasaha ga ci Gaba, Wanda Tsangayar Fasaha da Addinin Musulunci, Jami’ar Bayero, Kano ta Shirya, Daga Ranar Laraba 5 ga Watan Oktoba Zuwa Ranar Asabat 8 ga Watan Oktoba, Shek...

 • Abubuwan da suke karya azumi

  Posted Mon at 1:07 PM

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa, da wadanda suka biyo bayansu har zuwa rananr sakamako. A wata makala da ta gabata mun yi bayani akan falalar azumin watan Ramalana inda muka ka...

 • Yadda ake hada tuna muffins

  Posted May 19

  Asaalamu alaikum, barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya a yau. Zamu yi bayanin yadda ake hada tuna cheese muffins ne a yau. Abubuwan hadawa Tuna fish 2 Kwai 2 Gishiri Yaji Grated karas Corn flour Yankakken tattasai Yankakken koren tattasai ...

View All