Makalu

Sinadarin copper: Me aka sani game da ita?

 • Idan masu karatu suna biye damu a darussanmu na kimiyya da fasaha a gefen kimiyyar sinadarai, za ku ga cewa karatu ya yi nisa sosai domin akalla mun yi darussa akan nau'ikan sinadarai daban daban sama da guda 20. Dafatan masu karatu suna bibiyan rubutunmu kuma suna fahimtar karatun.

  A yau ma muna tafe muku da wani element ne wanda shi kam kusan kowa ma yasan shi. Wannan element kuwa ba komi bane illa Copper. Copper ya yi kaurin suna a bakunan mutane hatta harma da wadan da ba daliban sciense ba sun san shi kuma sun san abu ne mai matukar muhimmanci ga kimiyyar lantarki.

  Copper wani irin karfe ne daga cikin nau'ikan karfe da muke da su a duniya wanda ya ke kyalli kuma yana nan ne kamar launin ja kuma kamar launin ruwan kasa. Sinadarin karfe zan iya cewa shine metallic element na farko wanda dan adam ya fara mu'ama da shi ta fuskan iya sarrafashi da hannu wanda hakan ya sa ya ke da matukar muhimmanci a masana'antunmu.

  Copper wani nau'in tsohon karfe ne wanda an jima da gano shi a gabas ta tsakiya shekaru aru aru da suka gabata kamar shekaru 5100 BC. Sannan kuma tsabar (coin) kudin na kasar Amurka mai suna penny, an fara kera shi ne da sinadarin pure copper. Karfen copper shine karfe na uku wanda akafi amfani da su a duniya bayan karfen iron da kuma aluminium, kamar yadda kungiyar U.S Geological Survey suka yi bayani.

  Kashi uku cikin hudu na sinadarin copper ana amfani ne da shi wajen kera wayar wutan lantarki, telecommunication cables da kuma electronics circuits. Bayan sinadarin karfen gold, a periodic table babu wani karfe wanda siffan sa baya dauke da launin silver ko kuma gray in banda copper. Kenan dai copper da gold suna kama da juna a ido.

  Wasu abubuwan da ya kamata a sani game da copper

  1. Atomic number : 29
  2. Atomic symbol : Cu
  3. Atomic mass : 63.55
  4. Melting point : 1984.32 degree celcius.
  5. Boiling point : 2927 degree celcius.
  6. Density: 8.92 grams per cubic centimeter
  7. Phase at room temperature: solid

  Hakkin mallakar hoto: CafePress

  Tarihi da kuma karin bayanai game da copper

  karfen copper ya samo asali ne daga wani yankin manyan duwatsu da ke kasar Russia mai suna convenry yake gabas maso kudu a kasar Russia. Haka zalika duwatsun mountain ma convenry ya tafi har yankin Armenia, Azerbaijan da kuma Geogia wanda nisan sa yakai mil 600 ( 1000 kilometer away) kamar yadda bayani ya zo a wani littafi mai suna plos one wanda aka wallafa shi a shekarar 2014.

  A zamanin baya, mutanen kasar Egypt suna amfani ne da karfen copper wajen alloy metal da kuma sarka irin na yara wato toe ring a Turance. Bincike ya gano cewa kashi biyu zuwa uku na karfen copper amfi samunsa a jikin dutsen igneous rock wanda ake kiransa da suna volcanic rocks, haka zalika akan sami wasu karfen copper a jikin dutsen sedimentary rocks, kamar yadda bayani ya zo daga U.S Geological Survey.

  Za a iya duba: Bayanai akan sinadarin cobalt

  Haka zalika copper yana iya sarrafuwa zuwa siffar igiya shiyasa ma ake iya yin wayar wutan lantarki da shi kamar yadda bayani ya nuna. Kamar yadda Peter van der Krogt ya yi bayani, kalmar copper ya samo asali ne daga yaruka daban daban saboda sabanin tarihi, wasu suna da fahimtar ya samo asali ne daga kalmar cuprum daga Cyprium aes wanda kalmar shi kuma ya samo asali ne cyprus saboda a can lokacin ana samun copper ne a cyprus.

  Da za'a sami wayoyin copper wanda aka sanya a cikin motoci na zamani akayi wayarin da su, idan da za'a mike su straight  to tabbas da tsayin wayoyin ya kai kilometer daya da rabi kamar yadda U.S Geological Survey suka yi bayani. Duk adadin yawan wutan lantarkin da zai wuce ta cikin copper cikin sauri to ba zai taba kai silver sauri ba, Kamar yadda kungiyar Jefferson Lab suka yi bayani.

  Galibin karfen copper ana samun sa ne a jikin duwatsu masu dauke da dattin abubuwa, ta haka ake cire shi ta hanyar amfani da kimiyyar zamani kafin nan a fara amfani da shi wajen hada kayan lantarki. Wani lokacin kuma ana iya samun wani nau'in sinadarin copper wanda ya ke samuwa a dalilin reaction da ke faruwa a tsakanin wasu elements kamar yadda chemistry database site da ke mai suna Chemicool suka yi bayani.

  Shekaru kamar 8000 da suka wuce, mutanen duniya sun yi ta amfani da karfen copper wajen sarrafa wasu abubuwa na rayuwar su da kuma yadda za su tace shi kamar 4500 BC da suka wuce. Haka zalika sinadarin copper an gano cewa shima ana iya hada alloy metal da shi ta hanyar hada shi da sinadarin karfen tin (kuza) wanda hakan daga karshe yana haifar da karfe mai karfin gaske sama da a ce anyi amfani da shi shi kadai.

  Haka zalika mutanen da suka gabace mu sun yi amfani da karfen copper wajen sanya shaida ga wani abu wanda aka binne sa (boye) kamar yadda aka samu a kabarin wata mata a kasar Isra'el wanda kabarin ya kai shekaru 5100 BC, an sanya wannan copper ne domin ya zamto shaida ga wannan kabarin matar.

  Wannan shine karshen karatunmu game da copper, Allah ta'ala shine mafi sani. Sannan za a iya karanta: Duk abinda ya kamata a sani game da sinadarin da sauransu

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Magani da wasu alfanun ganyen Bi-ni-da-zuga (Jatropha Curcas)

  Posted Apr 17

  Alfanun tsiro ko ganye a matsayin abinci ko hanya ta samar da waraka (magani) daga wasu nau’o’in cututtuka ga ɗan Adam daɗɗaɗe abu ne a tarihi. Don haka, kusan kowace al’umma ta tanadar da hanyoyin sarrafa nau’ukan abincinta da kuma samar da kari...

 • Yadda ake hada Nigerian jellof rice

  Posted Apr 17

  Assalamu alaikum, barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. A yau zan koya mana yadda ake hada Nigerian jellof rice. Abubuwan hadawa Man gyada Tarugu Tumatur Tattasai Albasa Maggi Spices da seasoning Peas Carrots Kifi Yadda ake hadaw...

 • Yadda ake hada net crepes

  Posted Apr 17

  Assalamu alaikum, barka da sake saduwa a fannin girkegirkenmu na Bakandamiya. Harwa yau mai karatu zai iya duba makalunmu da muka gabatar na daruruwan girke-girke a baya. A yau kuma zan koya mana yadda ake hada net crepes. Abubuwan hadawa Fulawa Baking powder Foo...

 • Yadda ake hada desiccated coconut and chocolate chips cake

  Posted Apr 17

  Assalamu alaikum, barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. Harwa yau mai karatu zai iya duba makalunmu da muka gabatar na daruruwan girke girke a baya. A yau kuma zan koya mana yadda ake hada desiccated coconut and chocolate chips cake. Abubuwan ha...

 • Bayanai game da Charle's Law

  Posted Apr 16

  Charle’s law na daya daga cikin laws na gas wanda a makala ta da ta gabata na yi bayani akai. Yau kuma zan yi bayani ne, kamar yadda na ambata a baya, akan daya daga cikin gas law din wato charle’s law. Wannan law din ya samo sunansa ne daga wani masanin kim...

View All