Makalu

Abubuwan da dalibanmu ya kamata su sani kafin rubuta JAMB, WAEC da NECO

 • A yau za mu ci gaba ne da tattaunawarmu akan jarabawar JAMB da muka faro a baya. Idan mai karatu na bukatar sanin abinda muka yi a baya zai iya duba inda muka tattauna akan Ire-iren matsalolin da dalibai ke fuskanta game da jarabawar JAMB.

  Insha Allah za mu ci gaba daga inda muka tsaya. Za mu duba:

  1. JAMB awaiting Result.
  2. Kalubale ga dalibai
  3. Wanne shiri ka ke yi?

  ASOF ta yi nazari tare da samo bakin zaren. Kamar yanda ku ka sani mafi yawanci dalibai yan aji uku (SS3) na sakandare suna cika JAMB din su a abinda ake kira ‘awaiting result’ ne.

  Mene ne awaiting result?

  Wata dama ce da aka bawa daliban sakandare yan aji uku, ko kuma wadanda sun gama sakandire din amman Jarrabawarsu ta SSC (NECO/WAEC) ba ta yi kyau ba ko ba su ci Turanci da Lissafi ba. Shine suke amfani da wannan damar wajen rajistar JAMB, ya yin da babu SSCE result. Amma da niyar za su kawo saboda za su rubuta jarrabawar WAEC da NECO duk dai a wannan shekarar.

  Abun tambayar shin wani shiri ka ke yi domin tunkarar wannan aikin da ya ke gabanka?

  A lokuta mabanbanta kungiyar ASOF ta na cin karo da daliban da suka ci jarrabawar JAMB sosai wasu ma sama da 200 amma kash da Jarrabawar su ta NECO ta fito sai kaga basu ci Turanci ko Lissafi ba, wanda kuma wannan ginshiki ne a batun jami’o'inmu.

  Misali, a shekarar da ta gabata akwai wani dalibi a jami’ar Bayero ya ci maki sama da 200 har an ba shi admission amma fa bai iya haye screening ba, sakamakon bai ci English ba.

  Saboda haka yana da kyau dalibai iyayen daliban ko yayyensu ma'ana majibantan lamuransu su sani:

  Abu na farko: Ya kamata kowanne dalibi ya sani cewa koda ya ci JAMB to ba zai samu admission ba dole sai ya ci jarrabawar WAEC ko NECO akalla Credit biyar. Wannan Credit biyar din kuma dole ya kunshi Turanci da Lissafi (English/Math).

  Na biyu:  Ya kamata iyaye su fahimci hakan, kuma su mai da hankali sosai wajen bawa 'ya'yansu, hadin kai da kuma daura su akan hanyar da za su iya cin dukkan jarrabawowin guda biyu wato JAMB da kuma WAEC ko NECO domin ta haka ne dalibi zai samu damar zuwa jami'a ko wata makarantar gaba da sikandire.

  Abu na uku: Rashin litattafan karatu, wannan wata babbar illa ce ga dalibanmu. Wanda basa mallakar littafin karatu misali, kai dalibi ne da za ka rubuta jarrabawar NECO ya yin da za ka yi Economic, Govermment da Math amma kuma baka da littafin ko daya daga cikin su, balle ka yi nazari da karatu, balle kaje gida wajen wani ya kara fahimtar da kai, kawai dai ka zauna kana jiran ranar jarrabawar, wata kilama kai zumudi ka ke yi na zuwan jarrabawar.

  Abu na hudu: Wannan kuwa babban barazana ce ga iliminmu. Abinda ya dace a ce kowanne dalibin sikandire da zai rubuta NECO ko WAEC yana dukufa ne wajen neman hanyar da zai yi nasara. Ta hanyar dagewa da karatu da kuma haduwa da dalibai domin yin group discussion domin a taimaki juna. Amma a yanzu abun takaici mafi yawanci dalibanmu sun fi mai da hankali da kuma dogaro akan azo a basu amsa ranar jarrabawar. Wannan kuma ya samo asali ne yayin da daliban ba su dage da karatu ba ko kuma ba'a koyar dasu yanda ya dace ba.

  Muddin dalibi idan ya dogara da wannan to tabbas zai fuskanci kalubale guda biyu. Na farko tayuwu a ranar da dalibi zai rubuta English ko Math a turo musu invigilator din da bazai yadda a bada amsa a wannan ranar ba. Hakan yana nufin duk dalibin da ya ke dogara da a bashi amsa a wannan ranar ya fadi jarrabawar English wacce akafi so. Kuma a ranar English din anfi turo invigilator mai tsanani. Kalubale na biyu da dalibin zai fuskanta shine, bayan ya tafi jami'a ko wata makarantar gaba da sakandare zai sha wahala saboda bai yi karatu a sakandare ba, kuma a karatun da ake yi a chan ne za a dora a ci gaba. Ya zama wajibi mu yi amfani da gyararran tunaninmu wajen kawo gyara a wannan bangaren, musamman ma iyayen daliban da kuma yayyensu, domin kaucewa irin wannan matsalar.

  Dole Dalibi ya yi karatu, kuma yamallaki kayan karatun gwargwadon ikon sa! Haka kuma dole ya yi shiri sosai domin tunkarar jarrabawarsa kowacce iri ce.

  Dan'uwa cikar burin ka na zama lauya, ko likita, ko injiniya, ko direban jirgi ko soja ba zai yuwu ba a yayin da ka ke gida a kwance dole sai ka fito ka zage damtse ka tunkari dukkan kalubalen da zai iya bijiro maka domin hanaka cimma burinka. Kuma ka yi tunani ka waiwaya baya, duk wanda suka cimma burinsu suma hakan ta faru da su.

  Me ya sa na fadi jarrabawar JAMB?

  Kungiyar ASOF ta damu matukar damuwa wajen ganin yawan daliban Arewa da suke faduwa jarrabawar JAMB. Da yawa daga cikin wadanda ASOF ta zanta da su, wasu sun yi jarrabawar JAMB so biyu wasu so uku wani ma da ASOF. ta tattauna da shi so biyar ya yi JAMB bai ci ba.

  A ina matsalar take? Shin ban iya computer ba ne? Shin ban iya karatun ba ne?

  Mece ce matsalar?

  Amsar wannan tambayar ta na kunshe ne a abunda ka iya hararowa kai da kanka ko kuma wani wanda ya fahimci hakikanin matsalar ka. 

  Ga wasu dalilai da ke saka dalibai faduwan wannan jarabawar kamar haka:

  Rashin samun good background (tushe mai kyau)

  Sanin kowa ne ba a yin gini sai da foundation, to a bangaren ilimi ma haka abin ya ke, matukar dalibi baifito daga makarantar da'akeyin karatu ba to kuwa ba zai yi karatunba. Domin Hausawa suna cewa ice tun yana danye ake malkwasashi idan ya bushe sai dai ya karye. Matukar dalibi ya fito daga makarantar da ba a karatu to zai dauka ko ina ma haka ya ke. Saboda haka zai dauka cin jarrabawa ma ba sai anyi karatu ba. Hakan kuwa zai saka shi ya sakankance akan hakan daga bisani kuma idan ya yi jarrabawar JAMB ya fadi, to anan ne zai gane cewa tunaninsa ba mai kyau ba ne.

  Mafita

  Yana da kyau iyaye su fahimci makarantun da ya dace su kai 'ya'yansu, ma'ana makarantun da aka tabbatar da cewa suna karatu yadda ya kamata. Sannan ga daliban da aka bawa mulki a makarantun Secondary su tabbatar da cewa dadin mulki bai dauke musu hankali ya hana su karatu ba.

  Sannan koda iyaye ba su fahimci cewa makarantarku ba a karatu ba, ka/ki yi kokari ki sanar da su da zarar kin fuskanci hakan domin adauki mataki.

  Yarda/dogara da wasu wadanda su ke kiran kansu exam helpers

  A zahirin gaskiya wannan matsala ce da ta zama ruwan dare game duniya, domin kuwa a halin yanzu akwai wasu mutane da suke karbar kudade a hannun dalibai da sunan exam helpers. Kuma tabbas hakan yana haifar da matsaloli ga daliban da suka yarda suka bada kudinsu da sunan za a taimaka musu su ci jarrabawa. Kai ni naga wanima wanda ya ke cewa dalibai ba sai sun yi karatu ba suna zuwa kawai za suga an amsa musu jarrabawar sai dai su yi submitting. Wannan kuwa ba karamar matsala ba ce, domin babu wanda ya isa ya hau system din JAMB ta harya amsa maka tambayoyi.

  Wasu kuma suna cewa zasu turo maka amsar jarrabawar, ana saura awa 2 ko 3 ka/KI shiga wannan jarrabawa, wanda wannan duk ba gaskiya ba ne.

  Shawarwari akan wannan matsalar

  1. Kada ka yarda wani mutum ya karbi kudinka da sunan exam helpers.
  2. Sannan kada ka fadawa wani registration number ka ko profile password dinka, saboda da shi suke amfani su shirya amsoshinsu na karya, su ce wai questions dinka ne su karbi kudi a gurinka.
  3. Kuma dan Allah wadanda suke yin wannan hali su bari domin a cikinmu su ke.
  4. Yakamata hukumar JAMB ta dinga daukar mataki akan duk wanda aka kama yana karbar kudade a hannun dalibai da sunan zai taimaka musu a jarrabawa.

  Wannan rubutu ya zo muku ne daga, kungiyar Arewa Students Orientation Forum (ASOF). ASOF kungiyar ce mai wayar da kan dalibai akan dukkan al'amuran da suka shafi karatunsu.

  Photo credit: Youth Village

Comments

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Wai shin mene ne data da kamfanonin layukan waya ke sayar mana?

  Posted Oct 13

  Kamar wata biyu da su ka wuce, Mallam Rabiu Biyora ya yi tambaya akan DATA da mu ke saye daga kamfunan waya inda ya ke cewa "DATA da kamfanonin layukan waya ke siyar mana, har muke amfani da ita wajen hawa Internet, su kamfanonin siyowa suke daga kasuwar siyar...

 • Egg and vegetable pocket

  Posted Oct 9

  A yau makalarmu ta girke-grken zamani zat yi bayani ne akan yadda ake hada wani abincin zamani mai suna egg and vegetable pocket. Ga yadda ake yin sa kamar haka: Abubuwan hadawa Filawa kofi biyu (flour 2cups) Baking powder 1½tsp (karamin cokali) Butter coka...

 • Rayuwar zamani: Babi na biyu

  Posted Oct 6

  Dedicated to Autan Hikima. Raihan na komawa office ya aiki masinga akan yaje yace ma head din ko wani department yana son ganinsa aconference hall, babu 6ata lokaci duk yabi ya fadamusu kafin ya koma ya sanar da zuwansu. Yana zaune a office kafin ya fara komai yaga ho...

 • Yadda ake hada sausages sultan chips

  Posted Oct 6

  Assalamu alaikum, barka da sake saduwa a cikin shirinmu na Bakandamiya. A yau Insha Allahu zamu yi bayanin yadda za ki hada sausages sultan chips. Abubuwan hadawa Dankali (irish) Sausages Carrots Albasa Tattasai da tarugu Man gyada Green peas Green pepper M...

 • Rayuwar zamani: Babi na daya

  Posted Oct 4

  Sulaiman bai yi mamakin ganinta ahakan ba domin hakan dabiar tace. taku take cikin isa da gadara irinta 'ya'yan masu kud'i y'a'yan masu hannu da shuni, Muhievert kenan yarinya fara doguwa kyakyawa, gata da k'ira mai kyau tsaruwarta ya zarce duk inda mutun ke tunani. Aka...

View All