Makalu

Sabbin Makalu

View All

Takaitaccen tarihi da kuma dalilan da ya sa harshen Turanci ya buwayi sauran harsuna

 • Turanci na daga cikin dangin harsuna da a ke ambato da ‘West Germanic. Sauran harsuna da ke cikin wannan dangi sun hada da Jamusanci da kuma yaren Dutch. Harshen Turanci ya zama daga cikin manyan harsuna da a ke anfani dasu a fannoni daban-daban na duniya. Kusan a na masa lakabi da harshen gama gari ko kuwa harshen da ya fi kowane harshe fice a duniya.

  Kasashen Turai da dama suna da tasiri a kasar Ingila da ma harshen Ingilishi, halan ko dan sanadiyar yake-yake ne ko kuwa zamantakewa. Saboda haka harsuna da dama sun shiga cikin harshen Turanci, kamar su Jamusanci, Faransanci, harshen Romawa da na Girkawa, kama har da harshen Larabci da kadan daga cikin harsunan Africa kamar yadda ya zo a bayanan masana ilimin harsuna.

  Misalin tasirin Larabci a cikin Ingilishi sun hada da aron wasu kalmomi kamar su ‘emir,’ ‘sultanate,’ ‘algebra,’ ‘algorithm,’ ‘alcohol’ da dai sauran kalmomi da dama. Masana sun tabbatar da cewa Kalmar Zebra’, wato rakumin daji ya samo asali ne daga yaren Congo. Sauran kalmomi daga yarukan Afirka sun hada da: ‘safari’ wanda a ka samo shi daga Swahili, su kuwa Swahili sun aro shine daga Larabci. Akwai kalmomi da dama bayan wadannan. A takaice a na iyan fahimtar cewa harshen Ingilishi dai tamkar jakar magori yake, ba bu yaren da baya cikinsa, ko kuwa muce tamkar hankaka yake mai maida dan wani na shi.

  Za a iya karanta: Abubuwa guda uku da ka iya janyo nasara a rayuwa

  Duk da cewa ana amfani da Ingilishi a kasashe daban-daban na duniya, amma kasashen da suka zama sune kasashen da harshen ya zama na farko sun hada da Birtaniya, Amurka, Kanada, Ireland, Australia da New Zealand. A kasashen da suka yi fice wajen amfani da Turanci a Afirka sun hada da Najeriya, Ghana, Afirka ta Kudu, Kenya, Liberia da dai sauransu. Kasar India, Malaysia, Malta, Hong Kong da makamantansu na daga cikin kasashen da ke amfani da Ingilishi matuka gaya.

  Harshen Turanci ya kara samun fice a duniya a sanadiyar fice da kasar Amurka ta yi a fannin tattalin arziki. Kasancewar kowace kasa na so ta yi hulda da ita a fannin ilimi ne, kere-kere ne, takanoloji ne ko kuwa harkar tsaro, ya janyo wa harshen Turancin cigaba kwarai, kuma a kullum kara habaka ta ke yi a fannoni daban-daban.

  Saboda haka a na iya cewa tasiri da matsayin harshen Turanci ya buwayi ko’ina da kowani fanni na rayuwa, wadda ya sanya shi ya zama muhimmin yare cikin yarukan da suka yi fice a duniya. Kuma hakika koyonsa zai zama tamkar mabudin ci gabane ga dukkan mutumin da ke son ingantaccen rayuwa a wannan karni da muke ciki.

  Sannan dubiMuhimmancin koyon harshen turanci na daya 

Comments

1 comment