Makalu

Adabin gargajiya: Ire-iren wakokin baka na Hausa

 • Gusau, (1983) ya ce “Wakokin baka na Hausa sun shiga ko’ina a dukkan bangarorin rayuwar Bahaushe. Wakar baka takan yi ruwa ta yi tsaki a duk inda ta ga Bahaushe ya jefa kafarsa. Kasancewar wakokin baka suna da wannan halayya ta ratsa kowane zango na rayuwar Hausawa ya sa suka zama suna tafiya daidai da rayuwar yara kanana  da matasa da kuma manyan mutane, maza ko mata. Za a iya karkasa wakokin baka na Hausa zuwa gida-gida kamar haka:

  Wakokin baka na yara

  Wannan nau’i na wakoki ya kunshi sassan wake-wake da yawa wadanda yara ‘yan maza da ‘yan mata suke gudanarwa da suka hada da wakokin wasannin dandali da wasannin tashe da wasan kwaikwayo da bikin aure da sallar takuutaha da rokon ruwa da sauransu. Ga wasu misalansu:

  Wakokin yara maz

  Wakokin yara maza su ne wadanda suke shiryawa a lokacin da suke wasansu na dandali. Irin wadannan wakoki akan sami jagora mai bayarwa, sauran yara kuwa suna karbawa, kamar a wakar sha burburwa:

  Bayarwa:       Shaburburwa,

  Amshi:           Sha.

  Bayarwa:       Kowa ya bace,

  Amshi:           Sha.

  Bayarwa:       A sha shi da kulki,

  Amshi:           Sha.

  Bayarwa:       Kulkin kira,

  Amshi:           Sha.

  Bayarwa:       Ba na aro ba,

  Amshi:           Sha.

  Bayarwa:       Ku ba shi gidanai,

  Amshi:           Sha.

  Bayarwa:       Har ya kawo,

  Amshi:           Sha.

  Wakokin ‘yan mata 

  Wakokin ‘yan mata su ma nau’i-nau’i ne kuma su ne ake kira wakokin gada ko na bojo. Su ma ‘yan mata suna gudanar da wasanninsu ne a dandali ko a wasu wurare na musamman kamar a wajen bikin aure ko bikin sallar takutaha ko lokacin rokon ruwa ko tashe a watan azumi da sauransu. Misalan wadannan wakoki akwai kamar haka:

  Wakar Talle:

  Bayarwa:                                                      Amshi:          

  Maina ya kone,                                             talle

  Ba da talle ba,                                               talle

  Jirkita mani,                                                  talle

  In ciwo kashi.                                                talle                      

  Wakar Sabara:

  Bayarwa:                                                  Amshi:

  Na tai tsarince,                                         Sabara

  Magarya tai mani jar tsikara,                      Sabara

  lye, lye, lye                                               Sabara

  Magarya ba haka nan akan yi ba,                sabara

  lye, iye, iye,                                              Sabara                       

  ‘Yar bakin gulbi,                                         Sabara

  Ta yi liya-liya,                                            Sabara

  Ku yayyafa mata ruwa,                               Sabara

  Shaf, shaf, shaf,                                         Sabara

  Ka dauko naka ka tura daka,                       Sabara

  Ka dauko dan wani kai ta damfara               Sabara

  Wakokin baka na manyan mata

  Wakokin baka na manyan mata su ne wakokin da yawanci mata suke yin su a lokacin da suke aiwatar da wasu ayyukan gida. Manyan mata suna yin wakoki a lokacin daka ko raino ko dabe ko nika ko wanke-wanke da sauran lokuta na gudanar da wasu hidimominsu na yau da Kullum.

  Wakokin daka 

  Wakokin daka su ne wakoki wadanda mata suke yi lokacin da suke daka inda za su dinga gwama tabarya da turmi, sai su ba da sautin da ake kira lugude ko mama. Misaim wakar daka ita ce:

  Ana lugude ana mama,

  Cikin shigifa cikin soro,

  Mama ba habaici ce ba,

  Salon daka a haka nan,

  Ga macen da ba a so ta haihu,

  Ta haifi kwandamin da namiji,

  Shugaban daka shi ka daka,

  ‘Yan tanyo kissa su kai,

  Sukus-sukus sai su aje,

  Gidan Marafa kaji ka daka,

  Tarmani na izon wuta,

  Angula na kirba dawo.

  Wakokin reno

  Wakokin reno su ne wadanda mata suke yi a lokacin da suke rainon yara suna yi musu tawai don su yi shiru su bar kuka a kwantar da hankalinsu a sanyaya musu rai. A cikin wakokin akan fadi nasabar yaro da ayyukan da ake yi a gidansu da yabon masoya da zambo da habaci ga magabta in akwai su. Ga misali:

  Yi shiru bar kuka,

  Ku taho ku gane shi,

  Ku yo ziyara,

  Dan yaro sai dai a bi ka.

  Wakokin dabe

  Wakokin dabe su ne wakokin da manyan mata suke yi a lokacin da suke aikin dabe Yawanci wakokin dabe sukan kunshi bege da zambo da habaice-habaice da kalmomin batsa da na zage-zage da sauransu. Ga misali:

  Ina Lumu shege,

  Mai malmala ga munta,

  Kare bakin bahwade,

  Ya hana mu walawa.

  Wakokin nika

  Wakokin nika su ne wakoki wadanda mata suke yi lokacin da suke nikan tsaba a kan dutsen nika na gargajiya. Wakokin sun kunshi begen miji ko wani masoyi ko habaici ga kishiyoyi ko uwar miji ko ta hanyar shagube ko ambaton juyayin nakuda da dai sauransu. Ga misali daga wakar nakuda:

  Wayyo nakuda ta tashi,

  Ciwon nakuda ya tashi,

  Kuma ciwon nakuda ya motsa,

  Yau kam babu zama zaure,

  Wayyo inna ki cece ni,

  Da kis sha dadinka,

  Shin wai ke tuna inna ta cece ki?

  Ko ko Ke tuna da baba ya cece ki?

  Wayyo nakuda ‘yar ziza,

  Ciwon nakuda hon ne,

  Ko ko nakuda hauka cc?

  Wakokin talla

  Wakokin talla su ne wakoki wadanda ake yin su a lokacin da ake tallan wani abu. A cikinsu akan zuga sana’ar da ake tallar tare da fito da kwarjiinta ko amfaninta. Misali:

  Ku sai dawon geroda barkono,

  Furata da ‘yan yaji rankandam,

  Sai da nid daka nib burke,

  Had da gudajin nono.

  Wakokin baka na cikin labarai da tatsuniyoyi

  Gusau, (1980) ya ce haka kuma akwai wasu ‘yan wake –wake da ake sakawa a cikin labarai ko tatsuniyoyi don kara musu armashi ko jawo hankali da tunanin mai sauraro. Ga wani misali daga tatsuniyar Madaci da Yarinya:

  Yaninya:       Madaci, Madacci ubana,

  Gare ka anka ban ni,

  Gare ka za ni tsira.

  Madaci:         Ishunki, ishunki diyata,

  Gare ni anka bak ki,

  Gare ni za ki tsira,

  Mutum dari da goma,

  Manzo dai kan kai gida.

  Wakokin baka mai tafiya da kade-kade

  Gusau, (1980) ya ce "Wakokin baka masu tafiya da kade-kade wakoki ne wadanda makadan baka suke shiryawa. Wakokin makadan baka sun karkasu dangane da ire-iren makadan da ke aiwatar da su, ko ta hanyar kayan kidan da ake amfani da su ko kuma ta yanay-yanayen wadanda ake yi wa su. Wakokin baka masu tafiya da kade-kade sun hada da:

  Wakokin jama’a

  Wakokin jama’a su ne wakoki wadanda ake yi wa attajirai da ma’aikatan gwamnati da sauran jama’a. Makadan da ke yin wakokin jama’a suna da yawan gaske, sunayen wasu daga cikinsu sun hada da Mamman Shata da Danmaraya Jos da Abdu Karen Gusau da Mammalo Shata da Garba Supa da Shehu Ajilo da Sabo Saya-Saya da Musa Danba’u da Aliyu Gadanga da Haruna Uji da Hassan Wayam da Sani Dan’indo da sauransu.

  Wakokin maza

  Wakokin maza, wakoki ne da ake yi wa wasu rukunin jama’a da suka hada da ‘yan dambe da ‘yan tauri da ‘yan kokawa, da ‘yan baura da sauransu. Daga cikin makadan wannan sashe akwai Kassu Zurmi da Muhammadu Bawa Dan’anace da Isa Danmakaho da Illon Kalgo da Muhammadu Gambu da makamantansu.

  Wakokin sana’a

  Wakokin sana’a, wakoki ne wadanda ake yi wa masu sana’o’in gargajiya kamar wanzamai da mahauta (runji) da manoma da masunta da makera da majema da masaka da sauransu. Yawancin makada na rukunin wakokin maza su ne suke shirya wakoki na rukunin wakokin sana’a kamar Dan’anace.

  Wakokin fada

  Wakokin fada wakoki ne wadanda ake shirya wa sarakuna da sarautunsu na gargajiya. Wasu daga cikin fitattun makadan fada sun hada da Ibrahim Gurso da Ibrahim Narambada da Salihu Jankidi da Abubakar Akwara da Buda Dantanoma da Muhammadu Dodo Maitabshi da Musa Dankwairo da Abdu Inka Bakura da Aliyu Dandawo da Sani Dandawo da sauransu.

  Wakokin ban dariya

  Wakokin ban dariya, wakoki ne wadanda ake aiwatarwa domin nishadantarwa da yi wa rai yayyafi. Daga cikin makadan ban dariya akwai ‘yan kama da ‘yan gambara da ‘yan galura da sauransu.

  Wakokin sha’awa

  Wakokin sha’awa su ne wakokin da ake shirya wa abubuwan da suka ba mutum sha’awa ko suka kayatar da shi. Da wuya a ware makadi daya daga cikin makadan Hausa a ce wakokin sha’awa kawai yake shiryawa, amma akwai wasu makadan da suke tsarma ire-iren wadannan wakoki jefi-jefi a cikin wakokinsu  kamar Haruna Uji da Mamman Shata da Danmaraya Jos da Hassan Wayam da Sani Dan’indo da sauransu. A dunkule, wakokin baka na Hausa suna nan jibge kuma sun ratsa dukkan sassan rayuwar Hausawa ta fuskar zamantakewa da siyasar zama ko tattalin arziki ko addini ko ta hanyar al’adu ko wasanni da sauransu. Mai karatu na iya duba wasu dga cikin makalunmu akan wakokin Hausa, kamar: Nazarin wakokin baka Muhammadu Dan Anace a wakar Garba Nagodi da Tarihin wakokin baka na Hausa da wanzuwarsu ko kuma Yadda wakokin yara ke gina tunanin rayuwar al’ummar Hausawa (na uku) da sauransu.

Comments

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Dalilan da ka iya sawa a koma vegan diet

  Posted Sep 2

  A ‘yan shekaru kadan da suka wuce, kafar yada labarai ta kasar Amurka mai suna USA Today ta ruwaito cewa kashi 50% na mutanen kasar Amurka suna ta kokarin su ga sun inganta lafiyarsu ta hanyar kokarin ganin sun rage yadda su ke cin nama da yawa a ciki abincinsu. A...

 • Physics: Darasi akan pressure in fluid

  Posted Aug 29

  Ga definition na pressure a Turance kamar haka; pressure is defined as the force acting perpendicularly per unit area. Idan kuma za a duba equation na shi ne a math, shi kuma ga shi kamar haka: Pressure = Force / Area , shi ne kamar haka,  P = F / A Ga abinda ...

 • Matsalar shaye-shaye a tsakanin matasanmu a yau

  Posted Aug 25

  A wannan Makala za muyi dubi ne zuwa ga wani maudu’i mai muhimmanincin gaske. Za mu duba matsalar shaye-shaye da ya zama tamkar ruwan dare gama duniya a tsakanin matasanmu maza har da mata a wannan zamani. Duk da cewa wannan mummunar dabi’a ba dabi’a ...

 • Wa ya gaya mi ki cewa yana son ki har cikin zuciyarsa? Ki lura da wadannan alamomi

  Posted Aug 24

  Abu ne mai matuƙar ciwo mace ta fahimci cewa namijin da take so, baya sonta. Baya son kasancewa da ita a rayuwarsa.  Abun takaici irin wadannan mazajen basa iya fadar cewa ba sa son mace a baki, bare har ta san inda dare ya yi ma ta. Sai ya zamo ke a zuciyar ki ki...

 • Maɗigo da yawaitarsa cikin al’umma: Ina mafita?

  Posted Aug 20

  Tasowarmu muna kanana cikin alumma mun ga iyayenmu da sauran magabata suna da aure. Kowa da mahaifinsa da mahaifiyarsa. Hakanan kuma yayin da muke rayuwa mun ga ‘yan mata da samari daban-daban sun taso kuma mun ga sun yi aure. Kuma sannan sa’i da lokaci mutu...

View All