Makalu

Sabbin Makalu

View All

CIKIN ƁAURE:Babi na sha-shida

 • Ta ɓangaren Abbas kuwa, tamkar farincikinsa ne gaɓaɗaya ya ba Asma'u a cikin takardar sakin, domin tunda suka baro gidan yake jin wani kalar tashin hankali a ransa, don ma ya yi ƙoƙari sosai ta yadda wani ba zai gane irin wutar da ke babbakar masa zuciya ba. 

   

  Bai iya gane shayi ruwa ne ba sai da ya koma gida da daddare, tun a rashin samun mai amsa sallamar da ya yi ya san Asma'u na da muhimmanci a gidan, don kuwa ta kan amsa mashi ko da ciki-ciki ne don ta sauke haƙƙin Musulunci. Wurin da take shimfiɗa tabarma a ƙofar ɗaki ya duba, wayam ɗin da ya ga wurin ne ya sanya shi girgiza kai, a fili ya ce "Zan yi kewar ki Asma'u", a hankali ya tura ƙofar ɗakin ya shiga, da taimakon fitilar wayarsa ya ƙarasa bedroom, tunga ya ja a bakin ƙofar yana ƙare ma ɗakin dake gyare kallo, ya san ba aikin Asma'u bane, amma duk da haka ya yi farinciki, saboda tsaftar jiki da ta muhalli tana yaye kaso mai yawa na baƙinciki, tsaftar zuciya kuwa, kawar da baƙincikin ma take da taimakon Allah. 

   

  Kallon gadon ya shiga yi, a ƙasan ransa kuma yana hasaso Asma'u kwance cikin kayanta na bacci. Lallai ko daa Asma'u zata dawo, ba abu ne mai sauƙi ya iya jure kewar rashin ganin ta a gidan ba, bare kuma gangancin sakin ta ba tare da shawara da kowa ba. 

   

  Jiki a mace ya dawo falo tare da zama jagwab! Kan kujera. 

   

  Kifa wayar ya yi a gefenshi, ta yadda haskenta zai game ɗakin, iska mai zafin gaske ya furzar, lokaci ɗaya kuma ya dafe kai da duka hannayensa, "An ya ban yi ganganci da na rabu da Asma'u ba?", tambayar da ya yi ma kansa kenan, don kuwa jikinsa ya yi la'asar hada magariba da isha'i. 

   

  Zuciya ce ta tunatar da shi rashin darajar da yake da ita wurin Asma'un, da irin kayan haushin da ta yi ta jibga mashi tun da ya aure ta, take kuwa ya tilasta ma kanshi basar da damuwar ta hanyar ɗaukar waya ya shiga Facebook, sai dai buƙatarsa bata biya ba, don ji ya yi kamar ƙuncin na daddale a facebook ɗin, ba arziki ya rufe data. 

   

   Zugar zuciyarshi ya sake bi, inda ta ruwaita mashi kiran Asma'u a waya, jikinsa na ɓari ya yi dialing numberta, ga kunne ya kara wayar tare da lumshe idanu, sai dai ba a ɗaga ba har ta tsinke, sake dialing number ya yi, da mamaki sai ya ga an ta datse kiran. 

   

  A wannan lokacin idan har yana da matsayi a zuciyar Asma'u, toh tabbas zata amsa kiranshi, domin dare ne lokacin da masoya suke samun damar ɗebe ma juna kewa a natse. Neman agajin Ubangiji ya yi ta hanyar faɗin "Allah ka dubi raunina, ka yaye mani damuwata."

   

  Miƙewa ya yi, domin ji yake falon ya masa kaɗan, rufe ƙofar falon ya yi, sannan ya koma bedroom ya kwanta, laluben gadon ya shiga yi, duk da ya san ba zai ji kowa ba, hannunsa na dira kan pillow ya jawo shi ya rungume, a hankali ya lumshe idanu, cikin zuciyarsa kuwa yana jin kamar wani ƙaton dutse ne aka ɗaura mashi. Addu'ar neman sassauci a wurin Allah ya shiga karantowa, da taimakon Allah kuwa sai ya ji kamar Asma'u ce a jikinshi ba pillow ba.

   

  A makamancin wannan lokacin ma, shiru ɗakin da Asma'u take kwance yake, baka jin sautin komai sai saukar numfashin su Nafeesa da ke can kan katifarsu ita da Saudat suna bacci, ɓangare ɗaya kuma sai tashin kukan sauron da ke ta yawo jefi-jefi, don kuwa ƙarfin mosquito coil ɗin da aka sa ɗakin ba zai iya kashe sauron ba. Ko kusa farincikin rabuwarta da Abbas bai bari ta lura da naƙasun da ta fara cikin karo da shi tun a ranar farko ba, domin kuwa a gidanta ta kan yi bacci a jikin mijinta, duk da ba wani matsayi ya ke da shi wurinta ba, amma yanzu ga ta kwance cikin ɗakin da ta manta da yanayinsa marar daɗi na tsawon shekara ɗaya, domin kan tsohuwar katifarta take kwance, wadda Nafisa ta gaje bayan Asma'un ta yi aure, yanzu kuwa tunda mai wuri ya zo, mai tabarma dole ya naɗe.

   

  Hannu ta kai saitin kunnenta ta kore sauron da ya ke mata ƙugi a kunne, gyara kwanciyarta ta yi a kan kafaɗarta, cike da son ta yi bacci da rumtse idanunta, sai dai baccin ya ƙi zuwa, ta kuma kasa gane rashin daɗin ɗakin ne ya hana ta bacci. Tuno Abbas ta yi, hakan ya bata damar yin mamakin yadda ya sake ta ba tare da ya wahalar da shari'a ba, "Toh ko ƙaryar so yake mani dama?", ta tambayi kanta, lokaci ɗaya kuma ta yi kwanciyar rigingine tana fuskantar sama. 

   

  Tuna yadda yake susuce mata ta yi, wanda kuma ya amsa mata tambayarta kan cewa dole ce kawai ta sa ya rabu da ita. 

   

  Wani sauron ne ya katse mata tunani a dalilin kukan da ya yi a kunnenta, bige shi ta yi kamar ɗazu, a ranta kuma ta ce "Yanzu na dawo cikin wannan yanayin marar daɗi kenan.?" 

   

  "Eh" ce amsar tambayarta, sai dai sanin sai an sha wuya kafin a sha daɗi ne ya sa ta watsi da duk wani tunani da zai sa ta yi nadamar rabuwa da Abbas. . 

   

  Haka wannan dare ya kasance marar daɗi ga Asma'u, saboda azababben sauro, da kuma wata kalar damuwa da ta rasa ta mece ce. Kamar yadda ya kasance mafi munin dare ga Abbas, don rutsum bai rumtsa ba, bare ya samu sassauci a ransa. 

   

   Washe gari kuwa ƙarfe takwas na safe can ta yi ma Abbas kamfaninsu blocks. Ba tare da ya zauna ba ya cigaba da aiki tuƙuru, lokaci ɗaya kuma bakinsa na ta ambaton Allah, domin kuwa shi kaɗai ne abin da zai sanya ma zuciyarshi nutsuwa. 

   

  Lokacin da Abdul ya zo kuwa har ya fara haɗa wasu blocks. Abdul na jin daɗin zafin naman Abbas, don bai da son jiki, shi ya sa suka yi kaso mai yawa na kwangilar blocks ɗin Nas, duk da ma'aikatan da suka ɗauka a kamfanin. "Katafila sarkin aiki" Abdul ya faɗa lokacin da ya ƙarasa inda Abbas ya ke, murmushin yaƙe Abbas ya yi, don shi kanshi ya san aikin da ya yi a ɗan lokacin da ya zo ba na lafiya bane, yana yi ne kawai dan neman sassauci a ransa. 

   

  Gaisawa suka yi, sannan suka koma kan wani benci suka zauna. 

   

  Abdul ya lura da Abbas na buƙatar fitar da abin da ke ransa na damuwar da ta fito masa a fili. 

   

  Ta hanyar zaulaya ya ɓullo ma Abbas ɗin, inda ya ce "Da gani safko ka bugo, koda yake gauro ne ai, madam ba ta nan", murmushi mai sauti Abbas ya yi tare da faɗin "Kai dai bari, ai...", sai kuma ya yi shiru. 

   

  Ɗan dubanshi Abdul ya yi "Hala gwaurancin ba daɗi?", Abbas ya ce "Ko kaɗan ma kuwa Abdul."

   

  Abdul ya ce "Ai lokacin da Hafsat ta tafi wanka ni ma na ɗanɗana kuɗata, dan ma ina zuwa gidansu, kuma ko da yaushe muna tare a waya", kamar Abbas zai yi kuka ya ce "Ai kai taka matar ta ɗebe kewa ce, ba zaka wani sha wahala ba dan bata nan."

   

  "Kai ma ta ka Insha Allahu zata gyaru."  

   

  "Wane gyaruwa kuma, bayan jiya da takardar sakinta ta koma gida", cike da jajircewa ya ƙarashe maganar, don zuciyarsa ta karye, kuka kawai yake son yi. 

   

  Fuskar Abdul ɗauke da wani irin mamaki ya dubi Abbas "Kamar ya da takardarta ta tafi gida?"

   

  Abbas ya ce "Na sake ta Abdul", Abdul ya ce "Da jinin haihuwar ka sake ta? Baccin kuma ba a sakin mace sai tana cikin tsarki.?"

   

  "Ya Salam! Wallahi takaicin ta ne ya rikitar da ni, idan ba sakinta na yi ba hankalina ba zai kwanta ba"

   

  Abdul ya ce "Toh yanzu hankalin ya kwanta ko?", Abbas ya ce "Ina fa, jiya rutsum ban rumtsa ba."

   

  Sosai ya ba Abdul tausayi, domin jarabawa a cikin soyayya ba kowa ke iya cinye ta ba, shi ya sa ake ganin wanda ya mutu a dalilin soyayya ya yi shahada. 

   

  Shi kuwa Abbas nadamar sakin ce ta bijoro mashi, dan kuwa gaugawa aikin shaiɗan ce, tunda ga shi ya yi saki ba yadda addini ya sharɗanta ba. Tambayar Abdul ya yi "Toh yanzu ya matsayin sakin yake?", Abdul ya ce "Ai ta saku, sai dai ba a yanayin da musulunci ya kindaya ba." 

   

  Neman gafarar Ubangiji Abbas ya shiga yi a zahiri da kuma baɗini, daga bisani kuma ya cigaba da fesa ma Abdul zafin da ke ransa, shi kuwa Abdul da ruwan lallashi ya kashe kaso mai yawa na wutar da ke ci a zukatansu, dan kuwa abinda ya samu hanci idanu ke taya shi jimami. 

   

  Abincin siyarwa aka kawo suka siya, daƙyal Abbas ya iya ci, dan bakinsa kamar na marar lafiya yake jinsa. 

   

  Maganar kuskuren saki cikin jini kuwa wani irin raɗaɗi ta sa ma Abbas, aiki kawai yake, amma zuciyarshi na wurin Asma'u yana saƙa yadda ma zai warware sakin. Suna gama aiki Da yamma liƙis ya tafi gidansu Asma'un, tana zaune a tsakar gida ta ji ƙarar mashin, sai dai bata ba ranta shi ne ba, sai da ta tsinkayi muryarsa a soro yana sallama, ras! Rabanta ya faɗi, don bata taɓa zaton zai zo a yau ba, abinda kuma ya ƙara firgita ta shi ne yadda su Aunty zasu ɗauki batun sakin, musamman idan suka ji ita ce ta hura wutar ya sake ta. 

   

  Cike da jarjircewa ta kori tsoron a ranta, inda can cikin zuciyarta ta ce "Kai koma me zasu ce, su ce, tunda ba su ke yi mani zaman auren ba."

   

   Aunty dake shirin fita kuwa ta lura da ɗimbin kewar da ke ɗawainiya da Abbas, don kuwa abin da babba ya hango, yaro ko ya hau dutsen dala ba zai iya hango shi ba, kuma ba ta ga laifinsa ba don ya zo wurin matarshi, hakan ma shi ne kulawa.  

   

  Gaisawa suka yi da Abbas ɗin, a cikin ran Aunty ta ce "Wallahi Asma'u ta yi dacen miji mai ƙaunarta, Ya Allah, itama Nafisa ka bata miji na gari mai son ta." 

   

  Abbas kuwa ƙaramar kujera ya jawo zai zauna, Aunty ce ta dakatar da shi da faɗin "A'a, ka shiga ɗaki mana, aikuwa ya ji daɗin wannan iso, "Toh" ya ce, lokaci ɗaya kuma idanunsa na kan Asma'u da ke ta ƙoƙarin haɗe fuska, Aunty na ficewa gidan Asma'u ta wurgo mashi tambayar "Me ya kawo ka yau kuma.?" 

   

  Abbas bai yi magana ba, sai dai ya bi bayanta suka shiga ɗakin a tare, gefen gado ta zauna, shi kuma ya zauna kan kujera suna fuskantar juna. Shiru na wucin gadi wurin ya yi, daga bisani bayan sun gaisa Abbas ya dube ta, lokacin da take duba waya, "Asma'u, ni kuwa ya jininki na haihuwa, yana nan?", da mamaki ta tambaye shi "Kamar ya?", idanunta cikin na shi ta ƙarshe maganar, cewa ya yi "Kawai so nake in ji", a tsiwace ta bashi amsa "Toh duka haihuwa kwana tara, ta ya jini zai ɗauke", ya ji daɗin wannan amsar kuwa, domin ya ƙara tabbatar wa ne ya ce "A taƙaice dai kina cikin jini", ta ce "Eh", bai ɓoye mata abinda ke ranshi ba ya ce "Toh na aikata kuskure, domin ba a saki a cikin jini", a zabur Asma'u ta dube shi, don tsaf zai iya ce mata ba saki. 

   

  Baki ta buɗe zata yi magana, amma sai ta ga ya dawo gefenta, sosai yanayinsa ya bata tsoro, domin toshe mata bakin tsiwa ya yi ta hanyar dafa kafaɗunta, cikin rawar murya ya ce "Asma'u, ko da a cikin tsarki na sake ki, toh na yi kuskure, domin zuciyata ba zata iya jurar rashinki ba, ki taimake ni mu yaga takardar nan don Allah, na maki alƙawarin duk abinda kike so zan maki."

   

  Abbas ya manta da a kyauta ake samun so, kuma a yanzu da Asma'u ke murnar samuwar ƴancinta ba zata yi gigin koma masa ba. 

   

  A sannu ta zare mashi hannu, bayan ta matsa gefe ne ta ce "Kada ka sake taɓani, tunda yanzu ni ba matarka ba ce, kuma da kake maganar saki a cikin jini duk inda ka je na saku, don haka kamar yadda na bar cikin uwata haka na barka", tana faɗin haka ta miƙe zata fita, ruƙo mata hannu ya yi "Asma'u ko yanzu idan na maida ki kin maidu, tunda saki ɗaya ne", aikuwa ta ce "Idan kuwa ka maida ni zan koma, amma Wallahi sai na kashe ka", ficewarta ta yi, ta bar shi da ƙuna a rai. 

   

  Daga can tsakar gidan ta cigaba da faɗin"Ni ban taɓa ganin jaraba irin taka ba, ana so dole ne da zaka hayyaci rayuwata?". 

   

  Bayanta ya biyo yana faɗin "Ba a so dole Asma'u, kuma in dai akwai zuciya a jikina na haƙura da ke."

   

   A kan kunnen Khadijah da ta shigo Abbas ya yi wannan magana, duk da Asma'u ta ga Khadijar, amma ta ce ma Abbas "Da na huta kuwa, jarababben banza da wofi". 

   

  Kallon Abbas da ke cikin kiɗima Khadijah ta yi, wani irin tausayinsa ne ya mamaye mata zuciya, har ta ji kamar ta yi kuka, maida dubanta ga Asma'u da ke ta huci ta yi, "Haba Asma'u, ko ba aure a tsakaninku ya fi ƙarfin wulaƙanci, bare kuma mijinki."

   

  "Wane aure kuma, bayan jiya da hannunsa ya bani takarda", sallallami Khadijah ta shiga yi, idanunta cike da ƙwallah ta dubi Abbas "Da gaske ka sake ta?", cikin raunin murya ya ce "Dole ta sa ni Khadijah, ina son Asma'u kamar raina, amma ta ce kashe ni zata yi idan ban rabu da ita ba", yana rufe baki kuka ya ƙwace mashi, a hankali Khadijah ta lumshe idanu, tare da matse ƙwallan tausayin Abbas. 

   

  "A gayas" ɗin da Asma'u ta ce ne ya sa ta buɗe idanu, lokacin kuma har Abbas ya fice daga gidan. 

   

  Cikin tsananin fushi Khadija ta ce ma Asma'u "Wallahi kin yi asarar miji, muddin kika bari Abbas ya kufce maki, har abada ba zaki samu kamarshi ba", har cikin ran Asma'u ta ji zafin maganar, a fusace itama ta ce "Ba bakinki ba, idan kuma kina ganin Abbas na gari ne, ki je ki aure shi ke dan Allah." 

   

  Girgiza kai kawai Khadijah ta yi, sannan ta juya, dan zamanta a gidan ba ƙaramin rikici zai haddasa ba. 

   

  A ƙofar gida ta samu Abbas tsaye, cike da lallashi ta ce mashi "Ka yi haƙuri, so da yawa mutum kan so abu, kuma ya zame masa sharri", ya ji daɗin maganarta, godiya ya yi mata, kana ya burka mashin ɗinshi ya tafi, da idanu Khadija ta raka shi har ɓace ma ganinta, ƙasan ranta kuma ta na ta yi mashi addu'ar samun sassauci a wurin Allah, dan kuwa itama so bai mata daɗi ba. 

   

  Abbas kuwa daƙyal ya kaiwa gidansu. Ƙannenshi na ganin yanayinsa suka yi tsit, Abeeda ce ta yi ƙarfin halin tambayarsa "Yaya Abbas lafiya?", maimakon ya bata amsa, sai ya ce "Ina Ummah? "

   

  Fitowar Ummansu a banɗaki ce ta amsa maahi tambayae da ya yi ma Abeeda. 

   

  Ɗakinta ya shiga, tana shigowa itama tun kafin ta zauna ta tambaye shi "Me ke faruwa ne.?"

   

  Yana kuka ya cigaba da zayyana mata abinda ke faruwa tsakaninsa da Asma'u.

   

   Sosa Ummansu ta kaɗu, amma don ta rage ma Abbas zafin dake ransa ta ce "Allah ya kyauta", shiru ɗakin ya yi, Ummansu kuwa sai dai ta fito tana fad'in "Wace irin masifa ce wannan?", Abida ta ce "Umma menene?

   

  "Ya saki Asma'u", ta bata amsa, sallallami Abida ta shiga yi, daga bisani ta ce "Wallahi ya huta, Umma wannan yarinyar ba matar arziki ba ce". 

   

  Shiru Ummansu ta yi, tana nazarin baƙaƙen halayen Asma'u, gani ta yi Abbas ya fito da ƙyal, hannu dafe da ƙirji ya zo daf da ita ya tsaya, "Umma Asma'u so take na mutu, Wallahi ina sonta, ba da gangan na sake ta ba, ko cikin da ya mutu bakinta ne ya kashe ɗan", wani irin tari ne ya sarƙe Abbas. 

   

  Kan kace me sai ga aman jini, hankalin Ummansu a tashe ta ce "Muddin ɗana ya mutu sai na yi shari'a da Asma'u", karon farko kenan da Ummansu ta fito da haushin Asma'u a waje. 

   

  Cikin hanzari aka samo motar mijin Zainab, ƴan unguwa kuwa sai cewa suke meke damun Abbas, shi da mata kowa ya kwanta asibiti. 

   

   

  Daga can gidan su Asma'u kuwa, Aunty na dawowa Asma'u ta miƙa mata takarda, cikin tashin hankali Aunty na karantawa ta ce "Wace irin masifa ce wannan.?"

   

  Da yake kowa nashi ya sani sai Aunty ta fara sababin Abbas ya wulaƙanta su. 

   

  Kiran number Ummansu Abbas ta yi, aikuwa ta ɗaga, gaisawa suka yi, Aunty ta ce "Toh Abbas ya faɗa maki ya saki Asma'u ko?", daga can Ummansu Abbas ta ce "Toh yanzu haka dai Abbas na ɗakin gaugawa, idan Allah ya sa ya fito, sai mu yi maganar sakin, idan kuma ya mutu sai Asma'u ta zuba ruwa ƙasa ta sha", tana faɗin haka ta tsinke kiran... 

   

  ©Hadiza Isyaku

  @HazaƙaWritersAssociation. 

Comments

1 comment