Mambobi

Sababbin Mambobi

 • Lawan Dalha Matashiya kan azumin watan Ramadhana *الحمل والرضاعة من الأعذار المبيحة للفطر في رمضان* *Daga uzurorin da su ke halatta, karya azumi a cikin yinin ramadhana akwai ciki da reno* *1/* عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله عنه، قَالَ: أَغَارَتْ عَلَيْنَا خَيْلُ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَأَتَيْتُ الرَّسُولَ وَهُوَ يَتَغَدَّى فَقَالَ: *«ادْنُ فَكُلْ»* قُلْتُ: إِنِّي صَائِمٌ، قَالَ: *«اجْلِسْ أُحَدِّثْكَ عَنِ الصِّيَامِ، إِنَّ اللَّهَ عَزَّ وَجَلَّ وَضَعَ عَنِ الْمُسَافِرِ شَطْرَ الصَّلاةِ. وَعَنِ الْمُسَافِرِ وَالْحَامِلِ وَالْمُرْضِعِ الصَّوْمَ»*. أخرجه الترمذي [715]، وقال: *حديث حسن*، والنسائي [2/103]، وابن ماجه [1667]، وقال الألباني: *حديث حسن* [صحيح سنن النسائي، رقم: 2145]. *Fassara* An ruwaito daga Anas -Allah ya kara yarda a gare shi-, ya ce: Dokunan yakin Manzon Allah -sallal Lahu alaihi wa sallama- sun kawo mana farmaki, Sai na zo wajen Manzon Allah alhalin yana cin abincin rana, Sai ya ce: *"Matso, ka ci"*; Sai na ce: Lallai ni ina azumi, sai ya ce: *"Ka zauna in baka hadisi kan azumi, Lallai ne, Allah ya dauke wa mai bulaguro rabin sallah. Haka kuma ya dauke azumi ga Matafiyi, da Mai ciki, da Mai shayarwa"*. At-tirmiziy ya ruwaito[715], ya ce: *hadisi ne hasan*, da AnNasa'iy (2/103), da Ibnu-majah [1667]. Albaniy ya ce: hadisi ne hasan (Sahih sunan An-nasa'iy, [2145]). *2/* قَالَ البخاري: قَالَ الحَسَنُ وَإِبْرَاهِيمُ: *«فِي المُرْضِعِ أَوِ الحَامِلِ، إِذَا خَافَتَا عَلَى أَنْفُسِهِمَا أَوْ وَلَدِهِمَا تُفْطِرَان،ِ ثُمَّ تَقْضِيَانِ»*. قاله البخاري معلقا [قبل حديث برقم: 4505]. *Fassara* Bukhariy ya ce: Alhasan da Ibrahim sun ce: *"Mai shayarwa, da mai ciki, idan har su ka ji tsoro ga kansu, ko ga 'ya'yansu, sai su karya azumi, sannan su yi ramuko"*. Bukhariy ya hakaito shi, a [Sahihul Bukhariy, gabanin hadisi mai lamba: 4505]. *3/* وعن ابن عباس رضي الله عنهما، أنه قال: *"وَالْمُرْضِع والْحُبْلَى إِذَا خَافَتَا عَلَى أَوْلادِهِمَا أَفْطَرَتَا، وَأَطْعَمَتَا"*. أخرجه أبو داود [2337، 2318]، وصححه الألباني، في إرواء الغليل [4/ 18، 25]. *Fassara* An ruwaito daga Abdullahi dan Abbas -Allah ya kara yarda a gare su-, ya ce: *"Mai shayarwa, da mai ciki, idan suka ji tsoro ga 'ya'yansu, sai su karya azumi, sannan su ciyar"*. Abu-dawud ya ruwaito shi [2337, 2318], Albaniy ya inganta shi, a cikin littafin (Irwa'ul galil, 4/ 18, 25). Kuma an rawaito kwatankwacinsa daga: Abdullahi bn Umar -Allah ya kara yarda a gare su-. *Tsokaci* Wadannan hadisan suna nuni akan; *(1)* Lallai yana daga cikin uzurorin da suke halatta karya azumin Ramadhana, akwai ciki da shayarwa. *(2)* A cikin watan rTamadhana, mace mai ciki, da wanda take shayar da jariri, ko dai ya kasance za su iya azumi, ko kuma tare da sun sha, ko 'ya'yansu sun sha matsanancin wahala, ko kuma lamarin ya kasance ba za su iya azumin ba kwata-kwata; Idan har za su iya, ko kuma da takaitacciyar wahala, to a nan sai su yi azumi, tare da mutane a cikin wannan wata mai alfarma. Idan kuma, azumin zai cutar da lafiyarsu, to sun zama kamar marasa lafiyan da ke ajiye azumi lokacin da jinya ta tsananta a gare su, sai kuma su yi ramukon abinda su ka karya, daga baya. Haka kuma, da tsoron nasu zai kasance ga 'ya'yan cikinsu ne, ko na goye da suke shayar da su, shi ma an musu rangwame ko uzurin ajiye azumin. *(3)* Idan mai ciki, da mai shayarwa su ka ajiye azumi, shin ciyarwa za su yi, ko ramuko? Wannan mas'ala an samu fatawa kashi biyu a kanta, tun zamanin magabatan kwarai, har zuwa yau. kuma su ne abinda su ka zo a cikin "asarai" da ambatonsu ya ke, sama. Sai dai kuma abinda ya fi fitar da mai ciki, ko mai shayarwar da ta karya azumi, daga sabani, sawa'un ta karya azumin ne, saboda kanta, ko don jaririn da ta ke shayarwa ko don cikinta = Shi ne, ta kirgi kwanakin da ta sha azumi a cikinsu, domin ta yi ramukonsu daga baya. *(4)* Masu uzurorin da ya halatta su karya azumi a cikin watan Ramadhana, idan uzurinsu ya zama a sarari, kamar rashin lafiyar da ta bayyana ga kowa, wannan ya halatta su ci abinci a idon jama'a. Yayin da wadanda uzurorinsu ka-iya buya, su kuma saboda alfarmar wannan watan, bai kamata, su rika cin abinci a cikin mutane ba, tsoron kada a munana musu zato, kamar mai haila da nifasi, da mai ciki, ko shayarwa, da matafiyin da ya iso gida, alhalin ya karya azuminsa tun daga hanya. *Allah Shi ne mafi sani*.
  Jun 1

 • Rahmatu Lawan *Yadda Ake Yin Sallar Jana'iza* 1. KABBARA TA FARKO ana karanta {suraul-fatiha} ne kawai, banda wata sura, ko wata a'ya. 2. KABBARA TA BIYU ana karanta Salatin Annabi ba wani salati na daban ba. 3. KABBARA TA UKU ana yin addu'a ga wanda ya mutu mace ko namiji. 4. KABBARA TA HUDU za ka yi addu'a ne ga sauran al'ummar Musulmi Wadanda suke Raye da matattu. DAN UWA KANA GAMAWA sai ka jira Liman ya yi sallama. Ita kuma sallamar guda daya ce tak! Kuma za ka yi ta ne a bangaren damanka. Allah muke roko da ya kara tabbatar damu akan Sunnar Annabin Rahama, Manzon Allah (S.A.W). Akwai bukatar a yada Wan nan Sako Dan Allah ta Hanyar Share. domin 'yan uwa musulmai su karu. Allah yabada ikon Hakan Ameen
  Jul 18

 • Kamaluddeen Abubakar Inayiwa mutanen Wannan social media fatan alheri. Dafatan yan uwa da abokan arziki suna cikin koshin lafya ameen.
  Apr 14

 • Safiyya Muhammad Bello Assalamu Alaikum!. Its nyc bein here, Allah yasa mu karu da juna
  Sep 23

 • Bakandamiya Muna farin ciki shaida wa mambobinmu cewa a halin yanzu muna aiki akan manhajojinmu, wato Apps namu na IOS da Android. In Allah Ya yarda nan bada jimawa ba za mu kammala. Saboda haka muna bada hakuri game da dan tangarda da za ku ke samu wajen browsing na taskartamu. Idan har kuga tangardan ta yi yawa kuna iya komawa full site inda zaku iya browzing babu wata matsala. Yadda zaku je full site shine, idan kuka latsa menu a mobile, sai ku gangara kasa, a karshe za ku ga 'Full site, nan zaku latsa zai kai ku inda kuka saba browzing na taskar. Da zarar mun kare upgrading na app namu inshaa Allahu komai zai daidaita. Mun gode.
  May 1

 • Usama S Goma KANASON GIDANKA YA CIKA DA ALBARKA? Ma'aiki (S.a.w.) Yana cewa: "Lallai Gida Yakan Samu Yalwa (Walwala da Nishadi) Ga Ma'abotansa, Sannan Mala'ikun Rahmah Sukan Shiga, Shaidanu kuma Su Nisanceshi, Alkhairansa Su Yawaita Idan ana karanta Alqur'ani a cikinsa. Hakanan Gida Yakan Quntata (Damuwa da quncin Rayuwa) Ga Ma'abotansa, Sannan Mala'ikun Rahmah Sukan Kaurace Masa, Shaidanu Su tare aciki, Kuma Alkhairansa Suyi Qaranchi idan ba'a karanta Alqur'ani acikinsa" (Saheeh Sunan Addarimy 3352). 09-01-1440H (19-09-2018)
  Sep 19