Makalu

Dangantakar wakar Sa’adu Zungur, Arewa Jumhuriya ko Mulukiya da halin da ake ciki a siyasar Arewacin Najeriya a yau

 • Kamar yadda aka saba sai mu fara da ƙoƙarin gane abin da kalmar waƙa ke nufi ga mutumin da ya tashi a ƙasar Hausa.  Idan ka haɗu da mutun a kasuwa ko a baƙin titi ko a wani wuri na gargagajiya ka tambaye shi abin da ake nufi waƙa da Hausa abin da zai faɗa maka ba zai wuce yawan son yin abu ba, ko kuma jan magana, ko nanata zance kan wani abu da ake son yi, shi ya sa za ka ji mutum yana cewa kullum ina waƙar zan zo mu gaisa amma abin ya faskara ma’ana yana ta saƙar zuci na son zuwa inda wancan abokin na sa yake amma bai je ba kenan. Waƙar abu na nufin ka yi ta kururuta batu ko jan batu a zuci na tsawon lokaci amma ba a aikatawa.

  Kenan idan aka natsu aka yi nazarin waƙa a zahiri za a ga wani zance ne ko magana ake ta ja a zuci har ta yi tsawon gaske. Amma ga masana, waƙa na nufin abubuwa da yawa.

  Ɗangambo (2007) waƙa na nufin saƙon da aka gina ne bisa tsararriyar ƙa’ida ta baiti ko ɗango ta hanyar rerarawa da kuma samun kari ko bahari da amsa-amo ko ƙafiya. Kenan za a iya cewa waƙa ta bambanta da zance nay au da kullum ta fuskar tsarawa da ƙa'idoji.

  Taƙaitaccen tarihin Sa’adu Zungur

  An haifi marigayi Sa’adu Zungura shekara ta alif da ɗari tara da sha biyar (1915). Daga cikin ƙabilar Hausawa. Ya samu ilmin boko da na Arabiya, sannan kuma yana da ilmin alƙur'ani mai girma, ya kuma yi aiki da ma’aikatan shari’a. Sa’adu Zungur y gama karatunsa a makarantar kwalejin Yaba dake garin Lagos yana ɗaya daga cikin ɗalibai ‘yan  Arewa na farko da suka dawo Arewa a matsayin malamai na makaranta a garin zariya sannan ya karantar a Bauchi a shekarar 1940 tare da malam Aminu Kano da Muhammadu Buba, haka kuma waɗannan mutanen guda uku sun yi yunƙurin ƙafa kungiyarsu ta siyasa a shekarar 1940.

  A shekarar 1950 Sa’adu Zungur ya zama sakatare na NCNC kafin daga baya ya bar wannan jam’iyar Sa’adu Zungur ya zama mawaƙi a Arewa akasar Kano. daga baya Allah ya masa cikawa a shekarar 1958.

  Salon Waƙar Sa’adu Zungur mai taken Arewa Jumhuriya ko Mulukiya

  Kafin mu yi bayani a kan irin salon da mawaƙin ya yi amfani da shi ya kamata mu faɗi ma’anar salo shi kan sa. Salo dai zaɓi ne na marubuci wajen rubutu, marubuci yana da ‘‘yancin zabeen kalmomi da jimloli. Abubuwan da ake nazarta a ƙarƙashin salo wanda kuma daga kan sa ake yanke hukunci a ce salon marubuci ya kayatar ya y armashi ko ragon salo ne sun haɗa har da kalmomi da ya yi amfani da su wajen gina labarinsa.

  Malam Sa’adu Zungur ya yi amfani da salo mai sauƙin fahimta wajen rubuta waƙarsa mai taken Arewa Jumhuriya ko Mulukiya inda ya yi bayani saosai gameda matsayn Arewacin Nijeriya da kuma yadda ‘yan  Arewa suka sa sharholiya a gaba  suka shantake ga kuma maganar ‘yan  daudu da karuwai da yadda sarakunanmu suka saki gaskiya. Misalin kaɗan daga cikin baitocin waƙar.

  Tuna baya waƙar Sa’adu Zungur mai taken Arewa Jumhuriya ko Mulukiya kamar haka:

  Matuƙar Arewa da karuwai da,

             ‘yan daudu da su da magajiya.

  Da samari masu ruwan kuɗi da,

              Maroƙa can a gidan giya.

  Matukar 'ya'yanmu suna bara,

              Titi-titi loko-loko Nijeriya.

  Hanyar birni da na ƙauyuka,

              Allah ba ku mu samu abin miya.

  Sun yafu da fatan bunsuru,

              Babu mai tariyansu da dukiya.

  Babu shakka ‘yan  kudu za su hau,

              Ɗokin mulkin Nijeriya.

  Inko ‘yan  kudu sunka hau,

              Babu sauran daɗin, daɗa kowa zai sha wuya.

  Arewa zumunta tamu ce,

              Sai ƙarya sai sharholiya.

  Camfe-camfe da tsibbace-tsibbace,

              Malam karyan ‘yan  damfara.

  Sai karyan kambon tsiya’

              Sai hula mai annakiya.

  Ga garin asali da na dukiya,

              Sai ka ce ɗan annabi fariya.

  Jahilci ya cika lakarmu duk,

              Ya sa mana sarƙa har wuya.

  Ya sa mana ankwa hannuwa,

              Ya daure kafarmu da tsarkiya.

  Bakunanmu ya sa takunkumi,

              Ba zalaka sai sharholiya.

  Wagga al’umma mai za ta yi,

              A cikin zarafofin duniya.

  Mu dai hakkinmu gaya muku,

              Ko ku karɓa ko ku yi dariya.

  Dariyarku ta zam kuka gaba,

              Da kalamar mai ƙin gaskiya.

  Gaskiya ba ta neman ado,

              Ko na zaƙin mryar zabiya.

  Ƙarya ce mai kunne bakwai,

              Da fari da baƙi ga rawaya.

  Ga kore ga kuma algashi,

              Toka-toka da ja sun gauraya.

  Babu shakka waɗannan baitoci sun isa su fargar da ‘yan  Arewa a kan irin abubuwan da suke faruwa a yau, a inda shi Sa’adu Zungur ya yi amfani da kalmomi masu sauƙin fahimta tare da jimloli masu armashi wajen rubuta wannan waƙar tasa, lallai za a iya cewa wannan salon nasa ya yi kyau ƙwarai da gaske.

  Jigo

  Shi dai jigo shi ne kashin bayan labari, wato shi ne makasudin da aka gina labari a kan sa, a kan sami babban jigo da ƙananan jigogi. To a nan za mu iya cewa jigon wannan waƙar ta Sa’adu Zungur mai take Arewa jumhuriya ko mulukiya suna da yawa kamar haka:

  1.      Gargaɗi

  2.      Gaskiya

  3.      Yabo

  4.      Zaman banza ko sharholiya

  5.      Wa’azi da sauransu.

  Marigayi Sa’adu Zungur ya fara waƙarsa ne da yabon Ubangiji mai kowa mai komai, wanda ya yi adukkan halittun duniya. Shi wannan jigon na yabon Ubangiji ga misalin kaɗan daga cikin baitocin kamar haka a inda ya ke cewa kamar haka:

  Ya mallaki dukkan talikai,

              Na kwari da tudu da samaniya.

  Da mutum aljan da mala’ika,

              Dabbar sarari da ta maliya.

  Mulki iko daula duka,

              Na ga sarki Allah shi ɗaya.

  Shi yake ba wanda ya so duka,

              Ya sarauta a lardi duniya.

  Shi yake karɓe ta ga talikai,

              Don ya ɗanɗani wahalar duniya.

  Shi ka cusa dare a cikin wuni,

              Kuma ya zaro hasken safiya.

  Shi ka rayarwa mamaci duka,

              Shi ke kashe mai rai shi ɗaya.

  Ikonsa a kan komai yake,

              A ruwa da tudu da samaniya.

  Alwakilu mu dogara duk ga rai,

              Zahirinmu a ɓoye  a zuciya.

  Mu amince zai mana taimako,

              Na haƙiƙa inda mazajiya.

  To wannan ne jigo na yabon yana ɗaya ne daga cikin jigogin wannan waƙar a inda ya bayyana yabonsa ga Allah subahanahu wa ta’ala a ciki. Babban jigon wannan waƙar ta Sa’adu Zungur mai taken Arewa jumhuriya ko mulukiya ita ce “gaskiya” shi ya hori sarakunanmu da yin gaskiya a yanayin gudanar da mulkinsu kamar yadda za mu gani a nan kamar haka:

  In za ka faɗi faɗi gaskiya,

              Komi taka ja maka ka biya.

  Haka ne Editanmu na gaskiya,

              Wanda ta fi dubun zinariya.

  Sai mu gode Allah shi ɗaya,

             Don shi ne sarkin gaskiya.

   Ya jikokin Shehu biyu,

              Sai ku ɗau tutarku ta gaskiya.

  Shehu Abdullahi haƙiƙatan,

              Ya bar mana gadon gaskiya.

  Hijira da ta iske alwali,

              Sai ta ƙarfafa tushen gaskiya.

  Ai Suleiman shi ne ja gaba,

              Kuma Dabo ya bi shi da gaskiya.

  Ga sarauta ga ilmi ciki,

              Ga adala shari’ar gaskiya.

  Arna da musulman Bauchi duk,

              Sun yi caffa don su ga gaskiya.

  Mallawa su da Barebari,

              Sun ga adalcinka da gaskiya.

  Duka sun san kai ne shugaba,

              Ka riƙe zarafinsu da gaskiya.

  A ƙasar Adamawa da Ahmadu,

              Lamiɗo fitillun gaskiya

  Jikan modibbo Shubaɗo sai,

              Ka tsare daularka da gaskiya.

  Ga Umaru Sanda da Gundiri,

              Malami ne ya san gaskiya.

  Ko ɓawo yana shakka tasa,

              Ya gaje tutar gaskiya.

  Wa ya gaji maza suna gwamutse?

              Sarkin Sudanin gaskiya.

  Karɓe shi Abdulƙadiri,

              Ka riƙe tutarka da gaskiya.

  Hakkin jama’a na kan su duk,

              Su riƙe igiyarsa da gaskiya.

  Farta ganda makairci duka,

              Sai a bar ta a binciki gaskiya.

  Dariyarku ta zam kuka gaba,

              Don nadamar mai ƙin gaskiya.

  Gaskiya ba ta neman ado,

              Ko na zaƙin mryar zabiya.

  ‘yan  Arewa ku daina gaganiya,

              Ku riƙe daularku da gaskiya.

  Zaku rera faɗar da-na-sani,

              Da na bi jawabin gaskiya.

  Insha Allahu mu tsarkake,

              Bisa fatan za mu bi gaskiya.

  Babu mai aiki bisa hankali,

              Da basira don ya ga gaskiya.

  To sarakai sai fa ku fargaga,

              Don ku gyara ƙasarku da gaskiya.

  Mun gode Allah shi ɗaya,

              Don shi ne sarkin gaskiya.

  A zahirin gaskiya, duk waɗannan baituka da muka kawo su a nan za a ga cewa dukkansu suna ambaton kalmar gaskiya, shi ya sa muka ce babban jigon wannan waƙar shi ne yin gaskiya.

  Zubi da tsari 

  Salon gargaɗi, misalin baitocin salon gargaɗi malam Sa’adu Zungur ya gargaɗi ‘yan  Arewa da sarakunansu bisa ga hangen nesa da ya ji bisa kan mulkin Nijeriya kamar haka: 

  An sha bamban kan nufi,

              Na shirin mulkin Nijeriya.

  Niyar kudu in suka ɗaukaka,

              Duk ƙasa ta zamo jumhuriya.

  Ku fahaimci shiri na mulukiya,

              Da yawan haɗari jumhoriya.

  Mulki na wakilan gurguzu,

              Babu sarki babu sarauniya.

  Sai ‘yan  sanda sai soja sai,

              Oda ita ce jumhuriya

  Fatanmu Arewa ta farga duk,

              Don ta gane lamarin duniya.

  Farfaganda makirci duka,

              Sai a bar ta a binciki gaskiya.

  Hudubobin kini bibi duka,

              Dangin zance na falaniya.

  Da sarakai sun fi ɗari biyar,

              Duka sun watse ba ko ɗaya.

  Sai ka ce da dai ba a yi su ba,

              Kun ji sharrorin jumhuriya.

  Duk misalan nan na Amerika,

              babu mai kyau na shirin jumhuriya.

  ‘yan  Arewa ku daina ganganciniya,

              Ku riƙe daularku da gaskiya.

  To sarakai sai ku yi tattali,

              Na adala ban da haramiya.

  Sun yi ta kau bisa kanmu ko,

              Mun roƙi zumuntar duniya.

  Kar ku ruɗu da zancen ja’iran,

              Masu son halakar Nijeriya.

  Za mu bika ka ja mu zuwa ga,

              Kar ka yarda Arewa ta wuya.

  Matuƙar Arewa da karuwai,

              Wallahi za mu ji kunyar duniya.

  Daga waɗannan baituka waƙar Sa’adu Zungur ya yi maganganu na gargaɗi musamman a kan jamhuriya da ‘yan  Arewa da ya kawo misalan a rubuce. Dangane da nazarin waƙar Sa’adu Zungur a cikin ƙananan jigon akwai “zaman banza ko sharholiya” yanzu za mu karkata akalarmu mu binciki yadda ya waƙe masu sharholiya da zaman banza (zaman kashe wando) musamman ma ga al’ummar Hausawa. Inda yake cewa:

  Matuƙar ‘yan  iska na gari,

              ‘yan  daudu da su da magajiya.

  Kai Bahaushe ba shi da zuciya,

              Za ya sha kunya nan duniya.

  Arewa zumunta ta mutu,

              Sai nishaɗi sai sharholiya.

  Ire-iren wannan jawabin da ya yi duk zaman banza yake kawo su, sannan ga inda ya yi maganan karuwai da ‘yan  daudu, idan mutum yana da ƙwaƙƙwaran sana’a ba zai shiga irin waɗannan hargitsi ba don mutum shi yak enema wa kansa mutunci.

  Shi kuma wannan jigo na wa’azi yana tafiya ne tare da maganar gaskiya ɗin inda yah ore mu da gudanar da gaskiya a duk inda muka tsinci kanmu don huɗubar yin gaskiya ma ai wa’azi ne ga misalin kaɗan daga cikin waƙar kamar haka:

  Ilimi, hikima addini duka,

              Da dabarar sarrafa duniya.

  Da aminci babu gwagwarmaya,

              Babu zalunci da hatsaniya.

  Hakki na ƙabiloli duka,

              Na wuyanku ku sauƙe lafiya.

  Daularku a kayin mumini,

              Da wasunsu taw aye lafiya.

  Wa’azi ne mulkin Indiya,

  Da ta zam daular jumhuriya.

  Wannan kaɗan kenan daga cikin baitoci a kan jigon wa’azi.

  Zubi da tsari 

  Ya ƙunshi labarin gabaɗayansa ne musamman muhimman abubuwa da suka faru a cikin labarin, waɗanda za a iya tunawa da su, kamar sunayen taurari manya da ƙanana, wurare da garuruwa a cikin labari da yadda wannan marubucin ya saƙo waɗannan wuraren da kuma abubuwan da suka faru manya da ƙanana.

  A nan tun da namu nazarin a kan waƙa ce to zubi da tsarin ma akan waƙa ce za mu yi kuma ya ƙunshi waƙar gabaɗaya wato daga farko har zuwa ƙarshe. Yanzu ɓari mu fara da sunayen manyan sarakuna na daular shehu guda goma sha ukun nan kamar su: Sarkin Kano Bayero da Bagauda, Suleiman, Sanusi Ciroma, Umaru Dallaji, sarki Abdullahi da Sarki Alhaji Usman Yakubu Yakubu na Maigari, Jafaru, Jafaru Modibbo Shuɓaɗo, Muhammadu mai Muri, Nda Yako Etsu, Umaru Sanda a Guddiri, Ahmadu, Abdu na ƙadiri, Ibrahim Nagwamutse Kabeji, Abdulƙadir, sarkin malamai sarkin Riron, sarkin Jukun, Shehu mujaddadi. Wannan mumin har sunan sojoji da ‘yan  sanda kai har da snan lugaed da su wajen rubuta waƙarsa.

  Malam Sa’adu Zungur ya yi amfani da sunan garuruwa da kuma wasu daga cikin ƙasashen waje waɗanda za mu fara da sunayen garuruwan cikin Nijeriya, kamar haka: da farko akwai Bauchi, Kano, Zariya, Birnin Gwandu, Adamawa, Muri Gudduri, Misau, Gombe, Ɗaura, Ilorin Okene, ƙasar Kuza, Abuja, Biron, Akure, Wukari, Binuwai, sannan ya yi magana a kan ‘yan  Arewa da ‘yan  kudu, sanna ya yi amfani da sunayen wasu daga cikin ƙasashen waje ga kaɗan daga cikinsu akwai: Amerika, Indiya, Pakistan, Ingila, Indonesiya, Sudan, London da Saudi Arebiya.

  Waɗannan su ne kaɗan daga cikin sunayen ƙasashe da ya Ambato a cikin wannan waƙar. Sai kuma ƙabilun ƙasar Nijeriya musammam ƙabilun Arewacin Nijeriya, ga kaɗan daga cikinsu. Hausawa, Katsinawa, Daurawa, Mallawa, su da Barebari, Zagezagi, Nupawa Jukunawa Igala.

  Dangantakar waƙar Sa’adu Zungur, mai take Arewa Jumhuriya ko mulukiya da halin da ake ciki a siyasar Arewacin Nijeriya a yau

  To yanzu zan karkata akala ta danganta wannan waƙar ta malam Sa’adu Zungur mai taken Arewa jamhoriya ko mulukiya da siyasar Arewacin majeriya a yau.

  Da farko dai malam Sa’adu Zungur shi ne wanda ya fara ƙafa jam’iyar siyasa a arewacin Nijeriya sannan kuma shi ne fitila na farko da ta fara haskaka jama’ar Arewa a cikin siyasa tun wajen shekarar 1940 ya ba wa abokansa sha’awar da su ƙafa jam’iya, saboda haka aka ƙafa jam’iyar abokai mai suna (zarias friendly society). Sannan kuma idan muka dubi maganar jam’iyar kuma tana nufin ɗan ƙullalliyar ƙasa.

  To kafin Arewa kuma ta zama jamhuriya said a manyan ‘yan  siyasa suka babbanƙaro na ƙasa a shekarar (1950) akan cewa za su ci gaɓa da zama a dunƙule ne ko da za a raba ƙasar daga nan ne aka cim ma matsaya ɗaya aka haɗe kar a rabu don ta zama ƙasa ɗaya.

  Sannan a ɓangaren tarihin siyasar ƙasar Nijeriya nan kuma za mu iya cewa a zamanin su sardauna wato da farko an yi siyasar gaskiya mai mutunci da kuma tsabta ga kuma riƙon amana, babu hasada kamar na yanzu su ‘yan  siyasa sun yi wa jama’ar su aiki sosai da gaskiya haka kuma sun sadaukar da kan su wajen bya wa jama’ar ƙasa bukatunsu irin waɗannan ‘yan  siyasa ba su damu da tara wa kai dukiya ba sai dai su yi suna ba ruwansu da hargitsi dukansu kayukansu a haɗe yake zaka ga cewa akwai ‘yan  siyasar Arewa zancen tara abin duniya bai dame su ba sosai, su da Arewa ce a gabansu haka ma ta ƙoƙarinsu na kudu su ma kudancin ne kawai a gabansu yadda zasu kawo wa jama’arsu cigaba ba ci baya ba.

  A yanzu kuwa ga irin siyasar da suke yi shi ne ƙazamar siyasa irin na danniya da murɗiya, misali idan ka tsaya takara ko da Allah ya baka nasara ba dole ne a baka ba in baka da ɗan uwa a mulki sai a murɗa a ɗauka a ba wa wanda yake da uwa a murhu. Sannan ga siyasar uban gida ga kuma cin hanci da rashawa wanda ta yi mana katut a kasarmu duk ya naɗa ya daka cikin abin da yake hana ruwa gudu a siyasar arewacin Nijeriya. Sannan har yanzu akwai wani sabon abu da ‘yan  siyasa suka kawo misali kamar siyasar bangaranci wanda a da ɗin ma akwai amma bai yi tasiri sosai kamar yanzu bat un da dai su Awolowo ya fito ne daga ɓangaren yorubawa akwai Azikwe shi kuma Iyamuri ne  ga malam Aminu Kano daga Arewa amma duk bai hana su su haɗa kais u yi wa ƙasa aiki ba. Sannan yanzu an kawo siyasa ta addini wanda a da babu shi, sannan ga ƙabilanci kusan duk wannan a siyasan yanzu ne a ka ƙirƙiro shi tun da dai babu shi a siyasar zamanin su sardauna.

  Idan aka danganta wannan waƙar da siyasar Arewa a yanzu za a ga cewa lallai malam Sa’adu Zungur mutum ne mai hange nesa wanda tun tuninsa da basirarsa ta taimaka gaya. Inda yake yi wa jama’ar Arewa gargaɗi da su yi taka tsan-tsan a kan lamarin ‘yan  kudu. Da ma tun farko ma shi ma kansa sardauna sai da ya gargaɗi ‘yan  Arewa a kan mulkin ‘yan  kudu sannan kuma ‘yan  Arewa su gayara halayyarsu sannan kuma su haɗe kawunansu don su gudanar da mulki mai tsabta. Ga kaɗan daga cikin baitocin da malam sa’adu ya yi bayani kan mulki misali.

  Addu’armu da musiba jimlatan,

  Ka kiyaye Arewa gabaɗaya.

  Ilmi addini hikima duka,

              Da dabarun sarrafa duniya.

  Jahilci ya ci lakarmu duk,

  Da dabarar sarrafa gaskiya.

  Addu’armu ga Allah Rahimi,

              Ya kiyaye Arewa gabaɗaya.

  Bamu da tsuntsu ba tarko duka,

              Wallah mun yi hasarar duniya.

  Jahilci ya ci lakarmu duk,

  Ya sa mana sarƙa har wuya.

  Duk misalan nana na amerika ko,

              Mai kyau na shirin jamhuriya.

  in sun ka sake jama’ar kudu

              Suka hau mulkin Nijeriya”

   daɗa ba mai sauran tambaya,

              Kowa ya san zai sha wuya

  An sha bamban bisa kan nufi,

              Na shirin mulkin Nijeriya.

  Niyar kudu in suka ɗaukaka,

  Duk ƙasa ta zamo jumhuriya.

  Mukam niyarmu a karkasa,

              Don Arewa ta zaɓi mulukiya.

  Ka fahimci shiri na mulukiya,

              Da yawan haɗari jamhuriya.

  Mulki na wakilan gurguzu,

              Ba sarki babu sarauniya.

  Fatarmu Arewa ta fargaga,

              Don ta gane lamarin duniya.

  Domin fa Arewa da hargitsi,

              Da yawan ɓarna ba kariya.

  Babu shakka ‘yan  kudu za su hau,

              Dokin mulkin Nijeriya.

  Waɗannan su ne baitocin da ya kawo a cikin waƙarsa, abin da yake faruwa a yanzu kenan kamar yana tsaye ne a wurin, amma duk abin da yake faruwa na mulkin ‘yan  gurguzu Allah zai iya maganinsa. 

  Sannan mai karatu na iya karanta: Tarihin wakokin baka na Hausa da wanzuwarsu

Comments

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Maɗigo da yawaitarsa cikin al’umma: Ina mafita?

  Posted Tue at 10:07 AM

  Tasowarmu muna kanana cikin alumma mun ga iyayenmu da sauran magabata suna da aure. Kowa da mahaifinsa da mahaifiyarsa. Hakanan kuma yayin da muke rayuwa mun ga ‘yan mata da samari daban-daban sun taso kuma mun ga sun yi aure. Kuma sannan sa’i da lokaci mutu...

 • Yawaitar binciken wayar miji: Dacewa ko rashin dacewa?

  Posted Jul 31

  A wannan zamani matsalolin da suke cikin aure musamman anan Arewacin Najeriya abin ba a cewa komai idan muka lura da ire-iren labarai da suke yawo yau da kullum a kafofin sada zumunta, wato social media. Duk lokacin da ka shiga social media idan yau baka ga labarin wata...

 • Takaitaccen bayani game da gravitational field

  Posted Jul 27

  A physics, gravitational field model ne da ake amfani da shi wajan bayanin tasirin da massive body ya ke da shi wajan zuwa sararin samaniya around itself producing a force on another body. Gravitational force of attraction da ke tsakanin body guda biyu ana governing din...

 • Sakamakon bincike game da matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a Najeriya

  Posted Jul 24

  Matsalar shaye-shayen miyagun gwayoyi matsala ce da kusan kowa da kowa na iya tabbarwa akwai shi a cikin al’umma musamman mu a Najeriya. Idan wani baya sha a gidanku, ko cikin danginku to kuwa lallai ba za a rasa masu yi ba a unguwarku ba. To amma duk da haka a ku...

 • Matsalar shaye-shaye a tsakanin matasanmu a yau

  Posted Jul 6

  A wannan Makala za muyi dubi ne zuw ga wani maudu’i mai muhimmanincin gaske. Za mu duba matsalar shaye-shaye da ya zama tamkar ruwan dare gama duniya a tsakanin matasanmu maza har da mata a wannan zamani. Duk da cewa wannan mummunar dabi’a ba dabi’a n...

View All