KU TALLATA HAJOJINKU

Mun zo da sabon tsari don aikawa da sakonninku ga wadanda ku ke bukata

TALLACE-TALLACE

Tsarin sanya tallace-tallace na zamani na daga cikin sabon salo da Bakandamiya ta zo da shi wanda ya banbanta ta da sauran taskokin yanar gizo. Kuna iya tallata hajojinku na kasuwanci ko wani harkoki naku ta hanyoyin daban-daban wadanda za su baku daman kaiwa ga abokan kasuwancinku kai tsaye babu shamaki.

 

Saboda haka ga hanyoyin nan kamar haka:

 

1. Sanya talla a activity feeds

 

Kuna iya kirkiro kuma ku sanya tallarku da kanku ta hanyar saka tallar a activity feeds, wato bangon nan wanda da zarar mamba ya yi signing in a Bakandamiya shi zai fara gani. Duk tallar da aka sanya a activity feeds kowane mamba na iya gani da zarar ya shigo, wato ya yi signing in a cikin account na shi.

 

2. Sanya talla a shafuka daban-daban

 

Har’ila yau zaku iya kirkiro da sanya talla da kanku wanda za a nuna a gaban mambobi a shafuka daban-daban na Bakandamiya, misali a shafin Makalu, hotuna, bidiyoyi da makamantansu. Shi wannan tsarin talla zai iya kaiwa ga kowane yanki ko wuri. Misali zaku iya aika tallanku ga mutanen ko kuwa mambobin da ke zaune a garin da kuke kasuwancinku.

 

Wani amfanin wannan tsari na talla shine, tallanku zai kai ne kawai ga mutanen da kuke sa rai za su zo su sayi hajojinku.

 

Bisa dukka wadannan tsaruka guda biyu na tallace-tallace da muka yi bayani a sama, zaku iya zabar ku biya kudin tallan bisa yawan kallon tallan naku da aka yi, wato based on views, ko kuwa bisa yawan latsawa da aka yi, wato based on clicks.

 

3. Aikowa da talla kai tsaye

 

Hanya na uku shine, za ku iya aikowa da tallar kai tsaye zuwa shashinmu na tallace-tallace. Za ku iya aikowa ne idan ku da kanku ba za ku iya sanya tallar ba, ko kuwa dai kun fi so ma’aikatanmu su sanya muku. Za su sanya muku ne kuma a irin tsari na 1 ko kuwa na 2 da muka yi bayani da farko.

 

4. Tuntubar mu don talla na musamman

 

Baya ga duk tsarukan da muka ambata a baya, har’ila yau kuna iya tuntubar mu don wata bukata taku ta musamman wacce ta shafi tallace-tallace ko kuwa wani kasuwanci.

 

Don tuntubar mu sai ku latsa nan ind za ku cike wani fam kuma ku aika shi gare mu. Har ila yau, kuna iya aiko mana da wasikar email ta adireshinmu kamar haka: talla@bakandamiya.com ko kuwa ku turo mana sakon WhatsApp ta wannan lambar: +234 (0) 907 230 4548.

 

Muna kara tabbatar muku da cewa ta hanyar amfani da tsarin tallace-tallacen taskarmu, za ku iya aika sakonninku zuwa ga wadanda ku ke so kai tsaye. Muna tabbatar muku da cewa sakonninku za su kai har gabansu.

 

Kamar yadda mu ka ce a farko, tsarin aika talla ko sakonni a Bakandamiya na daga cikin muhimman sabon salo da ya banbanta ta da sauran kafofin yanar gizo. Sai fa an gwada a kan san na kwarai.

 

Mun gode.