Makalu

Yadda ake lemun cucumber

 • Mai karatu barkanmu da warhaka, a cikin girke girkenmu na yau za mu koyi yadda ake lemun cucumber. Mai karatu kafin mu ci gaba za ku iya duba girke girkenmu na baya kamar yadda ake smoothie na avocado. To ga yadda ake lemun cucumber kamar haka dalla dalla:

  Abubuwan Hadawa

  1. Cucumber
  2. Danyar citta
  3. Ruwan lemun tsami
  4. Flavour na butterscotch (ko duk flavour da ki ke dashi)
  5. Kankara
  6. Sugar

  Yadda ake hadawa

  1. Ki samu cucumber ki wanke ta, ki yanka kanana da danyar citta ki sa a blender, sai ki rufe blender, ki nika su.
  2. Bayan ya yi sai ki tace ki sa suga, da ruwan lemun tsami, da flavour da kankara shikenan.

  Karin bayani

  • Za ki iya yanka cucumber slice ki zuba a ciki dan garnishing.

  Mai karatu wannan shine yadda ake lemun cucumber, sai mun hadu a girki na gaba, na gode. Kada a manta za a  iya duba girkinmu na baya kamar, yadda ake miyar ayoyo  da kuma yadda ake fluffy vanilla pancakes da makamantansu.

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Yadda ake hada turmeric fried rice

  Posted Feb 11

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. A yau zanu koyar da yadda ake hada turmeric fried rice. Abubuwan hadawa Turmeric Curry Albasa da lawashi Rice Man gyada  Tarugu Green pepper Carrots Green beans Peas Garlic ...

 • Yadda ake hada cabbage sauce

  Posted Feb 11

  Barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. A yau kuma zamu koyar da yadda ake hada cabbage sauce. A baya munyi bayanin akan yadda ake abinci daban-daban, za a iya dubawa. Abubuwan hadawa Cabbage Green pepper Peas Green beans Tarugu Tattasai S...

 • Yadda ake hada vegetable rice

  Posted Feb 11

  Barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. Yau zan gabatar mana da yadda ake hada vegetable rice. Abubuwan hadawa Peas Green beans Carrots Inibi Basmati rice/Ko normal shinkafa dangote Yadda ake hadawa Farko idan basmati rice za ki yi amf...

 • Yadda ake hada juice na abarba da kankana

  Posted Feb 7

  Assalamu alaikum, barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. A yau kuma zan nuna mana yadda ake hada wani juice na kankana da abarba. Abubuwan hadawa Kankana Abarba Sugar Flavour Yadda ake hadawa Farko za ki cire yayan kankana sai ki sa a ...

 • Yadda ake hada juice na lemu da carrots

  Posted Feb 7

  Assalamu alaikum, barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. A yau kuma zan nuna mana yadda ake hada juice mocktail na lemu da karas. Abubuwan hadawa Lemu Carrots Sugar Flavour (ko wane iri) Zuma (ba dole ba ne) Ice cubes Yadda ake hadawa ...

View All