Makalu

Ire-iren matsalolin da dalibai ke fuskanta game da jarabawar JAMB

 • Assalamu alaikum wa rahmatullah. A yau zamu yi magana ne akan ire-iren matsalolin da dalibai ke fuskanta yayin jarabawar JAMB. Tabbas dalibai suna fuskantar matsaloli masu tarin yawa, wanda daman mun yi alkawari zamu dauke su daya bayan daya muyi bayani a kai.

  Matsaloli kamar, misali a lokacin rajistar JAMB dinka kai namiji ne amma sai aka sa maka female, ko a sanya maka email mara kyau, ko kuma a sanja maka jihar da ka ke, ko ranar haihuwa. Wadannan matsalolin dole sai dalibi ya lura sosai a lokacin rajistar JAMB dinsa dan kauce musu.

  Abu na farko da zaka yi shine lokacin da zaka yi rajista ta jamb ka nutsu sosai, kuma a baka form ka cika, sannan duk abunda ka manta yadda yake to kar ka cika da ka, ka bari sai ka tabbatar. Kamar misali, kana shakkar shin a watan May ne aka haifeni ko March, to kar ka cika ka bari sai ka tabbatar da watan ta hanyar duba Birth Certificate dinka. Bayan ka gama cika Form din kuma sai kasa ido sosai akan monitor (allon kwamfyutar) domin kaucewa matsalolin. Sannan duk abunda ka gani an rubuta maka ba dai-dai ba to kar ka yi shiru ka yi magana a gyara maka. Wannan kenan. Ga wasu daga cikin matsalolin a jere kamar haka:

  1. Date of Birth
  2. Home Town
  3. Gender
  4. UTME Combination
  5. Name/Typing Error
  6. E-MAIL Address

  Date of birth (ranar haihuwa)

  Dalibai suna samun matsala sosai wurin yin online registration na jamb ta bangaren shekarun haihuwa. Sanya shekarun haihuwarka daidai da yadda yake a Declaration of Age dinka ko kuma Birth Certificate yana da matukar muhimmanci kwarai da gaske. Dan haka ka tabbata ka saka shi daidai yadda yake dan kaucewa biyan kudin Correction Data.

  Mafi yawancin wannan matsalar tana faruwa ne idan kayi rajistar a gun wadanda basu kware sosai ba, ko kuma suna sauri suyi su sallemaka dan suyima wasu.

  Sannan kuma duk wanda bayida takardar haihuwa (Birth Certificate) ko kuma Declaration of Age to kafin ya cika form dinshi na jamb ya tabbata yaje ya yi Declaration of Age din (Shi wannan Declaration of Age din a kotu ne akeyi, zaka biya 200 Naira ko makamancin haka). Idan kuma ba haka ba to ka tabbata date of Birth dinda ka saka a Jamb dinka shi zaka saka a Declaration of Age dinka a duk lokacinda kaje zakayi.

  Rashin saka date of birth din daidai ka iya hana maka zuwa aikin hidimtawa kasa wato National Youth Service Corps (NYSC). Misali, an haifeka a 10-10-1998 sai aka kuskure aka saka maka 10-10-1988 to kaga idan ka lissafa za ka ga koda zaka gama degree din naka kenan kana da kusan shekara 38 a duniya, to kuma a ka'idar NYSC duk wanda ya kai shekara 30 to ba zai je bautar kasar ba. A lokacin kuma idan kana so a gyara maka ta yadda zaka iya zuwa bautar kasar sai ka biya kimanin kudi Naira 20,000 wannan fa ina maganar 2017/2018 ne, ya kuke tunanen kudin zasu iya kaiwa nan da shekara hudu zuwa biyar. Dan haka sai a kula Sosai.

  Home Town (Inda ka ke zaune/Inda za ka yi JAMB din)

  Wannan shima matsala ne da dalibai suke fuskanta a lokacin yin jarabawar tasu ta JAMB. Ku lura akwai bambanci tsakanin examination town da kuma Home Town. Examination town shine inda ka ke so ka yi jarabawar JAMB din naka. Misali:

  1. Examination town: Kaduna
  2. Local Government: Zaria

  To kenan ka ga za ka yi JAMB din taka ne a jihar Kaduna, sannan a Kaduna din kuma a Local Government din Zaria, to a cikin Local Government din sune zasu turaka inda su ka ga dama. Wannan shine Examination town na ka, dan haka Hukumar JAMB ba ta da lasisin da zata turaka wuri mai nisa duk inda kaga an tura ka to kai ne ka cika can din.

  Za a iya duba: Physics: Bayanai game da gas laws

  Karin bayani:

  Kuma ba wai dole sai a jihar ku ko a Local Government dinku ne kawai za ka iya yin JAMB din ba. Misali idan kai dan Sokoto ne ka ga dama ka ci ka Kano, a matsayin State of examination, Fagge a matsayin Local Government of examination, to su kuma sai su duba centres din da ke cikin Fagge Local Government su turaka duk wace suka ga dama.

  Shi kuma Home Town shine: Asalin Jihar ka, Local Government dinka, da Anguwar ku. Misali:

  1. State of Origin: Kebbi
  2. Local Govt. of Origin: Sakaba
  3. Address: Tudun wada, Sakaba No. 12

  Matsalolin da zaka iya samu idan baka saka wadannan bayanai daidai ba

  1. Zaka iya rasa scholarship. Dalili kuwa su hukumar makaranta suna amfani ne da jihar da ka saka a jamb din naka. Dan haka yanzu su kuma gwamnoni sun gano cewa ana yi masu cuwa-cuwa wurin tantance daliban jihar su da suke karatu a kowace Tertiary Institution. To sai suka bullo da dabara, dabarar ita ce suna amsar list din daliban jihar su ne baki daya daga hannun hukumar makaranta, to kaga idan a Jamb dinka ba jihar ku ka saka ba to ita makaranta a wurinta kai ba dan jihar ba ne, dan haka jihar ta ku ba zata baka scholarship ba koda kuwa kanada Indigene.
  2. Zaka yi biyu babu. Su can Jihar da ka saka basu san da kai ba, dan idan sun zo screening exercise na scholarship din ba lallai ne su baka ba, saboda za su yita yi maka tambayoyin da indai kai dan garin ne dole ka iya amsawa, idan kuwa ka kasa amsawa to alamu karya ka ke yi kenan kai ba dan Jihar bane. Ita kuma jihar taka ta asali babu sunan ka a cikin 'yan jihar ka ga babu ma abunda za ka ce.
  3. Duniya kullum kara wayewa ta ke yi. Idan a JAMB dinka ka saka cewa kai dan Kano ne, to mai yasa kuma a SSCE dinka kace kai dan Zamfara ne haka ma Primary Certificate dinka, watakila ma har da Voters Card dinka da.

  Sai kuma matsalolin da dalibai ke fuskanta bayan kammala rajistar JAMB dinsu. Matsalolin sun hada da:

  1. Manta E-Mail password
  2. Manta Profile code
  3. Faduwar Slip
  4. Rashin sanin gurin jarrabawar
  5. An turani wani gari bansan inda zan kwana daya ba, da sauran wasu matsalolin.

  Tabbas wadannan matsalolin suna tada hankalin dalibai ainun. Dan haka da yardar Allah zamu dauki kowacce matsala daya bayan daya muyi cikakken bayani akai, ta yadda za a kaucewa matsalar, da kuma yadda za a magance ta idan ta faru, Insha Allah.

  Ku kasance tare da kungiyar ASOF a koda yaushe, dan sanin halin da Ilimi ya ke a kasar. 

  Mai karatu na iya karantaTarihin hukumar jamb da wasu muhimman bayanai game da jarabawar

  Wannan rubutu ya zo muku ne daga, kungiyar Arewa Students Orientation Forum (ASOF). ASOF kungiyar ce mai wayar da kan dalibai akan dukkan al'amuran da suka shafi karatunsu.

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Hanyoyi guda biyar na rage ƙiba ba tare da an shiga hatsari ba

  Posted Jun 12

  A duniyarmu ta yau, ƙiba na daya daga cikin matsalolin da ke addabar mutane da dama. Saboda irin ci gaba da aka samu na yawaitar abinci kala-kala – abincin gargajiya da na zamani, na gwangwani da na gona – ya sa da yawa mutane na yawaita cin abincin da zai k...

 • Sharudda da kuma ladubbar sallar idi karama

  Posted Jun 3

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da iyalansa da Sahabbansa baki daya. Idi shine duk abinda yake dawowa yana maimaituwa lokaci zuwa lokaci, kamar sati-sati, ko wata-wata, ko shekara-shekara. Shar'anta s...

 • Hukunce-hukuncen zakkar fidda kai

  Posted May 31

  Ma'anar zakkar fidda kai: Sadaka ce wacce ake bayar da ita sakamakon kammala azumin watan Ramadan. An shar'anta zakkar ne a shekara ta biyu bayan hijirar Annabi sallallahu alaihi wa sallam daga Makkah zuwa Madinah, a shekarar da aka wajabta azumin watan Ramadan. Huku...

 • Yadda ake hada local jollof rice

  Posted May 30

  Assalamu alaikum barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. Barka da shan ruwa. Yau zamu koyi yadda ake hada local jollof rice wato dafa dukan shinkafa ke nan da Hausa. Abubuwan hadawa Shinkafa Tattasai da tarugu Daddawa Albasa Seasoning Manja Ta...

 • Yadda ake hada bitter leaf soup

  Posted May 30

  Assalamu alaikum, barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya na yau. Barka da shan ruwa. A yau zamu duba yadda za ki hada bitter leaf soup (miyan shuwaka). Abubuwan hadawa Manja Nama Seasoning Garlic  Ginger Shuwaka (bitter leaf) Tattasai Ta...

View All