Forums » Alwala

Ina cikin alwala sai na tuna cewa na manta wani gaba a baya

  • 8 posts
  November 19, 2018 8:34 PM GMT
  Assalamu alaikum malamai, a taimaka mini da wannan tambaya game da gyaran alwala.

  Ina cikin alwala sai na tuna cewa na manta ban yi wani abu a baya ba, misali na manta ban kurkure baki ba ko kuwa ban wanke fuska ba.

  1. To idan na tuna ina cikin alwala, misali, ina cikin wanke kafafuwa, me ya kamata na yi?

  2. Idan kuma yayin da na tuna na rigaya na gama alwala, me ya kamata na yi?

  3. Haka kuma idan ina cikin sallah ne na tuna ko na fahimci hakan, me ya kamata na yi?

  Allah ya sa mu dace.