Recent Entries

 • A maganar matsalolin da suka shafi aure, yan Arewa muna da sauran tafiya mai nisa

  Jiya na iso wurin aiki da safe, sai na iske wani abokin aikina, dan kasar Saudiya, yana gyaggyara Shimag na shi zai shiga aji ya karantar. Shimag shine dan kyallen nan da larabawa ke yafawa a kansu. Cikin raha da zolaya, sai na ce masa, cikin Turanci, ‘getting set?’ ma’ana, ‘...
  comments
 • Muhimmancin koyon harshen Turanci (Na daya)

  Ko shakka babu muhimmancin yin abu akasari yana daidai na anfanarwa da zai yi wa mutum. Kusan ya zama dole koyon harshen Turanci a wannan karni, ba mu ce karnin baya ko mai zuwa ba, saboda muhimmancinsa a fannoni da dama. A wannan zamani, iya gwargwadon Turanci da ka ke ji, iya gwargwadon ci gaban a...
  comments
 • Takaitaccen tarihi da kuma dalilan da ya sa harshen Turanci ya buwayi sauran harsuna

  Turanci na daga cikin dangin harsuna da a ke ambato da ‘West Germanic. Sauran harsuna da ke cikin wannan dangi sun hada da Jamusanci da kuma yaren Dutch. Harshen Turanci ya zama daga cikin manyan harsuna da a ke anfani dasu a fannoni daban-daban na duniya. Kusan a na masa lakabi da harshen gam...
  comments
 • Abubuwa guda uku da ka iya janyo nasara a rayuwa

  Nasara aba ce da kowa ke bukatar ta. Don haka masu iya magana ke cewa, “babu baya haifar da akwai.” A bisa wannan dalili, matukar kana son cin nasara a koda yaushe, ya zama lallai ka yi aiki tukuru. To shin ko menene mutanen da ke samun nasara a rayuwarsu ke yi ya sa su dawwama a cikinta...
  comments
 • Almajiranci da illolinsa cikin al'umma

  Hakika almajiranci a halin yanzu na daga cikin abubuwan da suka kawo tabarbarewar al'umma, musamman a arewacin Najeriya. Duk da cewa abu ne da ya samo asali don nufin ilimi da ilmantarwa, amma saboda rashin tsari da kuma rashin kulawa na wasu iyaye da kuma hukumomi, al'amarin ya baci, kusan ya ...
  comments
 • Kiyaye wadannan abubuwa guda biyu zai taimaka gaya a rayuwa

  Nazari da kuma lura da rayuwar mutane daban-daban da suka samu nasara a cikin rayuwarsu ta duniya, sun nuna cewa sanya wa kai hadafi da dauwama bisa alkibla na cikin manyan abubuwa da ke taimakawa gaya wajen cimma burin rayuwar da adam. Ko me ake nufi da hadafi da dauwama bisa alkibla? Hadafi ...