Makalu

Yadda ake hada local jollof rice

 • Assalamu alaikum barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. Barka da shan ruwa. Yau zamu koyi yadda ake hada local jollof rice wato dafa dukan shinkafa ke nan da Hausa.

  Abubuwan hadawa

  1. Shinkafa
  2. Tattasai da tarugu
  3. Daddawa
  4. Albasa
  5. Seasoning
  6. Manja
  7. Tafarnuwa
  8. Busashshen kifi
  9. Danyen nama

  Yadda ake hadawa

  1. Farko zaki dora tukunya ki zuba manja a ciki ki yanka albasa. Sai ki wanke nama ki zuba a ciki.
  2. A dai dai wannan lokacin uwargida ta gyara kayan miya (tattasai tarugu da albasa) sai ki zuba a cikin wannan naman ki juya, za ki ga yana dan soyuwa sama sama, sai ki tsayar da ruwan dahuwar shinkafarki.
  3. Ki zuba tafarnuwa, daddawa da maggi da sauran seasoning a cikin ruwan sannan ki rufe.
  4. Idan ya tafasa sai ki wanke shinkafa ki zuba ki rufe. Ki yanka albasa manyan slices sai ki gyara kifi busashe ki hade su.
  5. Idan shinkafarki ta fara tsotse ruwa sai ki zuba ki rufe su dahu tare. Idan ya dahu a sauke.

  Za a iya duba: Yadda ake hada onion sauce da yadda ake hada tuna muffins da sauransu.

Comments

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Yadda ake hada spinach soup (miyan masa)

  Posted Oct 19

  Asaalamu alaikum, barka da sake saduwa a cikin shirin Bakandamiya. A yau insha Allahu zamu duba yadda uwargida za ta hada miyan masa, kuma wannan miyan za ki iya cin abubuwa dayawa ma da ita. Abubuwan hadawa Manja Albasa da lawashi Kayan miya Naman rago Allayaho...

 • Darasi game da electrical method

  Posted Oct 18

  A makala ta da ta gabata mai suna method of mixture na yi bayanin specific heat capacity yanda ya ke dauke da method guda biyu na measuring dinshi wanda na kawo su kamar haka: Method of mixtures Electrical Method Saboda haka method din lissafinsu ma biyu ne, kuma...

 • Yadda ake grilled sandwich

  Posted Oct 18

  Abubuwan hadawa Biredi mai yanka Soyayyen plantain(agada) Kwai Nama (ki dafa, ki daka) Tarugu (ki jajjaga ko ki yanka) Koren wake (ki yanka) Karas (ki yanka) Kabeji (ki yanka) Maggi Gishiri Butter Abun gashi (manual sandwich grill) Yadda ake hadawa ...

 • Yadda ake hada buttered shape cookies

  Posted Oct 14

  Assalamu alaikum, makalarmu ta yau zamu yi bayani ne akan yadda zaki hada butter shaped cookies Abubuwan hadawa Flour 2 cups Sugar 1 cup Butter 250grm Baking powder 1tspn Kwai 1 Icing sugar Egg white Yadda ake hadawa Farko za ki mixing sugar da butter n...

 • Yadda ake hada red velvet coconut balls

  Posted Oct 14

  Assalamu alaikum barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. Zamu yi bayani akan yadda za ki hada red velvet coconut balls a yau. Abubuwan hadawa Kwakwa Condensed milk Madarar gari Corn flour Red colour Yadda ake hadawa Farko za ki zuba corn ...

View All