Makalu

Sabbin Makalu

View All

Abubuwa guda uku da ka iya janyo nasara a rayuwa

 • Nasara aba ce da kowa ke bukatar ta. Don haka masu iya magana ke cewa, “babu baya haifar da akwai.” A bisa wannan dalili, matukar kana son cin nasara a koda yaushe, ya zama lallai ka yi aiki tukuru. To shin ko menene mutanen da ke samun nasara a rayuwarsu ke yi ya sa su dawwama a cikinta? Abubuwan dake kawo cin nasara suna da yawa. A cikin wannan takaitacciyar makala na yi dubi ga guda uku kacal.

  Rashin wasa da lokaci

  Duk mutum mai kokarin cin nasara a rayuwarsa baya wasa da lokaci. Lokaci na da matukar muhimmanci a rayuwa. Abune da aka sani, idan lokaci ya wuce ba’a mai dashi. Masana harkokin kasuwanci na nuna cewa lokaci shine babban jari da za ka iya samu cikin kasuwancinka bayan kudi. Don haka, yana da matukar muhimmanci, a rika amfani da shi kan turban da ya dace. Yana da kyau mutum ya tsara lokutansa – abinda zai yin a kowane rana, na kowane wata da kowane shekara. Amfani da lokaci ke sa mutum ya sanya wa kansa kudurin abunda zai cimma a shekarun rayuwarsa.

  Masana na bada shawara mutum yake amfani da da yar takarda wacce ake kira to-do list a Turance wajen rubuta abubuwan da mutum ke bukatar yi na wuni ko kuwa wasu yan lokuta, kuma ya kasance a karshen wadanan lokutan, mutum ya zaura ya yi bitan abinda ya rubuta don tabbatar da wanda ya yi nasara akai da wanda abi yi ba. Hakan na taimakawa matuka wajen kiyaye lokaci da amfani da shi. Mai karatu na iya karanta wannan makala na Turanci don karin bayani game da to-do list.

  Fuskantar kalubale

  Rayuwa bai yiwuwa sai da daukar kalubale. Dole mutum ya fuskanci abinda ya fi bashi tsoro. "Matsoraci ba shi zama goni...," in ji Dr Mamman Shata. Saka zullumi da yawan tunanin me zai faru kan janyo rashin nasara a rayuwa. Don haka ma’abota cin nasara a koda yaushe basa kasa a gwiwa, basa karaya, amma suna daukan kaddara in ya same su, kuma sun fahimci cewa fadi-tashi shine ginshikin rayuwa.

  To amma fuskanta kalubale ba yana nufin fadawa rijiya bane, ko kuwa mutum ya zama baya tunani sai dai ya afka wa abu. Dole abinda duk mutum zai yi, yayi tunani akai, ya tabbatar da cewa abu ne da ya dace ya saka kanshi ciki, in kuma ya fahimci haka to babu sauran tsoro ko wasiwasi. Rashin tsoro kan kai mutum ga nasara in Allah Ya so.

  Rashin tsoron yin kuskure

  Masu iya mgana suna cewa 'kuskure alamu ne na cewa mutum na kokarin yin wani abu.' A duk lokacin da aka ce mutum ba ya kuskure, to bai taba yin wani abu sabo ba, la'alla ko don tsoron gwadawa ko kuma don makamancin hakan. A rayuwa dole mutum ya yi kuskure, kuma yin kuskure ne kawai ke sa mutum ya koyi wani abu sabo. Don haka kada mu ji tsoron kuskure. Mu yi tambaya akan abinda bamu sani ba, kuma mu sani sai fa an bata ake gyarawa matukar ba da gangan za'a bata ba.

  Daga karshe, duk mutumin da ya kiyaye wadannan abubuwa guda uku - rashin wasa da lokaci, da fuskantar kalubale, da kuma kudurar anniya cewa kuskure baza ta hana mutum sake gwadawa ba - in Allah ya so yana tare da nasara a dukkanin al’amuransa. Allah ya sa mu cimma burin rayuwarmu.

  Mai karatu na iya latsa link dake gaba don karanta makala makamancin wanna da yi bayani akan: abubuwa guda biyu da indan mutum ya kiyaye zai taimaka wa rayuwarsa.

Comments

1 comment