Makalu

Tasirin camfe-camfen Hausawa cikin tarbiyyarsu (Na daya)

 • Gabatarwa

  Duk da kasancewar camfi mummunar al’ada ce amma suna tattare da wasu hikimomi da za a iya ƙaruwa da su, ko da yake ba za su halatta amincewa da camfi ba. Idan aka dubi camfe-camfen Hausawa za a iya kutsa kai a laluɓo wasu isharori da suka yi na kyautata rayuwa da suka danganci tarbiya, da koyar ɗa ɗabi’u, da bunƙasa tunani, da faɗakarwa, da tunatarwa, da tsoratarwa, da nuni kan dogaro da kai. Sannan kuma camfi kan hana mutane aikata abubuwan ƙi da neman a guje musu. Wato ke nan a wata fuskar camfi dai wani ƙuduri ne na tarbiya, da horo, da hani, da kuma bunƙasa tunani, da faɗakarwa. Cikin wannan makala zan yi dubi ga kadan daga cikin ire-iren tasirin da camfi ya yi cikin tarbiyar Hausawa. Dubi rushe tarbiya ta duniyar yanar gizo

  Ma’anar Camfi

  Akwai ƙirdado da yawa dangane da ma’anar wannan kalma ta “camfi”, wannan ma shi ne ya sanya, na ɗora hannuna kan waɗannan ra’ayoyi na masana.

  Bunza (2006:58). Cewa ya yi "Camfi wata daɗaɗɗiyar al’ada ce da Hausawa suka tarar tun kaka da kakanni. Kuma masana da manazarta Hausa sukan yi wa camfi kallo ta fuskoki biyu, wasu na kallon camfi, al’ada ce kawai kamar irin kowace al’ada; a ganin wasu kuwa, abin ya wuce haka, ya kai matsayin addini daga cikin addinin gargajiyar Bahaushe”.

  El-shamy (1976) ya ce “Camfi yarda ne ko amincewa, ko yin imani da wani abu a matsayin an gaskata shi tare da abubuwan da ya ƙunsa”.

  Scott (1976) shi kuma cewa ya yi “Camfi shi ne, yarda ko amincewa da wani abu, ko aiwatar da wani abu, da aka gada, kaka da kakanni cikin duhun jahilci, saboda tsoro, ko nuna fargaba da abin da ba a amince da shi ba”.

  Ɗangambo (1984:38) ya ce “camfi shi ne mutum ya ɗauka cewa, in ya yi wani abu, ko ya ce wani abu, ko ya ji wani abu, to ya gaskanta wani abu zai faru, sakamakon haka”.

  Ma’anar Tarbiyya

  Yahya da wasu (1992:68). Tarbiyya wata hanya ce ta kyautata rayuwar ɗan-Adam da shiryar da shi ya zuwa ga halaye da ɗabi’u masu kyau, masu nagarta. Idan ɗan-Adam zai tashi da kima da mutunci da ƙwarjini da ganin kimar abokan zamansa, sannan zai dinga bai wa kowa hakkinsa daidai yadda ya kamata gwargwadon iyawa da hali, to za'a iya cewa yana da tarbiyya. Tarbiyya ta haɗa renon jikin mutum da ransa da abubuwa kyawawa masu sa kamala. Dubi illar kai yara aikatau don neman kudi

  Kamusun Hausa (2006:428) ya anbaci tarbiyya da cewa reno ne da ake yi wa yara domin tashi da halaye nagari su kuma kyamace munanan ɗabi’u.

  Funtuwa (1983:63) ya bayyana tarbiyya da cewa “Horo ne da iyaye ko manya nagaba ke yi wa yara don su tashi da halayen kirki. Duk yaron da ya tashi babu tarbiya, rayuwarsa na iya zama mai rauni ce, kuma ana koyon tarbiyya ne ta hanyoyi kamar faɗa da kwaɓa da hani da umarni da kwaɗaitarwa da duka sannan da sanya yara a makaranta don samun ilimi da halaye nagari”.

  Misalan camfi masu nuna tarbiyya

  Misalan da za su zo kadan ne daga cikin tasirin da camfi ya yi a tarbiyar Bahaushe.

  Camfi masu Hani/gargaɗi

  1. Idan aka doki maciji da karan rama, za a ga kafafunsa, amma za a mutu.
  2. Idan yaro na cin ƙwai zai yi sata.
  3. Cin kan kifi na sa dushewar basira.
  3. Idan mace mai ciki ta tsallake rafi to za ta yi ɓari.
  4. Ƙetarar wando na sa mata yawan mafarki
  5. Kallon majigi ga mai ciki, kan sa a haifi yaro mahaukaci.
  6. Yin shara da dare na kawo tsiya (talauci)
  7. Idan mace mai ciki ta ɗebi ruwa a rafi da daddare aljanu za su musanya ɗanta da nasu. Da sauransu.

  Idan aka dubi waɗannan misalan za a ga cewa camfin ya nuna tarbiya ga mata ko mutane inda yake hani ga barin wasu abubuwa da sauransu.

  A makala ta gaba za mu kawo misalan tasirin camfi cikin rigafi da kiwon lafiya, da nuni ga addini da sauransu. Sannan mai karatu na iya duba yadda wakokin yara ke gina tunanin rayuwar al'ummar Hausawa

Comments

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Maɗigo da yawaitarsa cikin al’umma: Ina mafita?

  Posted Tue at 10:07 AM

  Tasowarmu muna kanana cikin alumma mun ga iyayenmu da sauran magabata suna da aure. Kowa da mahaifinsa da mahaifiyarsa. Hakanan kuma yayin da muke rayuwa mun ga ‘yan mata da samari daban-daban sun taso kuma mun ga sun yi aure. Kuma sannan sa’i da lokaci mutu...

 • Yawaitar binciken wayar miji: Dacewa ko rashin dacewa?

  Posted Jul 31

  A wannan zamani matsalolin da suke cikin aure musamman anan Arewacin Najeriya abin ba a cewa komai idan muka lura da ire-iren labarai da suke yawo yau da kullum a kafofin sada zumunta, wato social media. Duk lokacin da ka shiga social media idan yau baka ga labarin wata...

 • Takaitaccen bayani game da gravitational field

  Posted Jul 27

  A physics, gravitational field model ne da ake amfani da shi wajan bayanin tasirin da massive body ya ke da shi wajan zuwa sararin samaniya around itself producing a force on another body. Gravitational force of attraction da ke tsakanin body guda biyu ana governing din...

 • Sakamakon bincike game da matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a Najeriya

  Posted Jul 24

  Matsalar shaye-shayen miyagun gwayoyi matsala ce da kusan kowa da kowa na iya tabbarwa akwai shi a cikin al’umma musamman mu a Najeriya. Idan wani baya sha a gidanku, ko cikin danginku to kuwa lallai ba za a rasa masu yi ba a unguwarku ba. To amma duk da haka a ku...

 • Matsalar shaye-shaye a tsakanin matasanmu a yau

  Posted Jul 6

  A wannan Makala za muyi dubi ne zuw ga wani maudu’i mai muhimmanincin gaske. Za mu duba matsalar shaye-shaye da ya zama tamkar ruwan dare gama duniya a tsakanin matasanmu maza har da mata a wannan zamani. Duk da cewa wannan mummunar dabi’a ba dabi’a n...

View All