Group Info

Tattaunawa

 • 0 replies

  Hadisi na goma sha biyu

  An karɓo daga Abi Hurairata (Allah ya yarda da shi) ya ce, " Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya ce, "Yana daga cikin kyawun musulunci mutum ya bar abin da ba ruwansa." Hadisi ne mai kyau Turmizi da waɗansunsu haka suka ruwaito shi
 • 0 replies

  Hadisi na goma sha ɗaya

  An karɓo daga Abi Muhammad Alhasan ɗan Aliyyu ɗan Abu Dalib, jikan Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) kuma ɗan lelensa (Allah ya yarda da su) ya ce, "Na kiyaye daga Manzon Allah, (tsira da aminci su tabbata a gare shi) cewa, "Rabu da abi...
 • 0 replies

  Hadisi na goma

  An karɓo daga Abi Hurairata, (Allah ya yarda da shi) ya ce, "Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya ce, "Allah Maɗaukakin Sarki tsarkakakke ne, kuma ba ya karɓar abu sai mai tsarki, kuma haƙiƙa Allah ya umarci muminai da abin da ya umarci...
 • 0 replies

  Hadisi na tara

  An karɓo daga Abi Hurairata Abdurrahman ɗan Sabri (Allah ya yarda da shi) ya ce, "Na ji Manzon Allah (Tsira da aminci su tabbata a gare shi) yana cewa, "Abin da na hane ku, ku nisance shi, kuma Abin da na umarce ku da shi, ku yi shi gwargwadon ikonku. Haƙ...
 • 0 replies

  Hadisi na takwas

  An karɓo daga ɗan Umaru (Allah ya yarda da su), ya ce, "Haƙiƙa Manzon Allah (tsira da amincin su tabbata a gare shi) ya ce, "An umarce ni in yaƙi mutane, har sai sun tabbata cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma cewa Muhammadu Manzon Allah ne,...
 • 0 replies

  Hadisi na bakwai

  An karɓo daga Abi Ruƙayyata Tanimu, ɗan Ausi Addariyyu (Allah ya yarda da shi) ya ce, "Annabi (tsira da amincin su tabbata a gare shi) ya ce, "Addini nasiha ne" Muka ce, "Ga me?" Ya ce, "Ga Allah, da Littafinsa, da Manzonsa, da shugabannin musulunci, da j...
 • 0 replies

  Hadisi na shida

  An Karɓo daga Abi Abdullahi ɗan Nu'umana ɗan Bashir (Allah ya yarda da su) ya ce, "Na ji Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) yana cewa, "Haƙiƙa halal a fili ya ke, haka kuma haram, shi ma haƙiƙa a fili ya ke. A tsakaninsu akwai waɗ...
 • 0 replies

  Hadisi na biyar

  An karɓo daga Uwar Muminai, Ummu Abdullahi, A'ishatu (yardar Allah ta tabbata a gare ta) ta ce, "Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce, "Wanda ya ƙaga wani abu da babu shi cikin al'amarimmu (Addini) to, ba za a karɓa masa ba". ...
 • 0 replies

  Hadisi na huɗu

  An karɓo daga Abi Abdurrahman Abdullahi ɗan Masa'udu (yardar Allah ta tabbata a gare shi) ya ce, "Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) mai gaskiya abin soma da gaskiya, ya ba mu labari, ya ce, "Haƙiƙa a kan tara halittar ɗayanku (wa...
 • 0 replies

  Hadisi na Uku

  An karɓo daga Uban Abdurrahman Abdullahi ɗan Umaru ɗan Haɗɗabi, (Allah ya yarda da su). Ya ce, "Na ji Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) yana cewa, "An gina musulunci a kan abubuwa biyar. Tabbatawa babu abin bauta wa da gaskiya sai Allah...
 • 0 replies

  Hadisi na Biyu

  Har wayau an karɓo daga Umar (yardar Allah ta tabbata a gare shi) ya ce, "Wata rana muna zaune tare da Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) sai wani mutum mai tsananin farin tufafi, mai tsananin baƙin gashi, ya ɓullo mana. Babu waɗa...
 • 0 replies

  Hadisi na Ɗaya

  An Karɓo daga hannun Sarkin Musulmi Abu Hafsi Umaru ɗan Haɗɗabi (Yardar Allah ta tabbata a gare shi), yace, "Na ji Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) yana cewa, 'Ayyuka da niyyoyi su ke tafiya kurum, kuma cewa abin da mutum ya yi ...