Makalu

Yadda ake doya mai kwai

 • Assalamu alaikum, barka da sake saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. A har kullum kada a manta, mai karatu zai iya duba makalunmu da muka gabatar na daruruwan girke-girke. A yau kuma zan koya mana yadda ake hada doya da kwai.

  Abubuwan hadawa

  1. Doya
  2. Kwai
  3. Maggi
  4. Tarugu
  5. Man gyada
  6. Albasa da lawashi

  Yadda ake hadawa

  1. Farko za ki yanka doya ki tafasa ta ki sa gishiri kadan sai ki zuba wannan doya a bowl.
  2. Ki samu wani bowl ki fasa kwai ki sa tarugu, da maggi, da albasa ki kada shi.
  3. Ki dora mai a cikin frying pan. Idan ya dauki zafi ki rika tsoma doyan a ruwan kwan, sannan ki rika tsomawa cikin man gyadan.
  4. Ki juya gefe dayan idan ya yi, sai ki kwashe idan shima gefen ya yi.

  Za a iya duba: Yadda ake hada egg sauce da yadda ake dambun nama da sauransu.

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Hanyoyi guda biyar na rage ƙiba ba tare da an shiga hatsari ba

  Posted Jun 12

  A duniyarmu ta yau, ƙiba na daya daga cikin matsalolin da ke addabar mutane da dama. Saboda irin ci gaba da aka samu na yawaitar abinci kala-kala – abincin gargajiya da na zamani, na gwangwani da na gona – ya sa da yawa mutane na yawaita cin abincin da zai k...

 • Sharudda da kuma ladubbar sallar idi karama

  Posted Jun 3

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da iyalansa da Sahabbansa baki daya. Idi shine duk abinda yake dawowa yana maimaituwa lokaci zuwa lokaci, kamar sati-sati, ko wata-wata, ko shekara-shekara. Shar'anta s...

 • Hukunce-hukuncen zakkar fidda kai

  Posted May 31

  Ma'anar zakkar fidda kai: Sadaka ce wacce ake bayar da ita sakamakon kammala azumin watan Ramadan. An shar'anta zakkar ne a shekara ta biyu bayan hijirar Annabi sallallahu alaihi wa sallam daga Makkah zuwa Madinah, a shekarar da aka wajabta azumin watan Ramadan. Huku...

 • Yadda ake hada local jollof rice

  Posted May 30

  Assalamu alaikum barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. Barka da shan ruwa. Yau zamu koyi yadda ake hada local jollof rice wato dafa dukan shinkafa ke nan da Hausa. Abubuwan hadawa Shinkafa Tattasai da tarugu Daddawa Albasa Seasoning Manja Ta...

 • Yadda ake hada bitter leaf soup

  Posted May 30

  Assalamu alaikum, barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya na yau. Barka da shan ruwa. A yau zamu duba yadda za ki hada bitter leaf soup (miyan shuwaka). Abubuwan hadawa Manja Nama Seasoning Garlic  Ginger Shuwaka (bitter leaf) Tattasai Ta...

View All