Makalu

Tarihin hukumar JAMB da wasu muhimman bayanai game da jarabawar

 • Wannan hukuma ta Joint Admissions and Matriculation Board (JAMB) cibiya ce ta shirya jarabawar share fagen shiga jami’a tare da sauran cibiyoyin karatu, kamar irinsu polytechnics da colleges a duk fadin Najeriya. Kuma mutum zai samu damar yin jarabawar ne matukar dai ya kammala karatunsa na sakandare.

  Shiga Jami’a kafin a kirkiri hukumar JAMB da yadda aka kirkiro hukumar

  Kafin a kirkiri hukumar JAMB, Najeriya tana da jami’o’i ne guda shida zuwa bakwai a shekarar 1974 kenan. Kowace jami’a daga cikinsu tana shirya jarabawarta ne kuma ta dauki adadin daliban da suka yi nasarar cin jarabawar. Ana cikin hakan karkashin jagorancin mulkin Chief Olusegun Obasanjo, a shekarar, sai ya kara kirkirar wasu jami’o’i guda shida (6), sannan sai gwamnatin ta kafa wani kwamiti da zai rika kula da jarabawar ta shiga jami’a karkashin shugabancin Mr. M. S. Angulu.

  Bayan haka, sai wannan kwamitin ya bada shawarar da a kafa wasu hukumomi guda biyu, wato; Central Admission Board da kuma Joint Matriculation Board. Gwamnatin mulkin soja na waccan lokacin ta amshi shawarwarin da kwamitin ya bata inda ta kirkiri Joint Admissions and Matriculation Board. Daga nan sai aka kafa hukumar a shekarar 1978, 13th February a karkashin dokar kundin tsarin mulkin soja ta Nigeria shekarar 1978. (Decree No. 2 of the Federal Military Government of Nigeria).

  Dubi wata makalarTsarin yanki da ganga (phrase and clause structure) a Hausa

  Daga nan, sai a shekarar 1988 watan August aka yi gyara a kundin tsarin mulkin sojan No. 2 decree, inda aka basu iko da damar shirya jarabawar shiga makarantun polytechnics da colleges of education a duk fadin Najeriya. Shi wannan gyaran wato amendments a Turance da aka yi, a wancan lokacin aka tsara shi aka rubuta shi cikin kundin tsarin mulki na soja (Decree No. 33 of 1989, of the Federal Military Government).

  To ko ya ya ake yin jarabawar ta JAMB?

  A da anayin jarabawar ta JAMB ne da takarda da pencil wato abinda aka fi sani da Paper and Pencil. Amma a shekarar 2012 Registrar na hukumar JAMB din a wancan lokacin ya bada sanarwar cewa yanzu jarabawar za ta kasance ne ta dayan hanyoyi uku:

  1. Paper and Pencil Testing (PPT): Inda za a yi jarabawar da takarda da pencil.
  2. Dual Based Test (DBT): Inda za a kawo tambayoyin a kwamfyuta amma sai a amsa su a takarda.
  3. Computer Based Test (CBT): Shi kuma anan da tambayoyin da kuma amsoshin duka zai zama ne a cikin komfyuta din.

  Hakan ya faru ne sakamakon wasu da dama daga cikin dalibai suna rasa sakamakon jarabawar ta su saboda bacewar takardar da suka amsa jarabawar.

  Hakanan wannan jarabawa ana yin ta ne sau daya a shekara inda a kowace shekara ake samun kimanin dalibai miliyan daya da suke zaunawa jarabawar. Kuma jarabawar tana da darasi hudu ne, darussan sune; English Language wanda dole ne sai kowanne dalibi ya yi shi, sai kuma sauran darasi uku da suke da alaka da kwas (Course) din da mutum ke son karantawa a jami’ar.

  Sannan jarabawar tana dauke ne da tambayoyi guda dari biyu da hamsin ne (250), inda English ya ke da tambaya 100, sauran darusa ukun kuma suna da hamsin hamsin (50). Amma a shekarar 2017 an rage yawan tambayoyin inda aka dawo da su 180, English na da 60, sauran darusan kuma 40 ko wane.

  Haka zalika kuma jarabawar a shekarun baya tana da lokaci ne daya kai tsawon awa uku da minti goma (3 hours, 10 minutes). Yanzu shi ma an rage inda aka mayar da shi awa biyu kacal (2 hours). Sai dai adadin maki din jarabawar yananan yadda yake bai canja ba, wato maki 400.

  To maki nawa ake so mutum ya samu don cin wannan jarabawa na JAMB?

  Abinda kowa ya sani game da mafi karancin makin JAMB shine 180. Amma a kwai canje-canje da aka yi ta samu a shekarun da suka gabata. A shekarar 2007 mafi karancin makin din 160 ne, a shekarar 2008 kuma aka kara shi ya zama 170, kana kuma a shekarar 2009 aka mayar da shi 180, sai a 2017 aka dawo da shi 120 a shekarar 2018 kuma aka mayar da shi 140. Amma a wannan shekarar ta 2019 ba mu san nawa ne za su ce ba, sakamakon sai hukumar ta JAMB ta zauna da duka wakilan Jami'o'i da kwalejoji da sauran su dan tattaunawa akan abinda ya kamata a saka. Hakan kuma yana zuwa ne bayan an gama jarrabawar ta JAMB.

  Za a iya dubaPhysics: Misalan lissafin vector

  Wani abin lura anan: Ku sani kowace university tana da adadin maki din da take so, ya danganta ne da irin kwas din da mutum ke so ya karanta. Ba lallai ne dan ka ci maki 180, ko 140 ba ka samu admission.

  Ya ya zan yi in shiga jami’a ta hanyar JAMB?

  Wannan abu ne mai sauki, kawai abinda za ka yi shine ka je ka bude profile a shafin yanar gizo na JAMB (ku duba adireshin shafin a karshen wannan makala), daga nan sai ka je banki ka biya kudi, su kuma bankin za su baka wata lamba da ake ce ma e-pin, to idan suka baka sai ka je daya daga cikin ofishin hukumar ta JAMB don yin rajista ko kuma ka je daya daga cikin cibiyoyin (centers) din da hukumar ta basu lasisin yin jarabawar. Kar ka manta, idan za ka tafi sai ka je da O' level dinka (WAEC/NECO/Nbais/NABTEB).

  Sannan ka tabbata ka ci darasin English da ilimin lissafi (Mathematics) kuma ka tabbata ka ci darasin da ya ke da alaka da kwas din da ka ke so ka karanta a jami’ar, domin wannan dole ne kafin jami’a su dauke mutum. 

  To daganan idan lokacin jarabawar ya yi za su sanar da ku. Ka shirya sosai don tabbatar da ka ci maki da bai gaza wanda ake bukata ba a kwas din da kake son karantawa. To idan ka yi nasarar cin jarabawar, jami’ar da ka nema za ta baka admission inda zaka fara daga aji daya (Level 100/Level 1/ UG 1) to shikenan ka shiga jami’a!

  Sannan za ka yi shekara hudu a jami’ar idan kwas din mai shekara hudu ne, ko kuma biyar idan mai shekara biyar ne.

  Kuna iya karanta makala ta gaba don ganin ire-iren matsalolin da dalibai ke fuskanta wajen rubuta jarabawar JAMB.

  References

  • Prof. ‘Dibu Ojerinde (Registrar/CE/JAMB), Abuja, Nigeria: Using assessment for the improvement of tertiary education in Nigeria: The Joint Admissions and Matriculation Board (JAMB)
  • Joint Admissions and Matriculation Board Act
  • www.jamb.gov.ng
  • Sahara Reporters (Sep. 25, 2008) JAMB 2019/2020

  Wannan rubutu ya zo muku ne daga, kungiyar Arewa Students Orientation Forum (ASOF). ASOF kungiyar ce mai wayar da kan dalibai akan dukkan al'amuran da suka shafi karatunsu.

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Tasirin fina-finai a kan al’adun Hausawa: Keɓaɓɓen nazari a kan wasu Ɗabi’u na musamman a cikin fina-finan Hausa

  Posted Wed at 1:07 PM

  Maƙalar da aka Shirya Gabatarwa a Taron Ƙara wa Juna Sani na Ƙasa-da-ƙasa a Kan Gudummuwar Fasaha ga ci Gaba, Wanda Tsangayar Fasaha da Addinin Musulunci, Jami’ar Bayero, Kano ta Shirya, Daga Ranar Laraba 5 ga Watan Oktoba Zuwa Ranar Asabat 8 ga Watan Oktoba, Shek...

 • Abubuwan da suke karya azumi

  Posted Mon at 1:07 PM

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa, da wadanda suka biyo bayansu har zuwa rananr sakamako. A wata makala da ta gabata mun yi bayani akan falalar azumin watan Ramalana inda muka ka...

 • Yadda ake hada tuna muffins

  Posted May 19

  Asaalamu alaikum, barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya a yau. Zamu yi bayanin yadda ake hada tuna cheese muffins ne a yau. Abubuwan hadawa Tuna fish 2 Kwai 2 Gishiri Yaji Grated karas Corn flour Yankakken tattasai Yankakken koren tattasai ...

 • Jaye karar tsana: Uzuri da tuni daga mantuwa

  Posted May 16

  Ta Abu-Ubaida SANI Department of Languages and Cultures Federal University Gusau, Zamfara Phone No: 08133529736 Email: abuubaidasani5@gmail.com   1. Ya Allah mahalaccin komai,                  Wanda ya ƙaga yawan...

 • Kadan daga cikin falalar azumin watan Ramalana

  Posted May 14

  Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da alayensa da sahabbansa, da wadanda suka biyo bayansu da kyautata. Yana daga hikimar Allah Madaukakin Sarki fifita wasu mutane akan wasu, Ya kuma fifita wasu wurare aka...

View All