Makalu

Yadda ake hada spinach soup (miyan masa)

 • Asaalamu alaikum, barka da sake saduwa a cikin shirin Bakandamiya. A yau insha Allahu zamu duba yadda uwargida za ta hada miyan masa, kuma wannan miyan za ki iya cin abubuwa dayawa ma da ita.

  Abubuwan hadawa

  1. Manja
  2. Albasa da lawashi
  3. Kayan miya
  4. Naman rago
  5. Allayaho
  6. Maggi
  7. Tafarnuwa
  8. Mixed spices

  Yadda ake hadawa

  1. Farko za ki tafasa nama ki yanka albasa a cikin tafashen ki sa maggi, idan ya yi ki zube da ruwan a gefe sai ki mayar da tukunyar.
  2. Ki zuba manja a cikin tukunyar sai ki saka albasa idan ya fara soyuwa sai ki zuba kayan miya da ki ka nika. Ki rufe ki ba shi yan mintina dan su soyu, idan ki ka juya sai ki zube wannan ruwan tafashen da naman a ciki.
  3. Ki zuba su maggi da tafarnuwa ki rufe. Sai ki yanka allayaho dinki,ki sheka ma shi ruwan zafi akai (amfanin yin hakan dan colour din ya fito yadda yake) Ki zuba allayaho dinki ki juya idan ta dahu sai a sauke. A ci lafiya.

  Za a iya dubayadda ake hada buttered shape cookies da yadda ake hada red velvet coconut balls da sauransu.

Comments

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • GARIN NEMAN GIRA

  Posted Nov 1

  GARIN NEMAN GIRA...!* *ZULAIHAT HARUNA RANO* Ya faru a gaske. Cikin nutsuwa ta miƙe tana naɗe sallayar da ta yi sallah a kai, bakinta yana motsin da ke nuni da addu'a take yi. A hankali ta kai dubanta kan ƙaton agogon bangon falon, wanda ya nuna mata karfe goma...

 • Ra'ayoyin mazan Arewa game da kayan ni’ima na mata

  Posted Oct 31

  Bayan ra'ayoyin mata da mu ka ji da irin alfanu da kuma rashin alfanu da kayan mata ke da shi wanda mu ka tattauna a makalar da ta gabata, to yau kuma za mu kawo muku bayanin bincike da na yi dangane da ra’ayoyin maza akan lamarin. Mun ji ra'ayoyi ma bambanta kwar...

 • Yadda ake hada ring chocolate cookies

  Posted Oct 31

  Barka da sake saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau zamu gabatar da yadda za ki hada ring chocolate cookies(doughnut cookies). Abubuwan hadawa Flour Sugar Butter Kwai Cocoa powder Chocolate chips Baking powder Yadda ake hadawa Farko za k...

 • Yadda ake hada coconut pound cake

  Posted Oct 31

  Assalamu alaikum, barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girke na Bakandamiya. A yau zamu yi bayani ne akan yadda ake hada coconut pound cake. Sai a biyo mu dan jin yadda ake hadawa. Abubuwan hadawa Kwakwa (desiccated) Kwai 8 Butter 1 (250g) Sugar kofi 1...

 • MA'AURATA

  Posted Oct 29

  ????????????????????  *MA AURATA*????????????????????????????   *By Aisha Abdullahi*Tsaye take abakin ƙofa sai cika take tana batsewa tana jijjiga ƙafa wani matashi ne wanda bazai haura shekara 30 zuwa da 34 ba naga ya buɗe ƙofar da take tsayeDa sauri ta ...

View All