Makalu

Sabbin Makalu

View All

Almajiranci da illolinsa cikin al'umma

 • Hakika almajiranci a halin yanzu na daga cikin abubuwan da suka kawo tabarbarewar al'umma, musamman a arewacin Najeriya. Duk da cewa abu ne da ya samo asali don nufin ilimi da ilmantarwa, amma saboda rashin tsari da kuma rashin kulawa na wasu iyaye da kuma hukumomi, al'amarin ya baci, kusan ya jefa yara da dama cikin hali kaka ni ka yi.

  Kadan da ga cikin illolin da almajirancin ke haifarwa sun hada da:

  1. koya wa yaro munanan dabi'u irin su shaye-shaye da taurarewar zuciya
  2. matsalolin rashin lafiya ga yaro
  3. rashin soyayya tsakanin yaro da iyayensa
  4. yaduwar musibu a cikin al'umma, da dai makamantansu

  Saboda haka ya zama wajibi ga iyaye da su kula kada garin nema lada a shiga bata. Babu mai kula da yaro kamar yadda iyayensa za su yi. Yana da kyau gwamnati ma ta sanya hannu, ta kafa doka da zai rage irin wannan gurbataccen al'ada cikin al'umma. Malaman addini na da babban gudumawa da za su bayar.

  Allah ya sa mu dace. Sannan za a iya dubaKiyaye wadannan abubuwa guda biyu zai taimaka gaya a rayuwa

Comments

2 comments