Makalu

Yadda ake hada tuna muffins

 • Asaalamu alaikum, barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya a yau. Zamu yi bayanin yadda ake hada tuna cheese muffins ne a yau.

  Abubuwan hadawa

  1. Tuna fish 2
  2. Kwai 2
  3. Gishiri
  4. Yaji
  5. Grated karas
  6. Corn flour
  7. Yankakken tattasai
  8. Yankakken koren tattasai
  9. Albasa
  10. Lawashi
  11. Mayonnaise 1/2 cup
  12. Fulawa 1/2
  13. Baking powder 1 tsp
  14. Grated cheddar cheese 1cup

  Yadda ake hadawa

  Za ki gyara carrots dinki kiyi grating,ki yanka tattasai,koren tattasai da lawashi,kiyi grating cheese shima ki ajiye,Ki tanadi bowl ki zuba flour,corn flour da kayan da kika yanka a baya,Seasoning komai da aka lisafa a sama ki yi mixing zakiga ya hada batter din yayi thick yayi kyai.

  Ki nemo Muffins ki shafe jikin cupcake muffins (abun gasa cupcake kenan) sai ki dinga diba kina zubawa acikin shi,sai ki gasa a cikin Oven @ 180° Idan ya yi zaki ga yayi holds Brown ya gasu sai ki cire

  Za a iya dubaYadda ake hada sher's chips da yadda ake hada carrot juice da sauransu.

Comments

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Dalilan da ka iya sawa a koma vegan diet

  Posted Sep 2

  A ‘yan shekaru kadan da suka wuce, kafar yada labarai ta kasar Amurka mai suna USA Today ta ruwaito cewa kashi 50% na mutanen kasar Amurka suna ta kokarin su ga sun inganta lafiyarsu ta hanyar kokarin ganin sun rage yadda su ke cin nama da yawa a ciki abincinsu. A...

 • Physics: Darasi akan pressure in fluid

  Posted Aug 29

  Ga definition na pressure a Turance kamar haka; pressure is defined as the force acting perpendicularly per unit area. Idan kuma za a duba equation na shi ne a math, shi kuma ga shi kamar haka: Pressure = Force / Area , shi ne kamar haka,  P = F / A Ga abinda ...

 • Matsalar shaye-shaye a tsakanin matasanmu a yau

  Posted Aug 25

  A wannan Makala za muyi dubi ne zuwa ga wani maudu’i mai muhimmanincin gaske. Za mu duba matsalar shaye-shaye da ya zama tamkar ruwan dare gama duniya a tsakanin matasanmu maza har da mata a wannan zamani. Duk da cewa wannan mummunar dabi’a ba dabi’a ...

 • Wa ya gaya mi ki cewa yana son ki har cikin zuciyarsa? Ki lura da wadannan alamomi

  Posted Aug 24

  Abu ne mai matuƙar ciwo mace ta fahimci cewa namijin da take so, baya sonta. Baya son kasancewa da ita a rayuwarsa.  Abun takaici irin wadannan mazajen basa iya fadar cewa ba sa son mace a baki, bare har ta san inda dare ya yi ma ta. Sai ya zamo ke a zuciyar ki ki...

 • Maɗigo da yawaitarsa cikin al’umma: Ina mafita?

  Posted Aug 20

  Tasowarmu muna kanana cikin alumma mun ga iyayenmu da sauran magabata suna da aure. Kowa da mahaifinsa da mahaifiyarsa. Hakanan kuma yayin da muke rayuwa mun ga ‘yan mata da samari daban-daban sun taso kuma mun ga sun yi aure. Kuma sannan sa’i da lokaci mutu...

View All