Makalu

Sabbin Makalu

View All

Muhimmancin koyon harshen Turanci (Na daya)

 • Ko shakka babu muhimmancin yin abu akasari yana daidai na anfanarwa da zai yi wa mutum. Kusan ya zama dole koyon harshen Turanci a wannan karni, ba mu ce karnin baya ko mai zuwa ba, saboda muhimmancinsa a fannoni da dama. A wannan zamani, iya gwargwadon Turanci da ka ke ji, iya gwargwadon ci gaban al’amuranka sawa’un harkokin ilimi ne ko kasuwanci ko nishadantarwa.

  Abu ba farko da za a iya tunawa a fagen ci gaba shine ilimi. Ilimi bai samuwa sai da malamai da kayan karatu. Kamar yadda a ke cewa ci gaban al’umma bai wuce sanin malamanta, haka kuma gwargwadon iya ilimin da a ka rubuta cikin wani harshe shine gwargwadon abinda masu anfani da wannan harshe za su sani. A nan mai karatu sai ya duba, kama daga ilimin addini, kimiyya, lissafi, falsafa, adabi, zamantakewa da dai sauransu, kwatankwacin litattafan ilimi nawa harshen da ya fi anfani dashi ke da su?

  Da Kalifa Al Mahmoon, shugaban daular Abassid na Bagdad ya yi shirin daukaka kasarsa, abinda ya fara dashi shine, ya umarci masana kuma ya musu alkawarin ladan kudi mai yawa duk wata guda, a wancan lokacin dirhamin zinari 500, kimanin dalar Amurka $24,000, ga dukka wanda ya maida muhimmin litafi na ilimi, musamman na kimiyya, daga wata harshe zuwa harshen kasarsa na Larabci. Daga karni 715 – 915, masana daga Bagdad sun yi ta tafiye-tafiye zuwa kasashen duniya dake da tarihin ci gaba a baya, irin su kasar Girka da Rom da Misra, suna zakulo litattafai suna fassarasu zuwa Larabci. A sanadiyar wannan, sai da daular Abassid ta buwayi duniya ta zamo daular da tafi kowace daula ci gaba a wancan karni. A na kiran wancan karni cikin Turanci da ‘Golden Age of Islam.’

  Karanta: Takaitaccen tarihi da kuma dalilan da ya sa harshen Turanci ya buwayi sauran harsuna

  A wannan karni muna iya cewa da wuya a samu wata harshen da zata yi tinkaho da littattafan ilimi na kowane fanni a duniya fiye da harshen Turanci, wanda suma tarihi ya nuna fassarasu suka yi daga wasu harsuna zuwa Turancin. Ta haka ne koyon Turanci ya zama tamkar dole matukar kana bukatar karatu a fannoni daban-daban na ci gaba na duniya. Sauran harsuna, musamman na kasashen Turai da Asiya, wanda ya hada da Larabci, suma suna kokari, amma da sauran tafiya, musamman dai harsunanmu na Afirka na da jan aiki gabansu.

  Wannan shine dalili na farko da ya sa koyon Turanci a wannan karni ya zama wajibi ga duk mai son ci gaba. Za mu ci gaba da bayanin dalili na biyu a Makala ta gaba. Allah ya sa mu dace.

Comments

1 comment