GAME DA MU

Bakandamiya taska ce da aka ƙirƙireta don ba wa jama'a kowa da kowa damar musayar basira, sada zumunci da harkokin kasuwanci ta hanyar amfani da na'urorin zamani kuma cikin harshen Hausa.

 

Kowa na iya yin rajista ya buɗe shafi a taskar don mambobi su ƙaru da shi, kana shi ma ya ƙaru da su. Duk mamban da ya yi rajista (har ma da wanda bai yi rajista ba) yana iya amfana ko mu’amala da Bakandamiya ta muhimman ɓangarorinta guda 10 kamar haka:

 

1. Tambayoyi: Wannan sashe ne na amsoshi da tambayoyi wanda kowa zai iya amfana da shi. Wanda ya yi rajista yana iya tambaya kuma ya ba da amsar wata tambayar da wani ya yi. Idan kuma mutum bai yi rajista ba, to yana iya karanta komai amma ba zai iya rubuta tambaya ko amsa ba har sai ya yi rajista.

 

An kasa sashen ‘Tambaya’ kashi-kashi, kama daga tambayoyi a kan abin da ya shafi addini – tsarki, alwala, sallah, azumi, zakka, hajji – zuwa abin da ya shafi, kimiyya da fasaha, noma da kiwo, zamantakewa, girke-girke, koyon Turanci, na’ura mai ƙwaƙwalwa, tarihi da al’adu, da ma sauran tambayoyi daban-daban da za a ƙaru da su.  Ku latsa nan don ziyartar sashen tambayoyi.

 

Idan kuma kuna da tambaya game da yadda za ku yi amfani da taskar ne, misali kuna fuskantar wata matsala na rajista ko sanya hoto, ko makamantarsu, to kuna iya latsa nan don rubuta tambayarku ko kuwa samun ƙarin bayani.

 

2. Zauruka: Ana amfani da zauruka ne kamar yadda ake amfani da ‘group’ a kafafen sada zumunta. Kowane mamba na iya ƙirƙirar zaure gwargwadon abin da yake so ya yi da shi, kama daga zauren abokai, zuwa na haɗin kai da kai, da na kasuwanci, da na karatu da makamantarsu. A halin yanzu muna da zauruka daban-daban da mambobi da dama suka ƙirƙiro. Ku latsa nandon ganin su.

 

3. Maƙalu: Maƙalu na daga cikin muhimman sashe na Bakandamiya. A nan ne mambobi da ita Bakandamiya suke buga rubuce-rubuce masu ilmantarwa da suka shafi fannoni daban-daban, kamar su kimiyya da fasaha, kiwon lafiya, zamantakewa, tarihi da al’adu da makamantarsu.

 

Duk maƙalar da za a wallafa, Bakandamiya na iya ƙoƙarinta wajen tantancewa don ganin duk bayanan da marubuci zai wallafa ya zama ingantacce a bisa tsarin bincike da ilmi. Wannan na daga cikin babban abin da ya bambanta Bakandamiya da mafi yawancin kafafen sada zumunta na zamani – komai marubuci zai buga sai ya inganta – amma fa Bakandamiya ba ta yin katsalanda cikin ra’ayin marubuci. Kuna iya latsa nan don ziyartar sashen maƙalu.

 

Duk mai sha’awar rubuto maƙala sai ya tuntuɓe mu a shafinmu na “tuntuɓe mu” wanda za a iya samu a ‘menu’.

 

4. Bidiyoyi: Bakandamiya na da sashen bidiyoyiinda mambobi za su iya sanya bidiyoyi kala-kala, kuma kowa na iya kallo. Shi ma fannin bidiyoyi an kasa shi zuwa kashi daban-daban, kama daga kwalliya da sutura, wa’azi da tambayoyin addini, koyon sana’o’i, da abubuwan abin al’ajabi, da ma sauran bidiyo kala-kala. In dai mutum ya san Youtube, to tamkar haka ya ke.

 

Duk mai buƙatar sanya wani bidiyo don amfanin mutane da makamancin haka, to ya tuntuɓe mu.

 

5. Sautuka: Wannan muhimmin ɓangare neda Bakandamiya ke kawo muku abubuwa daban-daban cikin sauti, kama daga wa’azi da karatun littattafan addini, zuwa karatun littattafan Hausa na da da na yanzu, da waƙoƙi da dai makamantarsu.

 

Yanzu haka sashen sautuka na ɗauke da karatun littafin Magana Jari Ce na ɗaya da na biyu da na uku, kana da karatun littafin Ahlari da Iziyyah, da Risala wanda marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya karantar lokacin rayuwarsa.

 

Ku latsa nan don sauraren abubuwan da sashen ya ƙunsa. Kuma ku tuntuɓe mu idan kuna da abin da kuke so ku sanya don amfanin al’umma.

 

6. Hotuna: Wannan ɓangare ne da zai bai wa mambobi dama su ƙirƙiro albam na hotuna daban-daban don tarihi da makamancin haka, misali, akwai sashen hotunan tarihi da al’adu, da shahararrun mutaneda dai sauransu.

 

Abin da ya bambanta sashen hotunan Bakandamiya da na sauran kafafen yanar gizo shi ne, a Bakandamiya, kowane hoto da sunansa (sunan wanda ko abin da ke hoton) da kuma taƙaitaccen bayani game da hoton. Saboda haka, sashe ne na hotuna da ke ɗauke ta ɗimbin bayanai masu tarihi. Ku tuntuɓe mu don samun damar saka hotunanku.

 

7. Kasuwa: Kamar yadda muka faɗa a taken Bakandamiya a baya cewa, dandali ne na musayar basira, da sada zumunci da kuma kasuwanci. Yana daga cikin babban hadafin Bakandamiya, ya samar da wani tsari na zamani don al’umma da ke birane da ƙauyuka su amfana daga damar da na’urorin zamani suka bayar a yanzu don yin kasuwanci.

 

Kowane mamba na iya ɗora hajarsa, da hoton hajar, da adireshin inda mai saye zai samu hajar. Yana daga cikin tsarin Bakandamiya nan gaba in Allah Ya so, masu hajoji na iya sayar da hajojinsu kai tsaye a taskar, kuma su sami kuɗinsu ba tare da matsala ba. A halin yanzu, kuna iya tuntuɓar mu don ba ku dama ku ɗora hajojinku a kasuwar Bakandamiya.

 

Idan kuma banner na tallar hajojinku kuke buƙatar ɗorawa, to ku latsa nan don karanta cikakken bayani game da abin da ya shafi wannan, kama daga girman banner, da inda za a sanya maku shi, da yawan kwanaki da zai yi, ko yawan clicking da za a yi, da kuma kuɗin da za ku biya do yin hakan.

 

8. Sanarwa: Sanarwa sashe ne da kowane mamba zai iya ɗora wata sanarwa ta shi don kaiwa ga mutanen da yake buƙata. Misali, za ku iya ɗora sanarwar taruka, ɗaurin aure, bukukuwan al’adu da na siyasa da dai sauransu. Ku latsa nandon ganin yadda wannan sashe ya ke, kuma ku tuntuɓe mu don ba ku damar ɗorawa.

 

9. Ra’ayoyi: Wannan muhimmin sashe neda mambobi za su iya amfani da shi don sanin ra’ayoyin mutane dangane da wani abu da suke son sani, misali, suna son sanin ko wane cuta ne ya fi yi wa yara ƙanana illa a wani yanki, ko kuwa wane ɗan takarar siyasa ne zai iya yin rinjaye a zaɓe mai zuwa, da makamantarsu.

 

Mamba na iya ƙirƙirar tambaya tare da zaɓi guda biyu ko uku ko ma fiye da haka don mai zaɓar ra’ayin ya zaɓa. Da zarar an kammala zaɓe, zai ba ka cikakkun alƙaluma na yawan mutane da suka bayyana ra’ayinsu da kuma adadin ra’ayoyin na su.

 

10 Azanci: Azanci sashe ne na musamman don wasa kwakwalwa, tunatar da juna muhimman abubuwa na rayuwa da kumaa nishadi ta hanyar tattaro Karin magana, salon magana, hikimar zance da kuma nasihohi na masana na da da na yanzu.

 

Kowane mamba na iya badan a shi gudumawa ta hanyar rubutawa da kuma yin tsokaci ida wani ya rubuta. Ana iya latsa wannan wuri don zuwa shashen azanci.

 

Baya ga waɗannan muhimman sashe guda 10, har ila yau, kowane mamba na iya aikawa da saƙo, wato text message, ga wani mamba matuƙar akwai abota tsakaninsu. Har wa yau, waɗanda suka ƙirƙiro zauruka na iya aikawa da saƙonni ga mambobin zaurukan na su. Da zarar mamba ya yi rajista ya kuma shiga shafinsa, to zai ga inda ake latsawa a aika da saƙonni.

 

Har'la yau, kuna iya zuwa bangarenmu na karanta idan za ku iya koyon abubuwa daban-daban na ilimi da kasuwanci kai tsaye daga maluma da kwararru a fadin Najeriya da wajenta. Don zuwa wannan bangare sai ku latsa nan.

 

Kada ku manta kuna iya aikawa da duk wata tambaya game da abin da ya shige maku duhu game da amfani da taskar a “Zauren Bakandamiya”, wanda za ku same shi a cikin jerin sauran zauruka.

 

A taƙaice waɗannan su ne suka tattara suka gina Bakandamiya, kuma kowane mamba na iya amfani da kusan kowane sashe kyauta. Sai dai wasu sashen na buƙatar mamba ya tuntuɓi Bakandamiya don a ba shi damar sanyawa. Hakan ya zama dole ne don tabbatar da cewa ana ɗora abubuwa ingantattu da zai amfani mutane ba wai yaɗa ƙarerayi da jita-jita ba. Kuma kowane mamba na da ikon ya faɗi ra’ayinsa matuƙar ba zai cutar ko cin zarafin wani ba, babu gaira babu dalili.

 

Baya ga waɗannan abubuwa, Bakandamiya ta kasance cikin rukunin kamfanonin Penprofile, wanda ke ba da service daban-daban har ma da na ƙirƙirar website da sauransu.

 

Don haka, idan kuna buƙatar shafin yanar gizo, wato website, don gudanar da wasu harkoki ko kasuwanci naku, Bakandamiya na iya muku design na duk irin shafin da kuke so. Kuma za ta iya hosting maku cikin farashi mai rahusa. Dangane da tsara shafin kuwa, ba za ku biya ko sisi ba har sai kun ga tsarin ya yi maku yadda kuke so.

 

Don cikakken ƙarin bayani, shi ma sai ku tuntuɓe mu. Kuma ku yi mana bayanin irin website da kuke so, da irin abubuwan da za ku riƙa gudanarwa a kai. Shin wata gidauniya ce gareku wanda kuke so ku ke yaɗa manufofinta ta hanyar saka hotuna da labarai game da ayyukanku? Ko kuwa dai harkokin kasuwanci kuke yi, ko aikin yaɗa labaru, kuma kuna buƙatar kowa ya san da ku?

 

Duk abin da kuke so sai ku aiko mana. Kamar yadda muka ce a farko, ba za ku biya ko sisi ba har sai kun ga tsarin ya yi maku, kuma kowa na iya samun website naku kai tsaye.

 

Don ganin irin website da muka yi designing, kuna iya latsa nan. Kuna iya zaɓa daga cikin irin samfurin da kuka gani don mu san irin abin da kuke buƙata.

 

Daga ƙarshe, kuna iya ziyartar shafinmu na 'Terms of Service' da kuma na 'Privacy Policy' don sumun cikakkun bayanai game da ƙa'idoji da suka shafi amfani da taskar Bakandamiya.

 

Mun gode.