Makalu

Matsayin kunya a rayuwar Bahaushe a yau

 • Idan mai karatu na biye da mu a makalunmu na baya mun yi magana ne akan matsayin kunya a al'adar Bahaushe sannan daga bisani kuma muka gangaro muka duba asalin wadanda shi wanna al'adar tafi shafa a cikin al'umma. Yadda kunya ta kasance a rayuwar Bahaushe jiya, ba haka ta ci gaba da kasancewa a yau ba, domin kuwa ta samu ‘yan sauye-sauye, sakamakon mu’amalar wasu da wasu baƙin ƙabilu da suka shigo ƙasar Hausa, suka mamaye. Manyan al’umma da suka fi tasiri a kan rayuwar Bahaushe su ne Larabawa da Turawa.

  Larabawa

  Larabawa da suka shigo ƙasar Hausa, sun kawo Addinin Musulunci, wanda ya fidda rayuwar Bahaushe daga duhun kai na Addinin Maguzanci zuwa haske na Addinin Musulunci. Don haka aƙidun Balarabiyar al’ada wacce ta dogara kacokan kan koyar alƙur’ani da sunnah ta yi tasiri a rayuwar Bahaushe. Akwai al’adun Bahaushe da aka watsar saboda sun saɓa wa ƙa’ida, akwai kuma waɗanda aka cigaba da runguma sabo da sun dace da ƙa’ida. Cikin waɗanda aka cigaba da rungumar “kunya” na ciki. Dalili kuwa yana cikin koyarwar Alƙur’ani da Hadisi kamar yadda ayoyi suka tabbatar da hakan a baya. Don haka mu’amalar Bahaushe da Balarabe kyawawan sauyi aka samu cikin rayuwar Hausa.

  Kunya a Addinin Musulunci

  Addinin Musulunci shi ne addinin Bahaushe ya karɓa bayan fita daga duhun kai (Maguzanci) Musulunci ya yi tasiri sosai kan rayuwar Bahaushe wajen jaddada nasa bin umurni da hani na Allah (SWT) da kuma bin tafarki Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, (SAW). Kunya abu ne mai Muhimmanci da matsayi a Musulunci. Wannan ya tabbata ne cikin wasu ayoyin ƙur’ani da Hadisan Annabi Muhammad (SAW) kamar haka:

              Allah maɗaukakin sarki ya ce

  “Lalle wannan yana cutar da Annabi, to yana jin kunyarku alhali kuwa Allah ba ya jin kunya da gaskiya…” (ƙur’ani 33:53) (Fassara Gumi)

  Haka kuma cikin alƙur’ani mai girma, an kawo ƙissar Annabi Musa, wajen da taimaka wa ‘ya’yan Annabi Shu’aibu shayar da dabbobinsu. Saboda wannan taimakawar ne mahaifinsu ya umurce su, da su ƙirawo ya zo, zuwa gare shi. Allah (SWT) ya ce

  “Sai ɗayansu ta je masa tana tafiya a kan jin kunya, ta ce “Ubana yana kiran ka, domin ya saka maka ijarar abin da ka shayar, saboda mu” ......... (ƙur’ani 28:25) (Fassarar Gumi)

  Waɗannan duk ayoyi ne da ke jaddada “kunya” cikin Alƙur’ani Mai Girma. Hakazalika Hadisan Manzon Allah ma, sun jaddada muhimmanci da matsayin ‘kunya’ a Addinin Musulunci kamar yadda cikin hadisi an ce:

  “Daga Abu Sa’idul Khudri, Allah ya ƙara masa yarda yace “Manzon Allah (SAW) ya fi kowa jin kunya, mukan gane abin da ba ya so ne ta fuskar sa”.

                                                                                                              (Muslim ya ruwaito)

  Haku kuma wani ruwaya ta Bukhari an ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce

  “kunya daga cikin imani ne shi kuma imani daga cikin aljannace” (Bukhari ne ya Ruwaito)  

  A wata ruwaya kuma an ce

  “Manzon Allah (SAW) ya ce “kunya da imani an haɗa su wuri guda idan aka ɗauke ɗayan to shi ma ɗayan zai tafi”

  (Muslim ne ya ruwaito)

  An kuma ƙara faɗin Manzon Allah (SAW) yana cewa

  “lallai kunya da imani aƙida ne na Musulmi”

  (Minhajul Muslim)

  Dukkanin waɗannan ayoyin Alƙur’ani da Haidisai jaddada matsayi da Muhimmancin kunya ne suke yi cikin Addinin Musulunci.

  Turawa

  Kamar yadda zuwan Balarabe ƙasar Hausa ya kawo tasiri ga rayuwar Bahaushe, haka zuwan turawa. Duk da cewa zuwan Bature ya kawo tasiri ga rayuwar Bahaushe ta samar da wasu kayayyakin more rayuwa da, da can baya bai san su ba, amma kuma sun kawo tarnaƙi ga wasu al’adun Hausawa, waɗanda daga cikin su akwai “Kunya”.

  Zuwan Turawa ƙasar Hausa, ya sa Bahaushe na ɗaukar wasu al’adunsa, a matsayin rashin wayewar kai musamman masu ilimin boko. Don haka za a taras ɗaiɗaiku ne daga cikin mata a yau ke iya kinayar sunayen mazajensu. Hakazalika ɓoye sunan ɗan farko ma ana ɗaukarsa rashin wayewa don haka yawancin mata na ƙiran ‘ya’yan fari da sunayensu. Haka kuma ‘yan matan zamani kan furta wasu kalamai da be kamata ba musamman a cikin fina-finai amma kunya ba ta kama su. Raye-raye tsakanin maza da mata duk abubuwa ne na kunya amma a yau ya zama ruwan dare a al’umma. Don haka al’ada da addini ba su amince da rashin kunya, kuma duk mara kunya ana ɗaukarsa ne a matsayin mutumin banza. Kuma duk abin da ya yi ba zai zamo abin mamaki ba. A faɗin wani hadisi Manzon Allah Tsira da amince Allah su tabbata a gare shi na cewa

  “Yana daga cikin abin da mutane suka riska daga kalaman Annabawan farko, idan ba ka da kunya, ka yi abin da ka ga dama”

  Mai karatu na iya duba ci gaban wannan tattaunawa akan al'adar kunya a makala ta gaba, inda za mu yi dubi ga illar rashi kunya a wajen al'umma

Comments

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Wai shin mene ne data da kamfanonin layukan waya ke sayar mana?

  Posted Oct 13

  Kamar wata biyu da su ka wuce, Mallam Rabiu Biyora ya yi tambaya akan DATA da mu ke saye daga kamfunan waya inda ya ke cewa "DATA da kamfanonin layukan waya ke siyar mana, har muke amfani da ita wajen hawa Internet, su kamfanonin siyowa suke daga kasuwar siyar...

 • Egg and vegetable pocket

  Posted Oct 9

  A yau makalarmu ta girke-grken zamani zat yi bayani ne akan yadda ake hada wani abincin zamani mai suna egg and vegetable pocket. Ga yadda ake yin sa kamar haka: Abubuwan hadawa Filawa kofi biyu (flour 2cups) Baking powder 1½tsp (karamin cokali) Butter coka...

 • Rayuwar zamani: Babi na biyu

  Posted Oct 6

  Dedicated to Autan Hikima. Raihan na komawa office ya aiki masinga akan yaje yace ma head din ko wani department yana son ganinsa aconference hall, babu 6ata lokaci duk yabi ya fadamusu kafin ya koma ya sanar da zuwansu. Yana zaune a office kafin ya fara komai yaga ho...

 • Yadda ake hada sausages sultan chips

  Posted Oct 6

  Assalamu alaikum, barka da sake saduwa a cikin shirinmu na Bakandamiya. A yau Insha Allahu zamu yi bayanin yadda za ki hada sausages sultan chips. Abubuwan hadawa Dankali (irish) Sausages Carrots Albasa Tattasai da tarugu Man gyada Green peas Green pepper M...

 • Rayuwar zamani: Babi na daya

  Posted Oct 4

  Sulaiman bai yi mamakin ganinta ahakan ba domin hakan dabiar tace. taku take cikin isa da gadara irinta 'ya'yan masu kud'i y'a'yan masu hannu da shuni, Muhievert kenan yarinya fara doguwa kyakyawa, gata da k'ira mai kyau tsaruwarta ya zarce duk inda mutun ke tunani. Aka...

View All