Makalu

Shar’antattu daga cikin ladubban mai yin azumi

 • Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da alayensa da sahabbansa baki daya.

  Lallai Allah Ya shar'anta wasu ladubba ga ibadar azumi, wanda ya dace mumini ya yi riko da su, saboda ya yi azuminsa cikin cikakkiyar sura, don ya samu cikakkiyar lada.

  Daga cikin ladubban mai yin azumi akwai wadanda suke na wajibi ta yadda in mai azumi ya bar su zai samu zunubi, akwai kuma wadanda suke na mustahabbi ne, mai azumi zai samu lada in ya aikata su.

  Kafin ku duba wadannan ladubba na mai azumi, kuna iya duba wata makalar da ta yi sharhi akan abubuwan da yakamata musulmi ya yi lokacin shigowar watan ramalana.

  A yanzu, ga kadan daga cikin ladubban mai yin azumi:

  Tsarkake niyya

  Wajibi ne ga musulmi ya nemi lada da kuma yardar Allah da azuminsa; kada ya yi azuminsa don neman wani abin duniya. Saboda Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: "Wanda ya yi azumin watan Ramalana, yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa". Bukhari da Muslim ne suka rawaito wannan hadisi.

  Cin abincin sahur

  Mustahabbi ne mai azumi ya ci abincin sahur, saboda zai taimaka masa, kuma akwai albarka a cikinsa.

  Akwai hadisai masu yawa da suka tabbata daga Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) wadanda suke nuna falallar Sahur d a kuma umurni akan sa.

  An karbo daga Anas Bin Malik (Allah Ya yarda da shi) ya ce: ‘Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: "Ku yi sahur, saboda cikin cin abincin sahur akwai albarka"’. Bukhari da Muslim ne suka rawaito hadisin. Haka nan an karbo daga Amr Bin Al-Aas (Allah Ya yarda da shi), Lalle Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: "Abinda ya bambanta azuminmu da na Ahlul kitabi shine abincin sahur". Musulim ne ya rawaito shi.

  Mustahabbi ne jinkirta sahur. An karbo daga Anas (Allah Ya yarda da shi) daga Zaid Bin Sabit (Allah Ya yarda da shi), yace: "Mun yi sahur tare da Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), sai muka tashi zuwa ga sallah". Sai na ce: Nawa ne gwargwadon tsakanin sahur da sallah? Sai yace: "Ayoyi hamsin". Buhari da Muslim ne suka rawaito shi.

  Mustahabbi ne ga mai azumi ya shagaltu da zikiri da nafilfilu, da sauran ayyukan kwarai

  Yana da kyau mai azumi a koda yaushe ya kasance cikin ayyuka kyawawa kamar karatun al-Kur'ani da addu'a da tasbihi da istigfari da sadaka da kyautatawa musulmai, da sauran ayyukan da zasu kusantar da bawa ga Ubangirinsa.

  An karbo daga Ibn Abbas (R.A), yace: ‘Manzon Allah ya kasance ya fi kowa kyauta, kuma kyautarsa ta fi yawaita a watan Ramadan; lokacin da mala'ika Jibrilu yake haduwa da shi, kuma Jibrilu ya kan hadu da shi ne a cikin kowani dare, sai yayi bitar Al-Kur'ani tare da shi. Lalle Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya fi iska mai kadawa yin alheri"’. Buhari da Muslim ne suka rawaito shi.

  Kana ciyar da mai azumi yana da falala mai yawa. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) Ya ce: "Duk wanda ya ciyar da mai azumi abin buda baki, to yana da lada kwatankwacin ladan mai azumin, ba tare da an rage wa mai azumin ladarsa ba". Imam Ahmad da Tirmizi da Ibn Majah ne suka rawaito hadisin.

  Mai karatu na iya duba wata makala da ta yi bayani akan kadan daga cikin falalar azumin watan Ramalana.

  Ya wajaba ga mai azumi ya kiyaye azuminsa daga yasasshen zance da karya da duk sauran ayyukan sabo

  Irin wadannan munanan ayyuka da aka ambata suna rage wa mai azumi ladansa. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) y ace: "Wanda bai bar karya da aiki da shi ba, to Allah ba ya bukatar ya bar cin sa da shan sa". Buhari ne Ya ruwaito shi.

  Jabir (Allah Ya yarda da shi) yace: "Idan ka yi azumi, to jin ka da ganin ka da harshen ka su kame daga karya da sabo, kuma ka bar cutar da makwabci. Kuma ya zama kana da nitsuwa ranar azumin ka. Kar ya zama ranar azumin ka da ranar da baka azumi su zama daya".

  Barin musu da zage-zage da fushi da fada da mutane

  Daga cikin laduban mai azumi, ana so mai azumi ya bar musu da zagi da fushi da fada da mutane. Duk wanda ya nemi ya zage shi ko ya buge shi, to ya ce masa shi mai azumi ne. Ya zo a hadisil kudusi: Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) yace: ‘Allah Yace: "Idan ranar azumin dayan ku ta zo, to kada ya yi kwarkwasa (batsa cikin zance da iyali ko jima'i), kada ya yi ihu. Idan wani ya nemi zagin sa ko yin fada da shi, to ya ce masa ni mutum ne mai azumi". Buhari da Muslim ne suka rawaito hadisin.

  Yin addu'a kafin buda baki da lokacin buda baki

  Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: "Lallai mai azumi yana da addu'a da ba'a mayar da ita idan ya zo buda baki". Ibn Majah ne ya rawaito wannan hadisi.

  Kuma ya tabbata Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya kan ce bayan buda baki: "ZAHABAZ ZAM'U, WABTALLATIL URUKU, WA SABATAL AJRU IN SHA ALLAH". Ma'ana: "Kishin ruwa ya tafi, jijiyoyi sun jike, kuma lada ya tabbata in Allah Ya so". Abu Dawud ne ya rawoto shi.

  Gaggauta buda baki

  Da zarar rana ta fadi ana so mai azumi ya gaggauta yin buda baki. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: "Mutane ba zasu gushe cikin alheri ba, matukar suna gaggauta buda baki". Buhari da Muslim ne suka rawaito hadisin.

  Mustahabbi ne yin buda baki da danyen dabino wanda bai bushe ba

  Yana daga cikin ladubban mai yin azumi, yin buda baki da danyen dabino. Idan kuma ba a samu danye ba, to sai a yi da busasshe, in kuma ba a samu ba, to sai a yi da ruwa. An karbo daga Anas (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya kasance yana buda baki da dabino danye (wanda bai bushe ba), gabannin ya yi sallah, in kuma bai samu danyen dabinon ba sai ya yi da busasshen dabino, in kuma bai samu ba to sai ya sha ruwa”. Abu Dawud da Tirmizi ne suka rawito hadisin.

  Yin sallar tarawihi

  Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: "Wanda ya yi tsayuwar sallah a watan Ramalana, yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa". Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.

  Yana da kyau musulmi ya yi sallolin tarawihi tare da jama'a, kuma yayi kokari ya jira har sai an kare sallar tare da liman, saboda ya samu ladan wanda yayi tsayuwar dare. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: "Duk wanda ya tsaya tare da liman har ya gama, to za'a rubuta masa tsayuwar dare". Tirmizi da Nasa'I da Ibn Majah ne suka rawaito shi.

  Mustabbai ne yin Umrah cikin watan Ramalana

  Ga wanda duk Allah ya bashi iko, yin Umurah cikin watan Ramalana yana da falala mai yawa. An karbo daga Abdullahi Bin Abbas (R.A), Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: "Umrah a cikin Ramadan tana daidai da aikin hajji, ko (tana daidai da) hajji tare da ni". (Buhari da Muslim ne suka rawaito shi).

  Sai dai malamai sun yi bayani cewa wannan hadisin ba yana nufi cewa Umuran watan Ramalana ya dauken Hajjin farilla ba ne. Yana nufin cewa ladan Umuran da aka yi cikin watan Ramalana yana daidai da ladan Hajji ne. Allah Shi ne masani.

  Kuma muna fata Allah Ya karba mana ibadunmu, amin.

  Hari la yau, mai karatu na iya duba wata makalar da ta yi nazari akan abubuwan da suke karya azumi.

Comments

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Dalilan da ka iya sawa a koma vegan diet

  Posted Sep 2

  A ‘yan shekaru kadan da suka wuce, kafar yada labarai ta kasar Amurka mai suna USA Today ta ruwaito cewa kashi 50% na mutanen kasar Amurka suna ta kokarin su ga sun inganta lafiyarsu ta hanyar kokarin ganin sun rage yadda su ke cin nama da yawa a ciki abincinsu. A...

 • Physics: Darasi akan pressure in fluid

  Posted Aug 29

  Ga definition na pressure a Turance kamar haka; pressure is defined as the force acting perpendicularly per unit area. Idan kuma za a duba equation na shi ne a math, shi kuma ga shi kamar haka: Pressure = Force / Area , shi ne kamar haka,  P = F / A Ga abinda ...

 • Matsalar shaye-shaye a tsakanin matasanmu a yau

  Posted Aug 25

  A wannan Makala za muyi dubi ne zuwa ga wani maudu’i mai muhimmanincin gaske. Za mu duba matsalar shaye-shaye da ya zama tamkar ruwan dare gama duniya a tsakanin matasanmu maza har da mata a wannan zamani. Duk da cewa wannan mummunar dabi’a ba dabi’a ...

 • Wa ya gaya mi ki cewa yana son ki har cikin zuciyarsa? Ki lura da wadannan alamomi

  Posted Aug 24

  Abu ne mai matuƙar ciwo mace ta fahimci cewa namijin da take so, baya sonta. Baya son kasancewa da ita a rayuwarsa.  Abun takaici irin wadannan mazajen basa iya fadar cewa ba sa son mace a baki, bare har ta san inda dare ya yi ma ta. Sai ya zamo ke a zuciyar ki ki...

 • Maɗigo da yawaitarsa cikin al’umma: Ina mafita?

  Posted Aug 20

  Tasowarmu muna kanana cikin alumma mun ga iyayenmu da sauran magabata suna da aure. Kowa da mahaifinsa da mahaifiyarsa. Hakanan kuma yayin da muke rayuwa mun ga ‘yan mata da samari daban-daban sun taso kuma mun ga sun yi aure. Kuma sannan sa’i da lokaci mutu...

View All