Makalu

Sharudda da kuma ladubbar sallar idi karama

 • Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da iyalansa da Sahabbansa baki daya.

  Idi shine duk abinda yake dawowa yana maimaituwa lokaci zuwa lokaci, kamar sati-sati, ko wata-wata, ko shekara-shekara.

  Shar'anta sallar idin karamar sallah:

  Allah Madaukakin Sarki Ya shar'anta idi guda biyu na musulunci, na sallar azumi da na babbar sallah, saboda mu nuna godiya gare shi kan kamala ibadoji guda biyu masu girma; azumin watan Ramadan da hajjin dakin Allah mai alfarma.

  An karbo daga Anas (Allah Ya yarda da shi) ya ce: Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya zo Madina, ya iske suna da ranaku biyu na wasanni a cikinsu, sai ya tambaya: "Wadanne ranaku ne wadannan?" Sai suka ce: Mun kasance muna wasa a cikinsu a jahiliyya. Sai ya ce: "Hakika Allah Ya musanya muku da mafi alheri daga gare su; Idin karamar sallah da idin babbar sallah". Abu Daudu da Nasa'i ne suka rawaito wannan hadisi.

  Hukuncin sallar idi:

  Malamai sun yi sabani dangane da hukuncin sallar idi zuwa maganganu guda uku:

  1. Sallar idi farillah ce na kifaya, idan sashin mutane suka aikata ta, to sun daukewa sauran mutane, idan kuma babu wandanda suka tashi yin sallar, to duk mutanen garin sun yi laifi. Wannan shine ra'ayin Imam Ahmad.

  2. Sallar idi wajibi ne akan kowani Musulmi. Wannan shine ra'ayin Imam Abu Hanifa.

  3. Sallah idi sunnah ce mai karfi. Wannan shine ra'ayin imam Malik da Shafi'i.

  Magana mafi rinjaye itace ta uku, wato sallar idi sunnah ce mai karfin gaske, ba wajibi bane, saboda dalilai kamar haka:

  4. Salloli na farilla guda biyar ne kamar yadda ya zo a hadisi, wanda wani balaraben kauye ya tambayi Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) dangane da sallolin da suka wajaba akan shi? Sai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: "Salloli biyar cikin dare da wuni", sai balaraben ya ce: Shin akwai wasu a kai na bayan wadannan? Sai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: "A a, sai dai ka yi nafila". Buhari da Muslim ne suka rawaito hadisin.

  5. Da a ce sallar idi wajibi ce, to da ya wajaba ga wanda ta kubuce masa ya rama ta.

  Amma bai halatta ga wanda ya samu dama ya ki zuwa sallar idi ba, saboda Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya dawwama yana fita sallar idi har karshen rayuwarsa, haka kuma sahabbansa a bayansa. Kuma ya yi umurmi da a fita sallar har da matan aure da marasa aure, har da masu haila kamar yadda ya zo a hadisin Ummu Adiyya (Allah Ya yarda da ita).

  Mai karatu na iya duba makamancin wannan makala wacce ta yi nazari akan hukunce-hukuncen ittikafi.

  Yadda ake sallar idi:

  1. Sallar idi raka'a biyu ce, bayan fitowar rana da dagawarta gwargwadon tsawon sandar mashi, har zuwa lokacin da rana zata karkata daga tsakiyar sama.

  2. Ana yin sallar ba tare da an kira sallah ba, ba tare da yin ikama ba. An karbo daga Ibn Abbas (Allah Ya yarda da shi), yace: "Lallai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya yi sallar idi ba tare da kiran sallah ko ikama ba". Abu Dawud ne ya rawito shi.

  3. Kana ana yin kabbarori guda bakwai a raka'ar farko, da kuma kabbarori guda biyar a raka'a ta biyu. An karbo daga Nana Aisha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: "Lallai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya kasance yana kabbarori bakwai a raka'ar farko, a ranar kamar sallah da babbar sallah, kuma yana yin kabbarori biyar a raka'a ta biyu". Abu Dawud ne ya rawito shi.

  4. Ana so liman ya karanta suratul Aala da suratul Gashiya, kamar yadda ya zo a hadisin Nu'uman bin Bashir (Allah Ya yarda da shi). Ko kuma ya karanta suratul 'Kaf da suratul 'Kamar, kamar yadda ya zo a hadisin Ubaidullahi Bin Abdullah (Allah Ya yarda da shi), duka a bayyane ake yin karatun.

  5. Ana yin sallar ne kafin huduba kamar yadda Abdullahi Bin Abbas (Allah Ya yarda da shi) ya rawaito.

  6. Idan ranar idi ta dace da ranar juma'a, to mutane zasu je sallah idi, sa'an nan suna da zabi tsakanin zuwa sallar juma'a ko rashin zuwa. An karbo daga Ibn Abbas (Allah Ya yarda da shi) ya ce: Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: "Idi guda biyu sun hadu a wannan rana ta ku, duk wanda ya so (Idi) ya isar masa Jumma'a, lalle mu zamu halarci juma'a in sha Allah". Ibn Majah ne ya rawaito shi.

  Saboda haka, duk wanda bai samu halartan idi ba, to dole ya halarci Jumma'a. Haka nan limamin Jumma'a shi ma dole ya halarta, saboda ya jagoranci wadanda basu samu idi ba, da kuma wadanda suka halarci idi kuma suke son halartar jumma'a.

  Laduban ranar idi:

  1. Yin wanka da sanya tufafi mai kyau, da sanya turare. Saboda Abdullahi Bin Umar (Allah Ya yarda da shi) ya kasance yana yin wanka a ranar idin karamar sallah kafin ya fita zuwa masallacin idi". Imam Malik ne ya rawaito shi cikin Muwadda. Haka kuma "ya kasance yana sanya mafi kyawun tufafi". Al-Baihaki ne ya rawaito shi.
  2. Sunnah ne cin abinci kafin tafiya sallar idi a ranar karamar sallah. An karbo daga Anas (Allah Ya yarda da shi) ya ce: "Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya kasance baya fita (zuwa idi) har sai ya ci dabino, kuma yana cin su ne wutiri". Buhari ne ya rawaito shi.
  3. Sunnah ne yin kabbarorin idi in za'a tafi sallar idi. Saboda hadisin Ibn Umar (Allah Ya yarda da shi), ya ce: "Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya kasance yana yin kabbarori a ranar idin karamar sallah, lokacin da ya fito daga gidansa har ya je wurin sallah". Dar Al-kudni ne ya rawaito shi.

  Kabbarorin sune: ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA'ILAHA ILLALLAH, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD.

  1. Sunnah ne idan mutum ya je sallah idi ta wata hanya, to in zai dawo gida ya canja wata hanya, ya koma ta wata hanya ta daban. An karbo daga Jabir (Allah Ya yarda da shi) yace: "Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya kasance idan ranar idi ta zo, ya kan canja hanya". Buhari ne ya rawaito shi.
  2. Sunnah ne mutum ya je sallar idi a kafa in akwai halin yin hakan. An karbo daga Aliyu Bin Abi Talib (Allah Ya yarda da shi) yace: "Yana daga sunnah zuwa idi da kafa". Tirmizi ne ya rawaito hadisin.
  3. Wajibi ne musulmai su kauracewa sabon Allah a ranar idi, saboda an shar'anta idin ne don nuna godiya ga Allah Madaukakin Sarki akan kammala azumin watan Ramadan. Saboda haka ya zama wajibi ga iyaye su kula da 'ya'yansu kar su rika cakuduwa maza da mata, haka suturarsu kar ta zama irin ta kafurai, da kuma suturar mata kar ta zama matsastsu, haka nan sauraron kide-kide da sauransu.
  4. Ranar Idi rana ce ta murna da farin ciki, saboda haka babu laifi taya juna murna. An rawaito magabata sukan cewa junansu ranar idi: "TAKABBALLAHU MINNA WA MIN KUM". Ma'ana: Allah Ya karba mana, Ya karba muku.

  Allah Ya karba mana azumin mu, Ya kuma nuna mana azumin badin badada, muna da rai da imani.

  Har ila yau kamar yadda mai karatu ya sani, ana bukar mutum ya yi zakkar fidda kai kafin zuwa sallar idi. Don haka za a iya karanta wannan makala don sanin sharuddan zakkar fidda kai din.

  Hakkin mallakar hoto: isyaku.com

Comments

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Yadda ake hada spinach soup (miyan masa)

  Posted Oct 19

  Asaalamu alaikum, barka da sake saduwa a cikin shirin Bakandamiya. A yau insha Allahu zamu duba yadda uwargida za ta hada miyan masa, kuma wannan miyan za ki iya cin abubuwa dayawa ma da ita. Abubuwan hadawa Manja Albasa da lawashi Kayan miya Naman rago Allayaho...

 • Darasi game da electrical method

  Posted Oct 18

  A makala ta da ta gabata mai suna method of mixture na yi bayanin specific heat capacity yanda ya ke dauke da method guda biyu na measuring dinshi wanda na kawo su kamar haka: Method of mixtures Electrical Method Saboda haka method din lissafinsu ma biyu ne, kuma...

 • Yadda ake grilled sandwich

  Posted Oct 18

  Abubuwan hadawa Biredi mai yanka Soyayyen plantain(agada) Kwai Nama (ki dafa, ki daka) Tarugu (ki jajjaga ko ki yanka) Koren wake (ki yanka) Karas (ki yanka) Kabeji (ki yanka) Maggi Gishiri Butter Abun gashi (manual sandwich grill) Yadda ake hadawa ...

 • Yadda ake hada buttered shape cookies

  Posted Oct 14

  Assalamu alaikum, makalarmu ta yau zamu yi bayani ne akan yadda zaki hada butter shaped cookies Abubuwan hadawa Flour 2 cups Sugar 1 cup Butter 250grm Baking powder 1tspn Kwai 1 Icing sugar Egg white Yadda ake hadawa Farko za ki mixing sugar da butter n...

 • Yadda ake hada red velvet coconut balls

  Posted Oct 14

  Assalamu alaikum barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. Zamu yi bayani akan yadda za ki hada red velvet coconut balls a yau. Abubuwan hadawa Kwakwa Condensed milk Madarar gari Corn flour Red colour Yadda ake hadawa Farko za ki zuba corn ...

View All