Makalu

Yadda ake hada net crepes

 • Assalamu alaikum, barka da sake saduwa a fannin girkegirkenmu na Bakandamiya. Harwa yau mai karatu zai iya duba makalunmu da muka gabatar na daruruwan girke-girke a baya. A yau kuma zan koya mana yadda ake hada net crepes.

  Abubuwan hadawa

  1. Fulawa
  2. Baking powder
  3. Food colour (na yi amfani da green da yello)
  4. Kwai (1)
  5. Gishiri
  6. Gorar ruwa (empty)
  7. Meat filling/cabbage filling/potato filling (kaman yadda muka yi bayanin hadin naman samosa ko meat pie) 

  Yadda ake hadawa

  1. Farko za ki zuba fulawa da baking powder, kwai da gishiri a bowl ki yi mixing sai ya yi smooth sosai kuma ba da kauri ba.
  2. Sai ki raba shi, ki sa duk colors da ki ke so.
  3. Ki samu gora ki huda marfin kaman huduwa hudu.
  4. Ki zuba batter a cikinshi. Ki dora non stick pan akan wuta ki shafa mai.
  5. Ki dinga zuba batter na cikin gorannan ta koina a wannan pan din, ya yi saka-saka.
  6. Idan ya yi ki cire ki sa wani. Idan kin gama duka ki cire. Ki zuba filling a ciki ki rufe. Ki rufe kamar rufin shawarma. A ci lafiya.

  Za a iya dubaYadda ake hada desiccated coconut and chocolate chips cake da yadda ake hada ugwu egusi soup da sauransu.

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Tasirin fina-finai a kan al’adun Hausawa: Keɓaɓɓen nazari a kan wasu Ɗabi’u na musamman a cikin fina-finan Hausa

  Posted Wed at 1:07 PM

  Maƙalar da aka Shirya Gabatarwa a Taron Ƙara wa Juna Sani na Ƙasa-da-ƙasa a Kan Gudummuwar Fasaha ga ci Gaba, Wanda Tsangayar Fasaha da Addinin Musulunci, Jami’ar Bayero, Kano ta Shirya, Daga Ranar Laraba 5 ga Watan Oktoba Zuwa Ranar Asabat 8 ga Watan Oktoba, Shek...

 • Abubuwan da suke karya azumi

  Posted Mon at 1:07 PM

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa, da wadanda suka biyo bayansu har zuwa rananr sakamako. A wata makala da ta gabata mun yi bayani akan falalar azumin watan Ramalana inda muka ka...

 • Yadda ake hada tuna muffins

  Posted May 19

  Asaalamu alaikum, barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya a yau. Zamu yi bayanin yadda ake hada tuna cheese muffins ne a yau. Abubuwan hadawa Tuna fish 2 Kwai 2 Gishiri Yaji Grated karas Corn flour Yankakken tattasai Yankakken koren tattasai ...

 • Jaye karar tsana: Uzuri da tuni daga mantuwa

  Posted May 16

  Ta Abu-Ubaida SANI Department of Languages and Cultures Federal University Gusau, Zamfara Phone No: 08133529736 Email: abuubaidasani5@gmail.com   1. Ya Allah mahalaccin komai,                  Wanda ya ƙaga yawan...

 • Kadan daga cikin falalar azumin watan Ramalana

  Posted May 14

  Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da alayensa da sahabbansa, da wadanda suka biyo bayansu da kyautata. Yana daga hikimar Allah Madaukakin Sarki fifita wasu mutane akan wasu, Ya kuma fifita wasu wurare aka...

View All