Makalu

Matsayin kunya a al’adar Bahaushe

 • Gabatarwa

  Tun gabannin cuɗanyar Hausawa da wasu, Bahaushe mutum ne mai kyawun tsari kan al’amurar da suka shafi rayuwarsa na yau da kullum. Mutum, ne mai kykkyawar riƙo ga al’adarsa ta gargajiya, musammam ga abubuwan da suka haɗa da addininsa, tufafinsa, muhallinsa, sana’o’insa, zamantakewarsa, tarbiyar sa da kuma umurni da hani, wanda ya haɗa da “kunya” a cikinsu. Ganin irin muhimmancin da Bahaushiyar al’ada ke da shi wurin Hausawa ne, ya sa za a dubi yadda al’adar kunya ta kasance jiya da kuma yadda ta sauya a yau, sakamakon cuɗanya da wasu baƙin al’adu. Karanta: Illar rashin kunya ga al’umma

  Ma’anar kunya

  Wannan kalma ce da ke da mabambantar fassara daga mahangar masana al’adu. Kowane masanin da yadda ya dube ta, kuma ya ba ta ma’ana mafi dacewa da ita da haka ne:-

  Bunza, (2006:250) ya ce, “Kunya wata Magana ko wani aiki da ya saɓa wa tsarin kamun kai na al’ada, kuma al’ada ta zarge shi da muni na zubar da girma da mutunci. Da mai furta maganar ko aikata aikin da mai sauraronsa, ko mai kallonsa, duk suna shiga cikin hurumin wannan, jawabi a al’adance. Girma da mutunci mutun yakan zube idan Bahaushe ya fahinci bai nisantar ɗaya daga cikin abubuwa da zai haddasa ire-iren waɗannan abubuwan. Duk wani nauyin da al’ada za ta haddasa, ko wani kawaicin aikata wani aiki, ko faɗar wata magana a wani wuri, ko a wasu wurare, ko a tsarin rukunin wasu jama’a na musamman duk ana sa shi aikin wannan ma’anar”

  Rabe-raben kunya

  Idan muka kula da ma’anar kunya da muka bayar, daga cikin ma’anar akwai abubuwan tsinta da za su iya zama rabe-raben kunya a idon Bahaushe. Bisa ga tsarin ma’anar kunya, Bunza (2006:261) ya ƙasa kunya zuwa gida kamar haka:

  1. Kunyar magana
  2. Kunyar aiki

  Kunyar magana:

  Hausawa na cewa, wata magana surkuwar baki ce. Abin nufi a nan, ba kowace magana ake furtawa ba. Akwai maganar da mai faɗa da mai sauraro duk kowanensu zai ji kunya. Akwai wadda mai faɗa kawai zai ji kunya ba mai sauraro ba. Akwai wadda mai sauraro ne kawai zai ji kunya ba mai faɗa ba. Misali. 

  Maganar da miji zai yi da matarsa ta zamantakewa da more zaman aure idan ɗansu mai wayo ya ji su duka za su ji kunya. Faɗa da tsawar da miji zai yi wa mata na horo da hani, idan ɗansa ya ji yaron zai ji kunya ba uban ba. Idan mace na wasa da ɗanta na fari idan wani ya girshe ta, ita za ta ji kunya ba wanda aka yi aikin gabansa ba. Maganganun da ke fita a baki a ji kunya suna da yawa. Daga cikinsu akwai, batsa da zagi na fitan albarka da makamantansu. Dubi: Matsayin kunya a rayuwar Bahaushe a yau

  Kunyar aiki:

  Wasu ayyuka akan yi su gaban wasu mutane ba a ji kunya ba, amma idan aka yi su gaban wasu a ji kunya. Daga cikin ayyukan da ke haddasa kunya akwai:

  1. Iyaye su riski yaro na wasa da matarsa, ko yaro ya riski iyayensa na wasan miji da mata. A nan kowanensu zai ji kunya.
  2. Suruki ya riski surukinsa na wasa da matarsa, a nan kowanensu zai ji kunya.
  • Babba ya riski yaro na kwaikwayonsa kan wani abin ban dariya da ya yi. A nan yaron zai j i kunya.

  A idon Bahaushe waɗannan su ne kashe-kashen kunya kuma kowanensu akwai abubuwan da ya kamata a lura da su kamar haka:

  1. Kunya da ake samu ta fuskar magana ba mai maganar kawai zai ji kunya ba. Kunyar in dai babba ce, to za ta mamaye bigere da dama, domin zata game abubuwa kamar haka:
  • Wanda ya furta maganar
  • Wanda ya ji maganar ana yin ta.
  • Wanda ya ji labarin maganar
  • Wanda ya kai labarin maganar
  • Wadanda suka shaida maganar
  1. Ta fuskar aikata aikin kunya kuwa, ba wanda ya aikata aikin kawai zai ji kunya ba. A wajen Bahaushe waɗanda kunyar za ta shafa sun hada da:
  • Wanda ya aikata aiki.
  • Wanda ya ga ana aikata shi.

  Matsayin kunya a al’adar Bahaushe

  Kunya al’ada ce da Bahaushe kan ɗauka da babban muhimmanci. Don haka kunya na cikin muhimman al’amura da suka shafi rayuwar Bahaushe ta kowane ɓangare. Bahaushe kan ƙarfafa jin kunya da kuma guje wa abubuwa na jawo kunya cikin Addininsa, al’adarsa, adabi da sauransu harkokin rayuwarsa na yau da kullum. Bahaushe na da tasirin kunya cikin addininsa tun yana bamaguje kawo zuwa ga komawar sa Musulunci. Maguzanci addinine na Bahaushe (Bamaguje) da ya haɗa da bautar iskoki da wasu abubuwa da suka shafi tsafe-tsafe, koma bayan bautar Allah Maɗaukakin Sarki da kuma bin tafarki Manzannin Allah duk da cewa Bahaushe da ya karɓi Addinin Musulunci, addini ya yi tankaɗe da rairaya da wasu al’adunsa ya zubar, amma al’adar kunya na tare da shi har yanzu.

  Har ilayau wasu ta’adodin al’adu da Addinin Musulunci ya ɗauke su munana kuma abin ƙyama, al’adar Bahaushe ya ƙyamace wanda ya aikata abin kunya na daga ciki. Misali: aikata zina na ɗaya daga cikin abubuwan hani ga Musulunci to haka zalika a maguzanci kamar yadda Sudan (2015) ya ruwaito mana cikin bincikensa ga al’adun aure da haihuwan maguzawa. Al’adar maguzawan Gidan Bakwai (ƙasar Faskari), idan za a kai amarya, dangin amarya sukan yi sihirce-sihircensu na kiran tsafi da suke bautawa. Sun nuna cewa, idan dangin amarya ‘yan magiro ne sukan kira shi ya yi wa amarya rakiya. Za a riƙa jin ƙuginsa a lokacin da ake tafiya kai amarya. Idan aka ƙira shi ya ƙi zuwa, wannan ya nuna amarya ba ta kai ɗiyancinta ba. Rashin kai ɗiyanci kuwa abin kunya ne, a cikin al’umma. Ya ishi uwa da ‘ya abin gori idan ana Magana. Da zarar haka ta faru, za a ga ba su shiga jama’a ana hira, gudun kar su samu saɓani, da wasu su yi musu gori. (Sudan, 2015).

  Mai karatu dubi makala ta biyu don ganin waɗanda kunya ta fi shafa cikin al’umma.

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Hanyoyi guda biyar na rage ƙiba ba tare da an shiga hatsari ba

  Posted Jun 12

  A duniyarmu ta yau, ƙiba na daya daga cikin matsalolin da ke addabar mutane da dama. Saboda irin ci gaba da aka samu na yawaitar abinci kala-kala – abincin gargajiya da na zamani, na gwangwani da na gona – ya sa da yawa mutane na yawaita cin abincin da zai k...

 • Sharudda da kuma ladubbar sallar idi karama

  Posted Jun 3

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da iyalansa da Sahabbansa baki daya. Idi shine duk abinda yake dawowa yana maimaituwa lokaci zuwa lokaci, kamar sati-sati, ko wata-wata, ko shekara-shekara. Shar'anta s...

 • Hukunce-hukuncen zakkar fidda kai

  Posted May 31

  Ma'anar zakkar fidda kai: Sadaka ce wacce ake bayar da ita sakamakon kammala azumin watan Ramadan. An shar'anta zakkar ne a shekara ta biyu bayan hijirar Annabi sallallahu alaihi wa sallam daga Makkah zuwa Madinah, a shekarar da aka wajabta azumin watan Ramadan. Huku...

 • Yadda ake hada local jollof rice

  Posted May 30

  Assalamu alaikum barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. Barka da shan ruwa. Yau zamu koyi yadda ake hada local jollof rice wato dafa dukan shinkafa ke nan da Hausa. Abubuwan hadawa Shinkafa Tattasai da tarugu Daddawa Albasa Seasoning Manja Ta...

 • Yadda ake hada bitter leaf soup

  Posted May 30

  Assalamu alaikum, barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya na yau. Barka da shan ruwa. A yau zamu duba yadda za ki hada bitter leaf soup (miyan shuwaka). Abubuwan hadawa Manja Nama Seasoning Garlic  Ginger Shuwaka (bitter leaf) Tattasai Ta...

View All