Makalu

Sabbin Makalu

View All

Garabasar ranar Arafa

 • Wasu daga cikin yadda za ka/ki tsara yin amfani da ranar Arafat kamar yadda ya da ce don cimma alfanu mai tarin yawa.

  1. Yin bacci da wuri a daren kafin ranar Arafa

  2. Tashi daga bacci kafin lokacin sallar safiya don yin sahur da niyyar daukar azumin ranar Arafa

  3. Sai yin sallar nafila raka’a biyu ko hudu, sannan a tabbatar an yi adu’oi a yayin sujjada na samun duk alherin duniyar nan da na lahira kar a manta a yi wa Allah godiya da Ya ba da ikon ganin wannan rana mai albarka wadda Allah (S.W.T) Ya ke ba da alkhairai da yafiya ga al’umma ma su yawa

  4. Kafin alfijir, ka/ki sance kana/kina mai neman gafarar ubangiji domin a lissafa ka/ki cikin ma su neman gafara da dare.

  5. Ka/ki shirya yin sallar safiya sannan ka/ki kasance ka/kin ci gaba da neman gafarar ubangiji.

  6. Yi sallar safiyarka/ki, bayan kammalawa, cigaba da zama a wurin sallan kana/kina mai karanta Al’kurani maigirma da yin zikiri.

  7. Yi sallar Shuruk bayan minti 15 da fitowar rana sabo da ka/ki samu ladar yin Hajji da Umrah kamar yadda Manzon Allah (S.A.W) ya bayyana. Yi kokari kar wannan damar ta kubuce maka/maki!

  8. Bayan sallar Shuruk, za ka/ki iya yin bacci don samun kuzarin yin azumin da ke bakinka/ki

  9. Za ka/ki iya tashi ka/ki yi sallar Dhuha (walaha) akalla raka’a hudu sannan a ci gaba da yin zikiri da cewa: LA'ILLAHA ILLAL LAH WAHDAHU LA SHARIKA LAHU LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU WA HUWA ALA KULLI SHAI’IN KADIR.

  10. Yi sallar azahar, ka yi/ki yi kabbara sannan ka/ki karanta wani abu a cikin Al’kurani mai girma.

  11. Yi kokari ka/ki saurari hudubar Arafa a TV ko kuma a duk wata kafa da ta sauwaka

  12. Yi sallar la’asar sannan ka/ki cigaba da karatun Al’kurani da zikiri har magariba

  13. Lokacin da magariba ta doso kamar awa daya hakan nan, yi kokarin yin addu’oin neman gafara da albarkar Allah, sannan da duk wani alherin da ke cikin wannan duniya da lahira. Kar ka/ki mance da sauran ‘yan uwa musulmai wajen addu’arka/ki wadanda suke raye da matattu. Kar ka/ki manta da ranar da za ka/ki tsaya a gaban ubangijinka/ki. Ka/ki roki Allah Ya sa kana/kina daga cikin wadanda za a gafarta wa kafin wannan ranar ta fadi.

  14. Ana kiran sallar magariba ka/ki karya azuminka/ki,  ka/ki na mai yin adu’oi. Sai a yi sallar magariba, shi ke nan ranar Arafa ta kare!

  Da fatan Allan Ya karbi ayyukanmu na kwarai sannan Ya yi mana jagora, mukasance masu yin ayyuka kyawawa, kuma da fatan za mu kasance a cikin bayinSa da Yake alfahari da su, Allah Ya kare ni da ku daga shiga wuta sannan Ya sa mu cikin wadanda za a karbi ayyukansu a ranar da ba abin da zai yi amfani sai ayyukan kwarai. Sannan za a iya duba: Takaitattun bayanai kan hukunce-hukuncen zakkan fidda kai (zakat al fitr) da sauransu.

Comments

3 comments