Makalu

Yadda ake hada miyan allahayo (veg soup)

 • Assalamu alaikum barka da sake saduwa a cikin fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. Harwa yau mai karatu zai iya duba makalunmu da muka gabatar na daruruwan girke-girke. A yau kuma zan koya mana yadda ake hada veg soup ne wato miyar allahayaho.

  Abubuwan hadawa

  1. Tattasai da tarugu
  2. Manja
  3. Nama
  4. Albasa
  5. Seasoning da spices
  6. Allayaho
  7. Lawashi

  Yadda ake hadawa

  1. Farko za ki tafasa nama ki sa albasa a cikin tafashen da maggi. Idan ya yi sai ki juye ki zuba manja ki sa nama, sai ki zuba wannan chopped tattasai da tarugun da albasa mai yawa ki juya sai ki dan rufe ya soyu kaman mintina 3.
  2. Bayan kamar minti ukun, sai ki bude ki saka yan ruwa kamar kofi 1/4, ba da yawa ake so ba. Ki sa seasoning da spices, ki yanka albasa da lawashi da allayaho ki wanke ki zuba, ki rufe idan ya dahu a ci.

  Za a iya dubaYadda ake dambun shinkafa mai gyada da yadda ake hada healthy spinach mix da sauransu.

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Tasirin fina-finai a kan al’adun Hausawa: Keɓaɓɓen nazari a kan wasu Ɗabi’u na musamman a cikin fina-finan Hausa

  Posted Wed at 1:07 PM

  Maƙalar da aka Shirya Gabatarwa a Taron Ƙara wa Juna Sani na Ƙasa-da-ƙasa a Kan Gudummuwar Fasaha ga ci Gaba, Wanda Tsangayar Fasaha da Addinin Musulunci, Jami’ar Bayero, Kano ta Shirya, Daga Ranar Laraba 5 ga Watan Oktoba Zuwa Ranar Asabat 8 ga Watan Oktoba, Shek...

 • Abubuwan da suke karya azumi

  Posted Mon at 1:07 PM

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa, da wadanda suka biyo bayansu har zuwa rananr sakamako. A wata makala da ta gabata mun yi bayani akan falalar azumin watan Ramalana inda muka ka...

 • Yadda ake hada tuna muffins

  Posted May 19

  Asaalamu alaikum, barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya a yau. Zamu yi bayanin yadda ake hada tuna cheese muffins ne a yau. Abubuwan hadawa Tuna fish 2 Kwai 2 Gishiri Yaji Grated karas Corn flour Yankakken tattasai Yankakken koren tattasai ...

 • Jaye karar tsana: Uzuri da tuni daga mantuwa

  Posted May 16

  Ta Abu-Ubaida SANI Department of Languages and Cultures Federal University Gusau, Zamfara Phone No: 08133529736 Email: abuubaidasani5@gmail.com   1. Ya Allah mahalaccin komai,                  Wanda ya ƙaga yawan...

 • Kadan daga cikin falalar azumin watan Ramalana

  Posted May 14

  Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da alayensa da sahabbansa, da wadanda suka biyo bayansu da kyautata. Yana daga hikimar Allah Madaukakin Sarki fifita wasu mutane akan wasu, Ya kuma fifita wasu wurare aka...

View All