Makalu

Yadda ake hada ugwu-egusi soup

 • Assalamu alaikum, barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. Harwa yau mai karatu zai iya tuba makalun da muka gabatar na daruruwan girke-girke a baya. A yau kuma zan koya mana yadda ake hada ugwu-egusi soup.

  Abubuwan hadawa

  1. Ugwu leaf
  2. Egusi
  3. Tarugu da tattasai (t&t)
  4. Albasa
  5. Seasoning
  6. Manja
  7. Garlic
  8. Beef/Kifi
  9. Kwai

  Yadda ake hadawa

  1. Farko za ki saka manja a pot sai ki sa albasa ki juya ki zuba grated t&t dinki a ciki ki motsa(Idan kifi ne sai ki wanke shi ki gyara ki saka,Idan tafasashen nama ne sai ki zube da ruwan shi aciki,yadai danganta da yadda kike son ko wane a miya.
  2. Ki saka garlic a ciki ki yanka albasa mai dan yawa ki zuba. Ki wanke ugwu leaf ki yanka shi sai ki saka, Ki yayyafa yan ruwa ba da yawa ba.
  3. Ki sa seasonings da maggi idan ganyen ya fara dahuwa sai ki hada egusi. Ki zuba egusi a bowl ki fasa kwai ki kwaba shi da kauri. Ki dinga diban wannan paste ki na sawa kaman yadda ake saka kosai. Ki rufe na yan mintina sai ki bude ki juya, idan ya dahu sai a ci da ko wane irin tuwo.

  Za a iya dubayadda ake hada tsire a saukake da yadda ake hada miyan allahayo (veg soup) da sauransu.

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Hanyoyi guda biyar na rage ƙiba ba tare da an shiga hatsari ba

  Posted Jun 12

  A duniyarmu ta yau, ƙiba na daya daga cikin matsalolin da ke addabar mutane da dama. Saboda irin ci gaba da aka samu na yawaitar abinci kala-kala – abincin gargajiya da na zamani, na gwangwani da na gona – ya sa da yawa mutane na yawaita cin abincin da zai k...

 • Sharudda da kuma ladubbar sallar idi karama

  Posted Jun 3

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da iyalansa da Sahabbansa baki daya. Idi shine duk abinda yake dawowa yana maimaituwa lokaci zuwa lokaci, kamar sati-sati, ko wata-wata, ko shekara-shekara. Shar'anta s...

 • Hukunce-hukuncen zakkar fidda kai

  Posted May 31

  Ma'anar zakkar fidda kai: Sadaka ce wacce ake bayar da ita sakamakon kammala azumin watan Ramadan. An shar'anta zakkar ne a shekara ta biyu bayan hijirar Annabi sallallahu alaihi wa sallam daga Makkah zuwa Madinah, a shekarar da aka wajabta azumin watan Ramadan. Huku...

 • Yadda ake hada local jollof rice

  Posted May 30

  Assalamu alaikum barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. Barka da shan ruwa. Yau zamu koyi yadda ake hada local jollof rice wato dafa dukan shinkafa ke nan da Hausa. Abubuwan hadawa Shinkafa Tattasai da tarugu Daddawa Albasa Seasoning Manja Ta...

 • Yadda ake hada bitter leaf soup

  Posted May 30

  Assalamu alaikum, barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya na yau. Barka da shan ruwa. A yau zamu duba yadda za ki hada bitter leaf soup (miyan shuwaka). Abubuwan hadawa Manja Nama Seasoning Garlic  Ginger Shuwaka (bitter leaf) Tattasai Ta...

View All